@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED
Wani lokaci dariya kawai nake yi in naga an rubuta ko naji ance Sayyidinah Ali (R.A) shine na kaza a karbar muslimci.
Abinda mutane suka karanta ne kuma suka kasa fahinta, idan ka ji ance wane ya muslimta to, da can kafin wannan lokaci yana kan wani addini ne na dabam ba muslimci ba, saboda haka in ya bar wancan addini na farko ya dawo cikin muslimci sai ace ya muslimta.
Za ka iya fahintata cikin sauqi in har ka iya tuna cewa ba ka taba jin ranar da aka ce ita ce Manzon Allah (S.A.W W) ya muslimta ba, sai dai ace ranar da aka aiko shi a matsayin Manzo. Dalili kuwa shine, dama asalinsa musulmi ne, bai taba yin wani addini ba.
To, shima Imam Ali (A.S) haka yake, bai taba yin wani addini koma bayan muslimci ba, domin tare da Manzon Allah (S.A W.W) yake tun yana dan shekara 6, sannan kuma lokacin da aka aiko Annabi a matsayin Manzo bai balagha ba (Ali).
WASU RUBUCE-RUBUCEN MU:Kana zagin shugaban muminai kana yabon Azzalumi..!!
Abinda yayi kawai shine jaddada bai'arsa ga Annabi (S) yayin da aka ce ya bayyanar da wannan addini nasa ga sauran mutane.
Ko kun manta hadisin nan ne da ke cewa;
" DUKKAN WANI ABIN HAIHUWA ANA HAIFARSA MUSULMI NE, SAI DAI MAHAIFANSA SU YAHUDANTAR DA SHI KO SU NASARANTAR DA SHI."
Kuma kun san Yahudanci da Nasaranci na nan tun kafin a aiko Annabi (S.A W.W) a matsayin Manzo.Haba 'yan'uwa, ayi nazari mana! Ba kwa gani dukkan wanda ake cewa shine farkon muslimta daga cikin manya ko kuma ace mutanen da suka fara karbar muslimci daga cikin maza ko mata ko Bayi sune wane-da-wane, wance-da-wance? Kenan da suna kan wanin addinin muslimci ne. Da kan addinin muslimci suke da ba za ace sun muslimta ba.
Imam Ali (A.S) ya shafe tsahon shekaru 6 ko 7 a wata riwayar yana yin sallah tare da Manzon Allah (S) kafin wani ya muslimta, in ba Sayyidah Khadijah (S.A) da ta kasance tare da su cikin muslimci yayin da aka aiko Annabi a matsayin Manzo ba.
Duk wata fikira kyakkyawa da kuka ganta tare damu, wallahi mun same ta ne albarkacin wannan bawan Allah Sayyid Zakzaky (H).
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470-08137925034
Tags:
Munasabobi