Daga Babban Birnin Tarayyar Najeriya Abuja Rahoton abinda ya faru a tsakiyar birnin na Abuja a yau.



Ma'asumah Nigeria 🇳🇬 News Update.




A yau ne yan uwa musulmi almajiran Malam Ibrahim Zakzaky .  Masu bin akidar Shi'ar suka gudanar da taron tunawa da ranar da aka haifi Malamin nasu. Wato Ibrahim zakzaky da kuma Khalifan manzon Allah wanda suke cewa Imam Mahdi.
Shi dai wannan taron dama cen sun saba shirya shi duk ranar 15 ga watan Sha'aban .Domin taya babban Shehin Malamin murna Karin samun Shekaku a duniyar Maliki yau middini.
Sai dai a duk lokacin da suke gudanar da irin wannan taron nasu suna yin sane tare da Babban Malamin nasu, kuma a cen garin Zaria suke shirya taron nasu.Amma a wadannan shekaru uku da suka gaba sun dawo da gudanar da taron nasu a nan cikin Birnin na Abuja. Kasan tuwar tsare jagoran nasu da gwamnatin shugaba Buhari tayi . Tun ranar 12 ga watan December na shekarar 2015 . Wanda zuwa yanzu gwamnati na tsare da Malamin da Mai Dakin sa Malama Zeenatudeen Ibrahim Zakzaky.
Shi dai wannan Shehin Malamin na mabiya akidar Shi'ar a Nigeria ,an haifeshi ne ranar 15 ga watan Sha'aban a shekara ta 1372A.H a cikin Birnin Zaria. Wanda yanzu Malamin yana da Shekaru @68 a duniya.
Yan uwa Musulmin dai sun gudanar da wannan taron nasu na shekara-shekara ne Area 1 dake cikin Birnin Abuja a Diplomat Park garden. Inda dubban Mabiya Shehin Malamin ne da kuma Akidar ta Shi'a ne ,suka samu damar Halartar wannan taron.
Daga karshe an fara taron lafiya kuma an kammala lafiya. Sai dai kafin rufe taron da Addu'a , Mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky din Sun kara yin kira da babbar murya akan cewa Lallai gwamnatin Nigeria ta gaggauta sakin Malamin da mai Dakin sa . Tare da yin addu'o'i akan duk wanda yake da hannu a kan Kashe almajiran Malamin da kama Malamin. Akan Allah ya bimusu kadin abinda aka yi musu .
Wakilin Ma'asumah Nigeria🇳🇬 News Update.
~Auwal M Tukur
21/4/2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post