Yin "transfer" na data MB (wato tura data MB) a layin MTN abu ne mai sauki.
Da farko dai, dole ne ya kasance ka sayi data a layin ka na MTN. Sannan dole ne ya kasance ka yi rajista da "MTN data share" ta hanyar buga *131*2*1# ko aikawa da sakon SMS/text da kalmar "REG" zuwa 131. Za su aiko da sako kamar haka: "You have successfully registered for data share & gift data! Your default PIN is 0000. Dial *131# to change your PIN now."
Wakilan Ma'asumah Nigerian news Jim kadan bayan ziyartar Shek yaqub yahayayya katsina |
Shikenan! Daga yanzu idan kana son tura ma wani kyautar MB kawai sai ka danna 131*2# sai ka buga, zai jero maka abubuwan zaba a cikin sako. Sai ka zabi "3" (share data). Wato ka danna "reply" ko "answer". Sai ka danna "3". Ko kuma kai tsaye ana iya buga *131*2*3#. Bayan haka sai ka zabi adadin MB din da kake son ka tura. Sannan sai ka shigar da lambar wanda kake son ka tura ma. Zai tambaye ka PIN, sai ka sa "0000" ko kuma idan ka canza PIN, to sai ka sa sabon PIN din ka.
Za ka iya canza PIN din ka daga 0000 zuwa wasu lambobi guda hudu na sirri wanda kai kadai ka san su, kuma wanda ba za ka manta su ba. Domin canza PIN din sai a buga *131# sai a zabi 2, sannan a zabi 5. Ko kuma kai tsaye a buga *131*2*5#.
Ku gwada yanzu!
Tags:
Yanar gizo