__FILIN JAGORAN GASKIYA___
To, kuma Bature (lokacin da ya zo da kafircinsa) ko kadan bai yi wa mutanenmu babarodo ba, bai yi musu rufa ido ba, bai kuma boye musu ba, bai ba su abin a dunqule ba, a warware ya yi musu komai! Kar ku ce ya zo ne ya ce musu; ga adalci, amma a baya ya boye musu kafirci, sai suka ga adalcin ne kawai ba.
Kun san haka Shaidan ya kan yi ko? Sai ya zo maka da abu, ya 1ce ga shiriya, amma bata ne, ko ya ce; ga gaskiya, amma qarya ce, ko ya ce; ga abu mai kyau, alhali mummuna ne.
To, shi Bature ba za mu iya ma zarginsa da cewa ya yi mana haka ba. Qarara ya zo da abin sa, ya kuma nuna mana cewa shi ne ma za a yi a madadin namu, bai boye ba sam!Na’am, ta yiwu ya shige ma wani duhu, amma ana iya cewa;
don me zai shigar maka duhu?Alal misali; an dade ana kashe wani Kwabo mai huji, ina jin da yawan mun nan sun san Kwabo mai huji, na san yara ba su sani ba, yanzu yaran da suka girma ba su san ma ana kashe kudi na qarfe ba.
Amma wanda suka san Kwabo mai huji, idan da akwai wanda ka voye a gida, ka dauko ka duba, bisa al’ada ma akan yi wani abu, akan yi kacici-kacici, sai a wurga Kwabo ko a mulmula shi a rufe, a ce; kan Sarki ko dammara? Sai ka ce; kan Sarki, sai a bude, sai a ce; wooo, dammara ne, ka fadi kenan.
Kun san mene ne kan Sarki? Kanbi ne na Sarauta wanda Sarki ke sawa. To, irin Kambi wanda Sarkin Ingila ke sawa, shi ne aka sa a bangare guda na Kwabo dinn. Idan ka duba da kyau a wannan, ga qaton Saqandami ya sa. Mene ne Saqandami? ‘Cross’, ga ‘Cross’ sosai wanda yake alamin Kiristanci (Nasaranci) ne, baya kuma ga dammara. Kun san mene ne ma’anar dammara din? To, wannan shi ne abin da Yahudawa suke cewa; ‘Tauraron Dawud’, wanda wannan shi ne alamar Yahudanci.
Mu dai mun san ba ruwan Bature da wannan tauraron, domin shi alami ne na Yahudu, shi kuma yana da ma’ana a wurin su (yahudawan), sun ce ainihin Daloli ne guda biyu (Triangle ne guda biyu), daya an birkita shi zuwa qasa, daya kuma yana duban sama, kuma duk cikarsu guda biyun sun yi musu alami cewa; yana nufin mallakar duniya a siyasance ne, da kuma mallakar arziqin duniya.
Daya yana nufin (mallakar arziqin duniya), daya kuma yana nufin mallaka ta siyasa.
Wato a taqaice abin da nake so in ce muku shi ne; kun ga alamomin nan guda biyu (da ke jikin Kwabon qasar mu), na Yahudu da nasara ne. Wato kamar ma masu wurgi da kwabon nan, su wurga su ce; kan Sarki ko dammara? Suna iya ce maka;Yahudanci ko Nasaranci? Domin daya Saqandamin nasara ne, daya kuma dammarar Yahudu ne.
Ka ga ashe wato kenan an nuna maka zahiran me ke iko da kai? Yahudanci da Nasaranci!To, sannan wanda ya fi kowanne zama qarara shi ne; abin da ya auku a Lokoja, wannan ya auku ne a watan Afrilu, bankiyaye ko nawa ga wata bane, la’alla ko daya ko hudu, amma masana sun ce; hudu ga watan hudu 1904 (4/4/1904), wanda
lokacin ne Bature ya haqqakar da muradinsa, ya kashe Sarkin Musulmi Attahiru a Bormi, yanzu kuma duk ya riga ya tabbatar da cewa ya dasa mulkinsa daram.
