""BABBAR MATSALAR QASAR NAN""

______FILIN JAGORAN GASKIYA___

""BABBAR MATSALAR QASAR NAN""


__daga bakin Sayyid Zakzaky (h)

To, ko da bisa hadari ne aka samu qasa sunanta NIJERIYA, kamar yadda muna iya cewa haka nan, ba mu ne muka taru muka ce; mun yadda sunanmu NIJERIYA ba, an maqala mana ne da qarfin tsiya.
Amma yanzu sunan mu dai muna da qasa sunanta NIJERIYA. To yanzu amma mu tambayar da ke gabanmu ita ce; wai shin a haka za a dunga tafiya ko kuwa? Ko da yake, sau da yawa idan ka yi wa wadansu wannan tambayar cewa; haka za a yi ta tafiya? Sai su ce; eh mana, a yi ta tafiya haka nan!

To, ga shi dai muna ganin rigingimu suna ta kunno kai, da rigimar qabilanci, da rigimar bangaranci, ana ta rigimar wane ne zai zama babban barawon qasa? ‘Yan Arewa sun ta kwasa suna kaiwa (Turawa), to yanzu ‘Turn’ din Yarabawa ya zo, to nan gaba kuma wanene?
Wasu sun ce sunan su Kudu-Kudu, ko a ba su ko a yi rigima! Wasu kuma sun ce sunansu Arewa, su ma sun ce dole sai an ba su! Ba wanda ya san in da za su jefa qasar nan saboda wannan abin da suke yi. Har yau ba wanda ya taba tsayawa ya yi tambaya ya ce; wai shin qasar nan akan me muka doru?
Kuma akan wane asasi muka doru? Akan me kuma za mu tafi? Wai ina muka dosa? Ina ne Alqiblar mu? Ina kuma muka sa gaba? Ba wanda zai gaya maka, gamu nan ne kawai! Ana ta kautar da hankulan mutane akan cewa; wane ya kamata ya zama shugaba! Kila ma a aukar da yaqi akan wannan.
Ba wanda ya tsaya ya tambaya cewa; wai shin tun asali me ya kamata ya zama asasin al’umma? Akan me al’umma take haduwa? Na’am, qasashen Turawa al’ummu ne daban-daban, amma sun doru akan asasi (muna iya cewa) na qabiloli, ko dayake su ba qabilu suke cewa ba, kamar Jamusawa, Faransawa, Italiyawa da ire-iren su, duk za ka ga suna da harshe, suna da al’ada, akan shi suka doru.Suna cewa; abin da ake ce ma qasa ko al’umma (wato ‘Nation’), shi ne; Al’umma wadda suka hada tarihi iri daya, suke da harshe iri daya, suke da addini iri daya, suke da al’ada iri daya. To, su qasashensu haka nan suke, su ‘Nation-State’ suke da shi, (amma mu Nijeriya ba haka ba ne).
A ‘Europe’ haka suke. Faransa qasar Faransawa ce, kuma suna da harshe da al’adar Faransanci, Jamani ma haka, Jamusawa ne su, haka ma Italiyawa suke, Ingila su ma haka nan suke, suna magana da Ingilishi, kuma suna da qasar Ingilishi, dadai ire-irensu.

Amma NIJERIYA fa? Ita ma al’umma ce? Ita ma irin wadannan ne? Ma su tarihi daya, da al’ada daya, da addini daya da harshe daya? Sai a ce; a’a. To tambaya za ta ta so; To me ya mayar da NIJERIYA ‘Nation’? Amsa: Turawan mulkin mallaka ne suka mallake mu a lokaci guda, Su ka hada mu, su ka ce sunanmu NIJERIYA! Shi kenan!To kowanne daga cikin irin wadancan al’ummun da muke ambatawa, irin su Faransa da Italiya da su Ingila din da suka zo suka bazu a nan su ka kakkafa qasashe, su suna da tarihi iri daya, kuma suna alfahari da wannan tarihin na su. Wanda qumajin al’umma ce masu tarihi iri daya, da al’ada iri daya, yasa sukan zabura domin kare wannan. Har su kan yi yaqi su sadaukar da rayukansu domin kare al’ummarsu, saboda suna ganin al’ummar ta su na alamta tarihinsu ne, da jininsu, da abin da suka yi Imani da shi. Amma Nijeriya ba ta alamta da wannanba!

To me ya alamta Nijeriya ta zama daya (wato ta zama ‘Nation’), tana da tarihi daya ne? Sai mu ce; Eh tana da‘Common History’, tana da tarihi daya. To, meye tarihin?  (tarihin shi ne); Shekara Sittin tana qarqashin bautar Ingilla, ka ji tarihin kenan! Yanzu za ka iya alfahari da tarihi wanda ya maishe ka Bawa? Yanzu da za a ce wadansu mutane sun zauna a qarqashin qangin bauta na wani mutum, za su iya haduwa, suce; mu ne tsofaffin Bayin wane? Sai kuma su yi alfahari da bautar?
Wato ita NIJERIYA ba ta da tarihi wanda za ta yi alfahari da shi, shi ya sa kuma ba zai yiwu a yi kishin NIJERIYA ba.
Idan ‘yan qasanci yana zaburar da mutane har su je su bayar da jininsu su yi yaqi, to kishin NIJERIYA ba zai taba zaburantar dawani ya je ya ba da jininsa ba! Duk wanda ka gan shi yana cewa; Nijeriya-Nijeriya, musamman ma yanzu, wallahi qarya yake yi, shi ne Nijeriyar! Idan komai ya yi masa daidai, to shi kenan NIJERIYA ta yi daidai kenan. Idan bai yi masa daidai ba,to Nijeriyar ma ta wargaje! Haka ma duk wanda za ka ji yana cewa; Kudu-Kudu, shi ne kudun, idan komai ya yi masa daidai, shi kenan, idan bai yi masa daidai ba, Kudun ma ta wargaje! Haka nan ma duk wanda za ka ji yana cewa; Arewa-Arewa, ba wani Arewa nan, kansa kawai, shi ne Arewan! Ko kuna tsammanin akwai wata Arewa ne? Ya aka yi aka samu Arewar? Ba sai da aka sami Kudu ba, sannan aka yi Arewa?Idan ka ji mutum yana ta ware baki yana; Arewa-Arewa, mu ‘yan Arewa, to shi ne Arewan! Idan Arewar ta yi masa daidai, ya ci gajiyar Arewar, shi ne aka ba shi kaza a Arewar, ya ci shi kadai, to Arewa kenan. Idan ko aka fitar da shi (daga gwamnati), ba a yi da shi, sai ka ji yana cewa; an yi banza da Arewa! Ba a yi da Arewa! To, har yaushe za a yi ta kada mutane haka nan kamar Shanu?

_______________________________________
Ma'asuma Nigerian News Updates,
Jawabin Sayyids Zakzaky (h) Daga Littafin ""Mulkin Mallakar Turawa""

Tareda Wakilinmu,

©___Mahadi Tukur Almizan.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post