ANA CIN YANKAN MUSULMI KO DA BAI AMBACI SUNAN ALLAH BA <*> } !!!

 

Muslimci addini ne wanda ke tsarkake ma'abucinsa, matuqar mutum ya amsa sunan muslimci kuma yana aikata shi, to ya tashi daga najasa.

Shine wanda zaiyi yanka ka ci, kuma ba ka hujjar qin cin yankansa matuqar ya san qa'idar yankan, kuma ba haqqinka bane bincike a kansa.
Allah (T) ya umarce mu da muci abinda aka ambaci sunansa a kansa, har ma yake qalubalantarmu cewa wacce hujja ce a gare mu da ba za muci abinda aka ambaci sunansa a kansa ba?
To, ba ma batun ambaton Allah ba, ko ma wanda ba a ambata bane za aci matuqar musulmi ne ya yanka.
Darul-Qudniy ya riwaito daga Ibn Abbas (R.A) yace, " IDAN MUSULMI YAYI YANKA AMMA BAI AMBACI SUNAN ALLAH BA, TO KUCI, DOMIN MUSULMI CIKINSA AKWAI SUNAN ALLAH ".
(Sunan-Darul Qudniy, J:4, Sh:95).
Shi kuma Baihaqi ya qarfafa hakan daga hadisin A'isha inda take cewa, " Mutane suka ce, yaa Manzon Allah, lalle mutane suna zuwa mana da Nama, amma ba mu san shin sun ambaci sunan Allah a kansa ko a'a ba ".
Yace,
" KU KU AMBATA A KANSA KUMA KU CI "!
(Bukhari, J:7, Sh:120).
===== ABIN DARIYA =====
__________________________________
Wata rana mun tafi wajen taron qarawa juna sani (workshop/semina), da aka kawo mana abinci sai naga kowa an dora masa rabin Kaza a kan abincin nasa, sai nake cewa wani mai irin wannan fahintar, idan ba za kaci Naman ba ka bani.
Nan da nan sai naga ya soma zazzare idanuwa yana waige-waige ya rasa abinda zai ce, amma fa bai haqura da Naman ba ya cinye shi kaf ! Alhali bai san wanda ya yanka ba.
Shine nake cewa ashe dama abin iskanci ne kawai !

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post