To, Lugard ya yi jawabinsa shahararre a birnin Sakkwato, ran 15 ga watan Maris 1903, inda ya fadi wata magana, (cikin abubuwan da ya fada a taqaice), ya ce; “Da can Fulani (kamar yadda ya ce) sun ci wannan qasa da yaqi, saboda haka suna da haqqin su mallaki qasar.
Amma yanzu mu dakarun Sarkin Ingila mun ci ku da yaqi! Saboda haka muna da haqqin mu mallake ku!”.
Jawabin Lugard din rubutacce ne yana nan a cikin littattafai. Amma ku lura jawabin a sarari ya nuna musu; “da can” (kamar yadda ya ce), Fulani amma mun san a fahimtarmu Fulanin nan yana nufin Shehu Usman danfodiye ne da almajiransa da ya ba tuta, mu kuma a fahimtarmu ba sunan su Fulani ba ne, ko da ko Fulani ne a jini, sunansu Musulmi, kuma mun san ba sun ci qasar nan ne da yaqi ba, a’a qasa ta yaqe su ne, Allah kuma ya ba su nasara, jihadi suka yi, ba sun zo ne suka ce; mu Fulani ne ba, ku ko ba Fulani ba, kamar yadda Bature ya zo ya ce; mu Ingilishi ne, ku ko Baqaqe.Amma danfodiyo ba cewa ya yi; mu Fulani ne, ku ko nan Habe ko Kado ko wani abu mai kama da haka nan ba, saboda haka ba yaqin Fulani ne da wadanda ba Fulani ba, sai Fulani suka yi nasara suka kafa mulki ba, wannan ba haka ba ne.
Zancen shi ne su wadannan Fulani ne ko ba Fulani ba, suna zaune a qasar ne, ‘yan qasar ne na asali. Kuma su Musulmi ne, suka ga kuma Sarakunan wannan lokacin suna gudanar da rayuwar al’umma ba bisa qa’idar addinin Musulunci ba, sai a bisa al’adu irin na gargajiya, suna kuma dora zalunci akan al’umma, suna dora musu kudin qasa da haraji a maimaikon Zakkah, wanda Allah Ta’ala shi ya dora musu.
Suna hada taqalidan Bori da ayyukan addini, wanda za ka ga Liman a lokaci guda, ba za ka raba shi da dan taba Borinsa ba, ko Sarki yana Bori, ko abin da ya yi kama da haka nan. Suka ce; wannan abin da kuke yi ya sava ma qa’ida, ya saba ma addinin Musulunci, ku zo ga abin da Allah ya ce, a tabbatar da iko bisa adalci kamar yadda Allah ya ce.
Sai Sarakunan suka yi fada da su, sauran talakawa suka amsa musu, Allah Ta’ala ya ba su nasara! Ka ga Jihadi suka yi. Mu ba mukan ce yaqin Fulaniba ne, ba mu tava cewa; yaqin Fulani ba, jihadi Shehu dan
Fodiyo ya yi.
Kun ga shi abin da Lugard yake hanqoron ya fada musu shi ne; da can Musulmi su suka yi mulki da qasar nan, amma mu kafirai, yanzu mun ci ku da yaqi, yanzu kuma mulkin kafirci za a yi! Amma ba haka ya ce ba, kila don kar wani ya gane, sai ya ce; “Da can Fulani sun yaqi qasar nan, sun ci qasar nan da yaqi, saboda haka suna da haqqin su mallaketa, yanzu kuma mu (Turawan Ingila) mun ci ku da yaqi, saboda haka mu muke da haqqin mu mallake ku)!”.
A lokacin suka kawo wanda za a nada Sarki, suka ba shi Sarauta, shi ma sunan shi Attahiru, ana mishi laqabi da Attahirun Alu.
Amma akwai bambanci tsakanin Attahirun Amadu, wanda suka kashe a Bormi, da Attahirun Alu da suka nada a Sakkwato. Wancan gyauron tutar Shehu ne, wannan ko na sabuwar tuta ne, daga ina ta fito? Daga Landan.
