Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates
Tare da wakiliyarsu SAKINA AHMAD.
Tare da wakiliyarsu SAKINA AHMAD.
Watan sha'aban kamar yadda muka sani a cikin sane aka haifi imam Muhammad mahdi (a.f) a daren 15 ga watan na sha'aban. Hakane yasa mabiya ahlulbaity (a.s) a sassan duniya daban-daban suke gabatar da taruka domin tunatar da juna Dan gane da bangarori daban-daban da suke da alaka da imam mahdi(a.s) kamar haihuwarsa,shiga gaibarsa,shaksiyyar sa,alamomin bayyanarsa,bayani da rubuce-rubuce dangane dashi.
Hakanne yasa mukaga dacewar kawowa makarantan my wasu daga cikin bayanai da kuma rubuce-rubuce da Shehu Usman dan Fodio yayi dan gane da Imam Mahdi (a.f). Sheikh bn Fodio ya rubuta litattafai masu yawa Dan gane da abinda ya shafi Imam Mahdi (a.f) ga wasu
kadan daga cikin su:-
kadan daga cikin su:-
1. AL-KAIBARUL HADI ILA AMIRIL IMAMIL MAHDI
2. TAHZURIL IKHWAAN MIN INDI'AA'IL MAHDIYYATIL MAU'UDATI
KHURUJUL MAHDI
3. ALAMATIL KHURUJUL MAHDI
4. ULLUW SHA'ANI MAHDI
5. TAMBIHIM FAHIM
2. TAHZURIL IKHWAAN MIN INDI'AA'IL MAHDIYYATIL MAU'UDATI
KHURUJUL MAHDI
3. ALAMATIL KHURUJUL MAHDI
4. ULLUW SHA'ANI MAHDI
5. TAMBIHIM FAHIM
Litattafan suna da yawa da bazaiyiyu mu kawo su duka ba. Sannan 'ya'yan sama Muhammad Bello da Yar uwarsa Maryam sunyi rubutu suma akan abinda ya shafi Imam Mahdi (a.f).kamar shi Muhammad bello a litattafansa guda hudu daya rubuta akan Imam Mahdi (a.f) ga 2 daga cikinsu :-
1. AL- KAUL MUKTASAR FI AKBARIL
MAHDI.
2. KASH'FUL KAFIYYI FI AKBARIL IMAM MAHDI.
Ita ma maryam tayi rubutu akan Imam Mahdi a littafinta mai suna DARIKUL HIJRATI ILA MAHDI. Sannan ma akwai jikansa dan Muhammad bello mai suna said daga cikin litattafan daya rubuta akwai:- SAHIHUL KABAR FI AMRIL MAHDI AL-MUNTAZAR. Dama sauran almajiransa da dan uwansa sheikh Abdullahi duk sunyi makamancin irin sannan rubutun.
Da mutum zaiyi kyakkyawan bincike zaiga cewa samun nahiya a duniyar sunnah wadanda malamanta sukayi litattafai da suka shafi imam mahdi (a.f) kamar wannan nahiya to gaskiya da wahalar gaske, mutum yadan bincika wasu kasashen musulmi na duniyar sunnah ya gani.

Kuma wani abin mamaki shine idan mutum ya bibiyi wadannan litattafai da Shehu Dan Fodio ya rubuta dangane da Imam Mahdi zai ga cewa
sunyi muwafaka da yadda sukazo a makarantun Ahlulbaity (a.s) misali yadda ya kawo shekara da watan haihuwar imam mahdi (a.f) da nasabarsa da alamomin bayyanarsa da sauransu. Kamar yadda zamuga haka insha Allah a nan gaba a cikin rubutun. Saboda haka ma aka samu wasu awancan zamani a bayansu da
rubuce-rubucensu da sukayi lokacin kawo tawili a wadannan rubuce- rubucen na shehu dan fodio domin ganin sunyi kama da yadda Shi'a suka tafi akai wadanda kuma basu iya tawililantar dash ba. Sun nuna cewa shehu usman dan fodio ya dawo daga wadannan ra'ayoyin karshen rayuwarsa ne.idan mutum ya waiwayi Malaman Ahlussunnah da sukayi rubutu dan gane da Imam Mahdi (a.f) zai iya
kasa su gida uku.
kasa su gida uku.
1. Akwai wadanda abinda suka rubuta yayi muwafaka da abinda suka
tafi akai.
2. Akwai kuma wadanda abinda suka rubuta yana kusa da abinda Shi'a
suka tafi akai
3. Akwai kuma wadanda abinda suka rubuta yayi karo da abinda Shi'a suka tafi akai.
tafi akai.
2. Akwai kuma wadanda abinda suka rubuta yana kusa da abinda Shi'a
suka tafi akai
3. Akwai kuma wadanda abinda suka rubuta yayi karo da abinda Shi'a suka tafi akai.
Kamar yadda wasu daga cikin malaman Ahlussunnah suka tafi akai cewa Imam Mahdi ba'a haifeshi ba ko kuma an haifeshi yayi zamani ya wuce da sauran makamantan maganganu iri wannan. Amman idan muka dubi shehu usman dan fodio duk da ya rayu a kasa da take ness sosai da kasashen malaman imamiyya kuma bai fita saga wannan nahiya ba tsawon rayuwarsa sai gashi da ra'ayi irin na imamiyya akan imam mahdi (a.f). Bayan haka shehu usman dan fodio ya fuskanci jarabawowi daban-daban a zamaninsa musamman bayan tabbatuwar addini na cewa shine Imam Mahdi (a.f) kuma babban abinda yafi karfafawar masu irin wannan ra'ayi shine tabbatuwar addini karkashin jagorancisa shine abinda yazo acikin wani littafi Na jalaluddin assuyudi mai suna"
Al-IRKUL WARDIY FI AKHBARIL IMAMIL MAHDI. Cewa imam mahdi zai bayyanane a shekara ta 1200hj ko kuma a shekara ta 1204hj, ga shehu usman dan fodio kuma ya rayu a dai-dai wancan lokacin ne, ga kuma Allah abisa ikonsa ya tabbatar da addini a karkashin jagorancinsa ga kuma sannan hasashe Na suyudi. Saboda haka akan wadanna dalilai aka samu jama'a da dama sukace shine imam mahdi. Amman
nan take shehu yayi inkarin wannan batu da tsananin gaske, kuma ya rubuta litattafai don gamsar da mutane cewa bashi bane Imam Mahdi (a.f) kamar yadda zamuga haka nan gaba kadan insha Allah rubutun zai gudana ta fuskoki akalla guda uku.

1. Bayanan shehu dan fodio dan gane da imam mahdi (a.f)
2. Inkarinsa na cewa bashi bane imam mahdi
3. Alakarsa da Imam Mahdi.
2. Inkarinsa na cewa bashi bane imam mahdi
3. Alakarsa da Imam Mahdi.
Kashi na Daya (1).
#FreeZakzaky.
Tags:
Munasabobi