Neman a zabi Nasiru Elrufai ya haukata mayunwata daga cikin Malaman Izala
JBWIS |
MSN_012
Wai yanzu saboda rashin kunya da iskanci, Kabiru Gombe ne ke cewa wai da su da yan Darika daya ne bayan kowa ya san suna kiran su Kafirai, Mushrikai da ba a cin yankan su don kawai yana yiwa Elrufai campaign.
Wai sai ga shi an kawo shi campaign a shago mai loud speaker a T/Wada a Kaduna yana lashe amai da suka yi na shekaru da dama don kawai ya yaudari mutanen Kaduna su zabi Elrufai.
Har tunzur mutane yakeyi wai cewa Elrufai na kashe yan Shi'a da Kirista saboda haka wai shi zasu zaba. Ko ya akeyi makashi na zama maceci?
Alhali mutanen Kaduna ba su son Elrufai ne saboda mulkin kama karya da rashin mutunci da rashin adalci da yake musu.
Ba su sonsa saboda cin zarafin mutane musamman ma'aikata, sarakuna, hakimai da Malaman makaranta.
Ba su sonsa saboda ya rayar da rikicin addini a tsakanin mazauna jihar domin biyan bukatarsa da son zuciyarsa.
Kowa na sane cewa babban Dan jarida kuma Dan Izala Alh Tukur Mamu yayi suka ga Kabirun lokacin da Elrufai ya raba masu kudade da motoci don su yi masa campaign.
Har ma yake cewa duk cikinsu da ya tonawa asiri in da mai ja akai, ya kaishi kotu. Amma har yanzu shuru kake ji ba su je kotu ba don ba su da gaskiya.
Amma don rashin kunya sai ga shi wai yau ana hawa mumbari ana cewa wai an zama daya da yan Darika alhali a zuciyarsa su Kafirai ne kuma Mushrikai da ba a cin yankansu, ba a binsu Sallah, kuma ba a basu aure.
Basu yarda sun janye wadannan miyagun maganganu akan Musulmi ba don Allah sai don Elrufai ya basu cin hanci su taya shi yaudaran mutane da sunan addini don su zabe shi.
Kuma a Dariqan basu bar kowa ba, ko Kadiriyya ne ko Tijjaniyya. Yadda suke kulla masu sharri don ci da addini haka suke yiwa yan Shia. Har ya kai ga cewa sharri da kareraki da suke yiwa yan Shia ma ya wuce misali duk don ana basu kudi. Saboda kudi da ci da addini da suke yi komai suna iya yi ko da ya saba wa addini. Su haramta halal, su halasta haram, su karkata fassarar Kur'ani duk don azzalumai na biyansu.
Ko da yake dai, Sheikh Dahiru Bauchi ya jima da basu amsa akan cewa gara Kirista da irin wadannan Malaman domin Kirista sun yarda cewa yan Darika Musulmi ne amma mayunwatan Malaman basu yarda ba.
Shi wannan shedanin ma har ayar Kur'ani ya kawo yana cewa wai Allah ne yace da dan APC da dan APC yan uwan juna ne duk don ya biya bukatan son zuciyarsa da ta wanda ya bashi kwangila. Ko ina Allah ya saukar da wannan aya? Oho!!
Su dai Harka Islamiyya da suke cewa yan Shi'a ba ruwansu da wannan kwamacalan siyasa da suke yi kuma kowa na addininsa ne bisa fahimta da fata, hisabi kuma sai an je gaban Allah ba shedanun malamai me yi ba.
Wani abu kuma shine cewa Najeriya ba ta yan Izala bace, ba ta yan Darika bace, ba ta yan Shia bace, ba ta Kirista bace, TA YAN NAJERIYA CE. Kuma kowa a Najeriya na da yancin yin addinin da ya fahimta.
Saboda haka irin wadannan mayunwatan malamai da Sheikh Dan Fodio ya kira malaman fada dole ne jama'a su guje musu da irin fitintinu da suke yadawa a cikin al'umma.
Tags:
Labaran Duniya