@Isma'il Abubakar Idri Katsina.
Mike faruwa a Kauyikan garin Zamfara, firar Wakilin Ma'asumah Nigeria News Update @Isma'il Abubakar Idris Katsina da Malama A'isha Zamfara ta wayar Hannu Duniyarka a hannunka wato ( *Android* ).
Wakilinmu : Assalamu alaikum Malama A'isha ina fatan kowa lfy, ya gida ya aiki ya Yara.
A'isha : Wa'alaikasalam Malam. Kowa da kowa Lfy, ya aiki.
Wakilinmu : Lfy Malama A'ishainaso inyimaki wasu Tambayoyi bansaniba ko zansamu amsarsu daga Bakinki.
Aisha : Malam Isma'il Bismillah kominene zanbaka amsa.
Wakilinmu : Nagode, Malama A'isha Minene Tunaninki akan Wanna Kashe-kashen da akeyi a Kauyikan Zamfara..?.
A'isha : Nidai abinda na fahimta Zalunci ne.
Wakilinmu : baki tunanin akwai wani zagon kasa da akeyima Al'umma tare da wasa da Hankali akan wannan Kashe-kashen dake faruwa a Zamfara...?
A'isha : Eh! hakane saboda Zinarin da ke karkashin kasar ne shiyasa aketa kashe Mutane baji ba gani, kuma Gaskiya wannan Gwammanne yasa hakan ke faruwa.
Wakilinmu : Malam A'isha minene dalilinki na cewa Wannan Gwamnan nada sahannu akan wannan Kashe-kashen...?.
A'isha : dalilina shi ne "
Lokacin wancen gwamnan ance babu yadda ba'ayi da shiba ayi wannan aika-aikan yaki yarda, wancan tsohon gwamnan yace "sedai inhar za'a dinga raba duk abinda akasamu da Talakawa", sai sukace a'a shi ne suka kadashi a kujerarsa ta Gwamna wanga nayanzu yahau.
Wakilinmu : kinada masaniya akan wadanne garuruwa ne ake wannan aika-aikar na kwashe zinaran kasarmu...?
A'isha: a tunanina kauyen Zurmi ne aka fara Tonuwa sabida a canne asalin faruwar al'amarin.
Wakilinmu : kinada masani cewa anfara hako wadannan Zinaran, kuma wadanne kasashe ake fita dasu...?
A'isha: Eh! Sosaima dan akwai wani dan can Zurmin class ment dina ne wlh da bakinsa yake fadamin cewa Mahaifinsa yana daya daga cikin manyan 'yansiyasa yace " yana zuwa gurin da akeyin aikin hako Zinaran kuma yakanzo da ita Zinarin yanuna masu".
Wakilinmu : Malama A'isha ko kintaba ganin Zinariyar da ake hakowa a Zamfara da Idanunki....?.
A'isha : eh! Nagani, akwai wani lokaci danace masa banta6a ganin Zinariba yace zai kawoman Zinarin in nagani kuma wlh seda ya kawo man Zinarin nagani. amma yaceman waje suke fita da'ita Canne ake gyara musu ana cire Zinarin ana cire kasar daban.
Wakilinmu : kamar wadanne Kasa she ne ake zuwa da wannan Zinaran..?
A'isha : To wlh bansan wace kasa bace ake fita dasu sabida Ban Tambaye shiba.
Wakilinmu : Malama A'isha a tunaninki akwai sahannun wasu Talakawa ake wannan aika-aika...?
A'isha : Eh! mana da yardansu gasunan zakaga wani yankar farce yake, da bincike yayi bincike saikaji dashi a ciki. wani kuma wankin takarmi yake amma kuma cikinsu yake.
Wakilinmu :A gidan redio kintaba ji gwamnati ta taba nuna kin amincewarta da wannan al'amari dake faruwa a Zamfara..?.
A'isha: hmmm Allah dai yayi mana maganinsu, Kawai kwadayin abun duniya ne.
Wakilinmu : Ameen ya Rabbee, Malama A'isha Nagode Fatan Alheri.