Ko daga wajen Shehu ta fito? Daga Landan ne! To, tuta daga Landan ana rubuta mata ‘La’ilaha illallah’ ne? Wato yanzu wannan Sarki ne, na’am (sunansa) Sarkin Musulmi, amma wakilin wanene?
Wakilin Sarkin Ingila!Akwai wata takarda na sha ba da misali da wannan takardar, don na karanta a littafi ne, wanda aka ce shi Lugard ya rubuta ma wani Sarki da ya nada a matsayin Sarki. To da yake takardar da Ingilishi aka rubuta ta, har ya fadi wata kalma, ya yi irin abin da ake ce ma gwari-gwari, ya ce; “Your Position is that of the ‘Wakil’ of the Governor General.” (Lokacin akwai ‘Governor Genaral’ a Legas). Ya ce; “Your Position is that of the ‘Wakil’ of the Governor General just as the Governor General is the Wakil of King of England.” Wannan a qarara kamar hasken rana ya fada, ya ce; “Kai matsayinka kai wakilin Gwamna ne (gwamna babba na Legas), kamar yadda shi kuma Gwamna babba, shi kuma wakilin Sarkin Ingila ne.” Ka ga kai wakilin-wakilin Sarkin Ingila ne kenan ko? Ko ba haka ba ne? Kai ne wakilin-wakilin Sarkin Ingila, qarara.
Ya ce kuma; Rasdan zai yi maka bayanin duk ayyukanka. Cikin ayyukan aka ce; aikin ka ne ka kawo rahoton duk wani wanda yake neman ya tada qayar baya. Wato aikinsa ne idan ya ga wani yana qira ya zuwa ga addini, ko a koma ga addini ko a koma tutar Shehu, ya yi maza-maza ya kai rahoto. ‘Ga wani nan yana nema ya kayar da tsarin mulkin ku ya kawo wani sabo!’Duk ina fadin wannan ne, idan ma wannan duk bai isa gwari-gwari ba, to a wannan rana da nake gaya muku, wanda nake tsammanin hudu ne ga watan hudu 1904 a birnin Lokoja.
Turawan nan sun tara duk Sarakuna a wani biki da su ka yi,suka tara su su ka yi musu bayani, aka ce musu; To! Yanzu da can abin da yake iko da qasar nan Musulunci ne, to daga yanzu ba shi ba ne! Kuma ma aka ce don ma ku gani (da idanunku), ina Alqur’anin da a da yake iko? Aka dauko Alqur’anin, aka kawo shi aka ajiye, aka ce wani Bature ya zo ya yi masa fitsari, kuma haka nan a gaban mutane ya kware al’aurarsa ya tsula ma Alqur’anin fitsari!!
Aka ce; To! Daga qarshe kun ga qarshen abin da yake tafiyar da mulkin ku a da!’ Kuma sai aka kawo tuta mai ‘La’ilaha Illallah’, aka ce; Kun ga wannan? To qarshenta ya zo!’ Aka balbala mata wuta! Aka dauko tutar Ingila aka tayar da ita sama aka buga Badujala! Aka ce; Kafin su yi wannan sai da aka aika Ingila aka kawo dakaru masu yawa saboda ko wasu za su tada qayar baya su ce ba su yarda ba.
Shi ya sa nake cewa; kyanshi wannan zuwan namu ma da mun yi shi ne a daidai lokacin cika shekaru 100 da faruwar hakan, kamar yadda muka yi bukin shekara 100 bayan Attahiru, wato a shekara biyu da suka wuce, shi kuma wannan da bara ya kamata mu zo, don ya dace da abin da suka yi, don su ma a irin wannan lokacin suka yi. Kuma watan wata rana insha Allahu sai mun zo wannan garin mun yi bukin ta da tutar ‘La’ilaha Illallah,’ da qona tutar Ingila!!
__________zamu cigaba__Insha__Allah____________/
Ma'asuma Nigerian News Updates,
[Jawabin Sayyid Zakzaky (h) Daga littafin Mulkin Mallakat turawa]
Tareda Wakilinmu
®__Mahadi__Tukur__Almizan.
__Inji Sayyid Zakzaky (h) [Jagoran Gaskiya]