Tare da Wakilinmu Muhammad Aliyu Daud (Dansudan) Azare* *070-32803940
A mulkin Buhari daya shige, zangon farko kenan wanda zamu iya ce masa "pass level" hawan Buhari mulkin da wata shida kacal ya tura sojoji Zariya suka yi ta kashe mutane mabiya shehin Malaminnan wato sheak Ibrahim Zakzaky, suka yi ta'addancin da ba a taba irinsa ba a duniya, sun kashe mutane sama da dubu maza da mata, yara da manya da dattawa, mata masu juna da jarirai wanda Allah ne kadai yasan adadinsu.
Badan komi ba sai don sunce Allah za subi ba "constitution" ba, wanda kowa yasan "constitution" kafirci ne, binsa kangarewa Allah ne. A cikin Al-Qur'ani Allah yana cewa, *"SUMMA JA'ALNAKA ALA SHARI'ATIN MINAL AMRI FATTABI'AHA, WALA TATTABI AHAWA'ALLAZINA LA YA'ALAMUN"* Sannan muka sanyaka akan shari'a akan kowane Al'amari, kabi kada kabi son zuciyar wa 'yanda basu da ilimi". Wannan dalilin yasa gwamnati ta tsanesu take kashe su.
Tabbas bijire musu da tawaye agaresu shine tsirarmu duniya da lahira, Don sun kasance azzalumai, kowa kuma yasan makomar azzalumai da kuma wanda ya bisu ya yi musu da'a, makomarsu daya ce. Eah mai karatu su azzalumai ne da fadar Allah ba tawa ba, acikin Al-Qur'ani Allah ya ce *"WA MANLAM YUHAKUM BIMA ANZALALLAHU, FA'ULA'IKA HUMUL ZALIMUNA"* Duk wanda bai yi hukunci da abinda Allah ya saukar ba toh shi Azzalumi ne! Toh kaji mai karatu.
Kada ka yi tunanin wai za su shiriya a gaba, a'a ai sun riga da sun bata, saboda Allah yace a Al-Qur'ani *"INNALLAHA LA YAHADIL QAUMALZALIMUNA"* "Lallai Allah baya shiryar da mutane Azzalumai."
Kaga mai karatu baka da mafita sai In ka yi musu tawaye kamar yadda Manzon Allah ya yi wa Quraishawa har addini ya tabbata, kaima abinda ake so ka yi kenan, ka samu uzuri a wajen Allah.
Shine abinda Sayyid Zakzaky(H) ke kiranka a ka yi, kada ka halaka kazo ka samu tsira anan duniya da lahira.
Ka amsa masa ka samu damar yin fahimtarka ta addini da 'yanci, musulmai su sakata su wala, tutar *"LA ILAHA ILLALLAH TA DAGA A WANNAN QASA TAMU, YA ZAMANA CEWA KOMI ZA A YI SAI ANCE QALALLAHU QALA RASULU"* Ba wai yana kira kazo ka yi Shi'a ba, A'a Sam yana kiranka kazo ka temaki addinin Allah ya daukaka, ka samu damar yin fahimtarka ta addini duk yanda kaso.
Mu kuma rabu da wannan musibar da take damunmu a kullum kuma karuwa take, nasan baza ka yi musu ba Inna ce don anbar Allah ne yasa muke cikin wannan hali, mai karatu wallahi mafita tana hanunsa ka amsa masa, musamu mafita duniya da lahira.
Wannan yasa gwamnati ta farmasa shida mabiyansa tanason ganin bayan kiran da yake, tun daga hawanta kisa take a lokuta mabanbanta, har wa'adin zangon mulkin farkon yakare, saboda batason addini, ya tabbata wanda shine kadai zai taka musu birki ga zaluncin da suke, shine kadai mafitar talaka najin dadin duniya da lahira. Yanzu gamu a zangon mulki na biyu mudaku shege ka fasa addini ba fashi musulunci shine a sama, har abada baza muyi muku da'a ba.
Gwamnati don ki shina gamu a "Next level" kamar yadda kika ce, mudaku shege ka fasa, mu munce addini za muyi, ku kuma kunce addini za ku rusa, sai Allah ya yi hukunci a tsakaninmu, Allah yana tare da bayinsa muminai.
*#FREE ZAKZAKY(H) WA UMMUNA ZEENAH*
*DANSUDAN AZARE 07032803940*
Tags:
#FREE_ZAKZAKY