__A LURA DA ABU BIYU_



___FILIN JAGORAN GASKIYA__

__A LURA DA ABU BIYU_

__Inji Jagoran Gaskiya [Sayyid Zakzaky],


_Zan so na tunatar da mu cewa, wannan al'amari na (halin da muke ciki), tushensa biyu ne; Na farko tsarin da ya fandarewa na Allah, kuma muka yarda da shi. Na biyu kuma tsarin nan abin da zai haifar shi ne fajirai, fasiqai, azzalumai su zama sune shugabanni. Wannan tsarin ba yadda za a yi ko Mala'ika ne ya tafi da shi! Ko Mala'ika ya sauko daga sama wanda bai taba zunubi ba, ka ce shi ne Shugaban qasar nan, dole sai ya zama Azzalumin Mala'ika. Saboda haka duk wanda ke shugabantar tsarin Azzalumi ne, ba kuma yadda zai yi ya tashi a zalunci, saboda tsari ne da ma bisa zalunci aka shirya shi. Fima-labudda azzalumi zai zama shugabanta. Kuma dole da ma mutane in
suka zama haka nan su zama fasiqai da fajirai.

Muna iya ganin yadda wannan al'amari yake, muna zaune a qasar nan, ba a yi fari ba, bara da bara wancan an sami abinci baje-baje, amma duk da haka ana fama da rashin abinci. Qasar nan na cikin qasashen da suke da arzikin man fetur, amma qasar nan yanzu ba man fetur. Ga Nijar, busasshen wurin da ba ko man fetur guda, amma har suna kukan cewa yanzu har fetur din ma ya yi masu yawa. Me ya janyo wannan? Masarar da muke shukawa da Dawa da Gero da sauransu, haqa rami muke muna zubawa, ko kuwa cinyewa muke yi? Kuma Mai din ina yake?
Idan ya zamana kenan azzaluman da yake ba rahama a zukatansu su suke tafiyar da al'amari, wanda yake da ma tabbas in aka fitsare wa Allah da ma azzalumai ne za su yi shugabanci, ba su da tausayin kowa, har ma su sanya a yi Giya da Dawa ya fi masu a ci a kasuwa. Kuma su kadar wa qasar waje da dukiyar qasa, har da Mai xin da ake taqama da shi ya fi masu, a yi masu gida a Paris ko London ko New York, a zuba masu kudi a Banki suna yi suna komawa can suna fasiqanci, Aljannarsu kenan, ya wadace su hakan.

Za su iya kadar da qasar da duk wadanda suke ciki, ko su mutu, ko su yi rai!Wannan kuma haka al'amarin yake. Ba mamaki in ya zama dukiyar qasar nan kadarwa aka yi a boye. Kamar Mai, a gano a boye wata takarda cewa ma daga nan zuwa shekara dari, Man ma ba naku bane, su wadanda aka kadar ma qasar sun riqekayansu ne.
Kuma ba mamaki, ya zama sananne ne, kan cewa abin da ake nomawa saye shi ake a kasuwa. Lokacin da aka yi wani fari nan a Habasha da Sudan, sai ga Amerika na kai Dawa da Gero, wai gudummawa. Muna iya tambaya, a ina ake noma Dawa da Gero a Amerika? Dawarmu aka kwasa aka kai can! Sannan kuma bayan dimbin hatsin da ake diba ana sarrafa su a masana'antu ana yin Giya, ko kuma a diba a yi waje da shi don a yi giya a qasashen duniya, wanda yake wadanda suke tafiyar da
al'amari ba rahma gare su ba balle ya dame su.

_______________________________________________________
Ma'asuma Nigerian News Updates,
[Jawabin Sayyid Zakzaky Daga Littafin Nigeria Ina Mafita]

__Mahadi__Tukur__Almizan__

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post