FIRAR GIDAN REDIYON BBC HAUSA DA SUKA YI DA SHAIKH YAQOUB YAHYA KATSINA JIYA A GARIN ABUJA

FIRAR GIDAN REDIYON BBC HAUSA DA SUKA YI DA SHAIKH YAQOUB YAHYA KATSINA JIYA A GARIN ABUJA.

 
SHAIKH YAQOUB YAHYA KATSINA. 

TAREDA MSN012,

BBC; "To ku amma a tunaninku miyasa kamar su mahukunta suke maku irin wannan dirar mikiya haka"?
SHAIKH; "To ina ganin wannan tambayar su ya kamata ayima wa, su ya kamata a tambaya aji dalili, amma har yanzu bamu san dalili ba, illa kawai mu yan kasa ne, kuma muna practice din addininmu yadda muka fahimta. Sannan kuma bana jin akwai wani tsari ko wata doka da ta hana mutum yayi addininsa yadda ya fahimta, ko da kuwa miye fahimtarsa, a dokar kasa. Wannan tambayar yafi kyau idan kun samo amsarta ku sanar damu".

BBC; "aka sarin lokuta da ake irin wannan dauki ba dadi, ko kuma ake farmaku za kaga idan an fito jerin gwano ko zanga-zanga kuma mahukunta suka ce ba su baku umarnin kuyi wadannan taruka ba".
SHAIK; "to bama tsammanin akwai wata doka akasar nan wadda tace sai ka nemi izni zakayi muzahara ba, ko jerin gwano babu. Yan kwanikan  baya ko ince yan shekarun baya da suka wuce yan siyasa sunyi fama da irin wannan matsaltsalun ana kai masu hare-hare wanda abin ya kai da shigar da kara akaje kotun koli ta yanke shawarar cewa baka da bukatar ka tambayi dan sanda  izni. Abin da ke aikin dan sanda idan yaga ka fito yana jin tsoran faruwar wani abu ko wata kungiya ta fada maka ko wani abu mai kama da haka ya bika baya ko gefe ya tsare ya ga cewa babu abin da ya faru, idan kuma yana jin tsoran kar afarma wani gine-gine na gwamnati ko na Al'umma ya tsatstsare su ya basu kariya ya tabbata kai ka tashi lafiya".

BBC; "amma ku kukan sanar da su hakan idan zaku fita alal misali"?
SHAIK; "to misali idan ya zama doka ne wa ya kamata yabi doka? Cewa baka neman izni dan kayi muzahara to doka ne? Su ya kamata su bi doka, yadda doka ta tsara masu".

BBC; "na'am ai sanar da su zai basu, maiyiyuwa idan kuka sanar dasu zai basu dama su san cewa za ku yi jerin gwano alal misali su baku irin waccen kariya ko kuma akasarin haka a yadda ka fada".
SHAIKH; "kun san babu abin da muke yi aboye, yanzu kamar wannan taron  da muka yi a yau an sanar dashi a social media an fada a Radiyo an fada a jaridu an fada ko ina yana nan za'a taro ranar kaza ga watan kaza lokaci kaza, wannan  sannan abu ne babu abin da muke a boye lasifika muke sawa a fada ko mu bada sanarwa a rubuta tun kafin lokaci yayi.
Yanzu muna da taron Nisfu Sha'aban wato ranar 15 ga watan Sha'aban wanda already sanarwa ta fara fita cewa za'ayi taro na Nisfu Sha'aban wanda aka saba duk shekara, to kaga wannan wani abu ne wanda yake haka suka zabi suyi illa iyaka".

BBC; "amma kasari akan baiwa kamar hukumomi wani lokaci akan rubuta wasika ko kwamishina yan sanda da sauransu ace gashi zamu shaida maku cewa zamu yi jerin gwano saboda haka idan mun fito ba zauna gari banza ba ne A'a kungiyar muce ta kaza daga waje kaza kuma ga manufar zanga-zangar".
SHAIKH; "sai idan kungiya tana da rivals tana da wasu abokan hamayya ko wadanda suke jin tsoran su auka masu, bamu rigima da kowa ba wata kungiya da muke rigima da ita, ba wata kungiya da take rigima damu bamu da matsalar sai mun sanarma hukuma saboda zamu yi jerin gwano, alhali ba mu da wani wanda muke jima tsoran ya kaimana farmaki ko hari ko wani abu mai kama da haka. Kuma sannan wannan abun kusan shekara arba'in 40 muna yi dan mi yanzu ya zama matsala"?

Wani bangare na Firar Shaikh Yaqoub Yahya Katsina da gidan Radiyon Bbc hausa a garin Abuja Litinin 1Apr2019.

AdamLawal
2Aprl2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post