ILIMI DA HANKALI ALAMAR MUMINI, DUK MAKARYACI YANA DA DABI'A TA MUNAFIKAI.



Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates
Tare da Wakilinsu  -Idishia Jos.


Manzon Allah (S) yana cewa Imam Ali alaman mumini guda uku ne wato duk mumini yana da alamomi guda uku, wanda bashida shi to ba
mumini bane kenan alama na farko shine, Assiyam , Wassalatu , Wazzakatu. Wannan sune abubuwa guda uku wanda mumini yake da
su, Azumi Sallah da Zakkah.

Wato shi mumini bayan azumi na farilah zaka ga yana yawan azumin nafiloli, haka kuma bayan sallah na farillah zaka ga yana yawan sallolin nafiloli, bayan Zakkah na farillah zakaga yana yawan Zakkah nafiloli. Manzon Allah (S) yana cewa; Mai kallafawa kansa mai Riya kenan shima yana da alamomi guda uku.

In zaiyi shaida to zai zamo mai cika baki, kuma yakan yi gulma idan ba a nan, sannan kuma yakan yi dariya idan abu ya faru da mutum dariya na mugunta, wannan alama ne na mai Riya kuma yazamo mai cin naman mutum wannan sifface ta mai Riya idan ka zamo mai dariya idan musiba ta samu mutum to wannan ba siffabace ta mumini sifface ta mai Riya.

Manzon Allah yace shiko azzalumi yana da alamomi guda uku yanda zaka gane shi , yakan rinjayi na kasa dashi ta hanyar galaba, sannan
wanda yake sama dashi to zaiyi abinda yake dashi na sabon Allah, kuma zai zamo yana taimakon azzalumi shi mataimakin azzalumine,
zaka ga yana taimakon masu zalunci, wannan alama ne na azzalumi.

Shiko mai Riya yana da alamomi guda uku; in yana cikin mutane sai ya nuna nishadi da jin dadin sa hakama in yana ibada, in ko shi kadai ne sai ya kasan ce mai kasala da bazai yawaita ibada ba, bazai nuna kusu'i da tawadi'u a cikin ibadan saba. Kuma shi mai Riya yana so duk
abinda yayi a yaba masa baya so a zargeshi sabida haka wannan siffofi alama ce ta me Riya mutum bai zanto mumini ba kammalalle ba.

Manzon Allah yace alamomin munafiki guda uku ne; idan yayi magana sai yayi karya , idan an bashi amana sai yayi ha'inci, in kuma yayi
alkawari sai ya saba. Sabida haka idan kana da wannan halaye guda ukun mutum munafikine Allah ya tsaremu. Kuma duk makaryaci yana
da dabi'a ta munafuki

Manzon Allah (S) yana cewa; Kasalalle shima yana da alamomi guda uku; zai dinga jinkiri har sai yayi sakaci zaiyi zarbabiya har ya zanto ya
tozarta abu, tozarta abu kuma yakaishi ga sabawa Allah ta'ala.

Manzon Allah yake cewa Imam Ali (as) abubuwa uku sune da hakikanin imani wanda yake nuna cewa lalle mutum mumini ne; na farko shine " Yin infaki a lokacin da kake cikin kunci gashi kana bukata amma sai ka bayar, da wa mutum adalci da kanka, wato kawa mutum adalci da kanka, da kuma bada ilimi ga me neman ilimi. Wannan yana daga cikin ainihin wato hakakik na imani.

Mutane muji tsoron Allah kuma ya zamo cewa kullum muna neman Allah ta'ala ya azurtamu da imani. WA BILLAHI TAUFIQ.

#FreeZakzaky

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post