IN IN ANA GADON WAQA TO LALLAI NAGADA*




-inji Abdurrahman El Bashir Kazaure
.
A tattaunawarsa da wakilinmu na Ma'asumiya a cikin shirinmu na na *FILIN MAWAQAN HARKA* ku biyomu don jin cikekkiyar tattaunawar.
.
Daga Shafin MA'ASUMIYA NIGERIAN NEWS UPDATES
-
Tare da Wakilinmu na yankin Bauchi, Gombe, Adamawa.
-
MA'ASUMIYA; Allah shi gafarta kana tare da Wakilin MA'ASUMUYYA NIGERIAN NEWS masu karatunmu zasu so ka gabatar musu da kanka musamman masu kaunar wakokin ka??
-
ABDURRAHMAN KAZAURE "Na'am da farko sunana Abdurrahman El Bashir Kazaure, ni haifaffen cikin karamar hukumar Kazaure ne ta Jihar Jigawar Najeriya."
-
MA'ASUMIYA; Al'umma na ganin irin baiwar Waka da Allah yayoma har wasu ke cewa ai kai dan gadone minene gaskiyar lamarin???
-
ABDURRAHMAN KAZAURE "Na'am, tabbas idan ance hakama ba laifi bane, domin in ana gadon waka toh lallai mun gada! Don kuwa Koh bakomai mun fito Daga gidan yabon Manzon Allah (S.a.w.a) ne Iyaye da kakanni, domin wanda ya haifi mamar mu har yabar duniya yana rubuta waka ta larabci, kuma koda mauludai aka gayyace shi idan yaje yafi yin yabon Annabi akan waazi duk dako Babban Mallami ne a Kazaure, kuma sai Allah yayi mu Mabiya Mallam ZAKZAKY (H) nida Abbah Shafiu Kazaure, kuma koda yaushe tare muke dashi."
-
MA'ASUMIYA; Wasu suna cewa kai dane na cikin Shi Shaheed Alhaji Shafi'u, wasu kuma suna cewa aa kaninsane kai, zamu so musan ya abun yakene??
-
ABDURRAHMAN KAZAURE "Eh dayawa suna kasa gane dangantaka ta dashi,
Toh Shi Kawuna ne domin shi Kanin mahaifiyata ne."
-
MA'ASUMIYA; Wannan shine dalilin dayasa muryarka da ta Shaheed Alhaji Shafi'u take zuwa daya ko kuma akwai wani horo da kasamu daga gareshi ne???
-
ABDURRAHMAN KAZAURE "Lallai Nima ban saniba Amma nasan ban taba jin zan kwaikwayi murayarsa ba. Amma da nayi waka sai mutane suke cewa kamar A. Shafi'u. Hatta dabi'ama mutane sukance kamar shi, na sha ina tafiya cikin duhu sai agaisheni amatsayin shine."
-
MA'ASUMIYA; Alhaji Shafi'u Jarumine tsayeyye da baza'a manta dashi a abubuwa da damaba nawannan Harka musamman Ittuhadu daku da kuke da kusanci dashi, yayi kukaji da kuka samu lbrn Shahadarsa???
-
ABDURRAHMAN KAZAURE "Toh da farko dai munsan ita wannan tafiyar da muke kai dama haka sunnar ta take, don haka bamuyi bakin ciki ba, illa kawai kuncin rabuwa da Wanda kukayi sabo dashi."
-
MA'ASUMIYA; Wnnan haka yake Allah ya tabbatar damu.
Acikin wata waka mai suna dan baiwa kace a mafarki ka sameta ko zaka Iya bayyana mana yadda kayi mafarkin kuwa????
-
ABDURRAHMAN KAZAURE "Ilaheey ajib,
Toh an nuna min kamar ina wani wajene haka kamar ana taro kawai ni kuma saina hangi maulana Sayyed zakzaky (H) a zaune muna gabansa kawai ina rera wannan wakar, toh harna tashi ma ina rera amshinta abakina."
-
MA'ASUMIYA; To ko zaka dan reromana kadan cikin baitukanta mudan ji??
-
ABDURRAHMAN KAZAURE " *Don haka kunga wakar 'yar baiwa nina ambaceta,
*Dominko wata baiwace daga gun ubagijin halitta,
*Yayi nufin nayi masa Dan baiwa duk ku taho kujita
*Na roki Wanda yajji yayi Du'a'i, Allah ya kare dan baiwa."
-
MA'ASUMIYA; Kayi wakoki da yawa a kalla yanzu zasukai nawa??
-
ABDURRAHMAN KAZAURE "Lallai nima bansan adadinsu ba."
-
MA'ASUMIYA; To amma daga ciki wacce kafi jin ta kwanta maka a rai??
-
ABDURRAHMAN KAZAURE "Akwai waken da nayiwa Sayyed, Mai suna Sai Shehu."
-
MA'ASUMIYA; To Malam Abdurrahman mezakace wa Masoyanka maso kaunar waqoqinka??
-
ABDURRAHMAN KAZAURE "Ina yiwa kowa Fatan Alkhairi, da fatan Allah ya tabbatar damu tare da jagoranmu abun koyi Sayyid Zakzaky (H)"
-
M'ASUMIYA; Wannane shawara gareka ga masu Sha'awar zama mawaka anan gaba??
-
ABDURRAHMAN KAZAURE "Shawarata garesu shine mutum ya nemi ilmi kafin Komai, kuma ya tanadi Ikhlasi domin shine ginshikin duk kyakkyawan aiki ya kuma muhimmanta abinda yakeyi."
-
MA'ASUMIYA; Minene kiranka ga sauran mawaqa??
-
ABDURRAHMAN KAZAURE "Kirana shine mawaka su kasance masu yin komai domin Allah, kuma su doru akan koyarwar Jagoranmu Sayyed Zakzaky (H)
-
MA'ASUMIYA; Minene kiranka ga gwamnati akan tsare Jagora Sayyid Zakzaky (H) da takeyi, Alhalin kotu ta bada umarnin ta sakeshi tare kuma da biyansa diyya amna har yanzu taki gashi kuma yana fama da yanayi na rashin lfy???
-
ABDURRAHMAN KAZAURE "Ina kiran gwamnati da kakkausar murya data gaggauta bin umarnin kotun data kafa da Kanta, ta sake mana Jagoranmu! Domin Sun zalunce shi, su gaggauta sakin sa ba tare da wani sharadi ba."
-
MA'ASUMIYA; Minene fatanka anan gaba??
-
ABDURRAHMAN KAZAURE "Fatana shine naga fitowar jagirana, Kuma Allah Ya nuna masa karshen makiyansa."
-
MA'ASUMIYA; Mun gode Malam Abdurrahman.
-
ABDURRAHMAN KAZAURE "Nima nagode."
-
Wakikinmu
Salisu Umar Mazajen Zakzakyya
08021395846


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post