Ni Sakina Ahmad sai Balkisu Usman da Sauran wakilanmu Mata a wajen Taron karawa juna sani da wakilan Ma'asumah muka Shirya a Katsina
Daga Ma'asumah Nigerian News Update
Rubutawa SAKINA AHMAD KAZAURE
Ita ɗin Ɗaya ce daga cikin jikokin Manzon Allah (S) itace jika ta uku, ita ƙanwa ce ga Imam Hussan da Imam Hussain.
Sunanta Sayyida Zainab (sa) an haife ta ne a birnin Madina ranar Juma'a 5 ga watan Jimada Ula shekara ta biyar bayan Hijara,
Mahaifinta shine Imam Ali bn Abi Dhalib (As) Mahaifiyarta kuma itace Sayyidatul Nisa'il Alameen wato Sayyida Zahra Ƴar Ma'aikin Allah (saw).
Tayi Aure bayan rasuwar Mahaifiyarta da wasu shekaru, Sunan mijinta Sayyid Abdullahi bn Ja'afar bn Abu Ɗhalib sun haifi Ƴaƴa biyar (5) tare dashi huɗu maza ɗaya mace wato Aliyu, Aunu, Muhammad, da Abbas, sai kuma Ummu-Khulsum. Biyu daga cikinsu sunyi Shahada a Karbala da Imam Hussain (As) Abbas kuma babu wasu alƙaluman bayanai game dashi, Wala Alla ya rasu ne tun yana yaro ƙarami, amma shi Aliyu ya girma har-ma yayi aure ya haifi Ƴaƴa ana kiransu da suna " Aliyul Zainabiy" ta jikinsa ne zuriyar Sayyida Zainab ta wanzu, ake kiran zuriyar da (Zainabiyyun)
La-Alla Ummu-Khulsum itace Ɗiya babba a wurin Sayyida Zainab (sa) domin itace ta girma har tayi aure tun Imam Hussain yana raye saboda Imam Hussain ɗinne ya aurar da ita ga ɗan baffanta wato Alƙasim bn Muhammad bn Ja'afar Ɗayyar, kafin Imam Hussain ya zaɓa mata miji seda yayi Addu'a ta Musamman ga Allah Ta'ala yace ya Rabbu ka bawa wannan Baiwa taka dacewa da miji Yardajje awurinka daga zuriyar Annabi (saw).
--
Imam Hussain ya aurar da Ummu-Khulsum ga Alƙasim akan sadaki dirhami 480 kuma sun sami zuriya mai Albarka a tsakaninsu.
==
Sayyida Zainab tayi mafi yawan Rayuwarta ne amadina, tayi Aikin Hajji da dama, ta rayu a birnin kufa na ƙasar Iraƙi a lokacin Khalifancin Babanta, tayi tafiye tafiye zuwa Iraƙi Dimashka (Demascus) da kuma birnin Misra,
Sayyida Zainab (sa) ta gaji kyau na Mahaifiyarta Sayyida Faɗima Azzahra (As) ta gaji Shafa'a da Jarumta na Mahaifinta Imam Ali (As) ta gaji kwarjini da haiba na ɗan Uwanta Imam Hassan (As) ta kuma gaji Juriya da Haƙuri na Ɗan Uwanta Imam Hussain (As).
Ta rayu a duniya tsawon shekaru hamsin da bakwai (57) kuma ta rasu ne a shekara ta 62 bayan Hijira ƙabarinta yana Dimashka (Demascus) ƙasar Siriya ko kuma muce birnin Misra ahalin yanzu.
----
Sayyida Zainab tana da fitattun mawaƙa da suke rero baitocin Yabo da jinjina, gwarzantawa da suke mata daga cikinsu akwai Allama Muhammad Isfahany, Allama Miraz Muhammad Aliyul Arwiy, da Sheikh Miraza Muhammad Najafy, da sauransu.
Hakama a Nigeria Fitattun Mawaƙan Ahlul-bayt (As) da yawa sunyi waƙoƙi ga Sayyidah Zainab (sa) daga ciki akwai Alhaji Mustapha Umar Baba Gadon Ƙaya, da Sidi Uzairu Badamasi Kano, Malam Nasiru Fudiyya, Malam Yunusa Saminaka, Malam Zahraddeen Lawan Kazaure, Shaheed Alhaji Shafi'u Kazaure, Ina Rabauta Group da dai sauransu.
KARAMAR SAYYIDA ZAINAB BINTU ALI (AS)
Wakiliyarmu Sakina Ahmad kazaure a wajen Taron na Wini biyu a garin katsina da shafin nan ya shiryawa wakilan shi dai-dai suka fito daga garuruwa daban daban |
Bisa Ɗabi'a Dukkan Manyan Bayin Allah Tsarkaka Masu cikakkiyar daraja basu rasa mu'ujiza da kuma wasu karamomi na musamman, to hakan ne ya faru ga Sayyidah Zainab domin tana da ɗinbin karamomi masu yawan gaske, daga karamar Sayyida Zainab.
An ruwaito cewa a daren da Sayyida Zahra ta samu cikin Sayyida Zainab (sa) ta kasance cikin murna, cikinta baya mata ciwo, goshinta yana haske, kamar hasken rana,
Lokacin da Sayyida Zainab ta cika wata tara a ciki, haihuwa bata zowa Sayyida Zahra da wahala ba ko raɗaɗi Sayyida Zahra tana cewa "ina durƙushe banji ciwo ko zafin haihuwarta sai naga haske ya ya haske gidan har sai da gidan ya cika da haske da iska mai daɗin ƙanshi, ina wannan yanayi sai kawai Naji na haifi Ƴata Zainab (Sayyida Zainab)
Lokacin da aka haifi Sayyida Zainab anzo da ita cikin farin ƙyalle aka miƙata ga Mahaifinta Imam Ali (As) akace ya sanya mata suna, sai yace bazan rigayi Manzon Allah (S) sanya mata suna ba, a lokacin kuma Manzon Allah baya gari aka jira har saida ya dawo, isowarsa keda wuya aka masa Albishiri da haifa masa Jikanya, Manzon Allah yayi murna matuka, ya zarce gidan Sayyida Zahra ya ɗauki Jikanyarsa ya rungumeta yana murna da farin ciki yana godiya ga Allah (T) daya bashi Jikanya ta farko amata, sai aka bukaci Manzon Allah ya sanya mata suna, sai yace bazan rigayi Ubangiji sanya mata suna ba, zuwa jimawa sai ga Mala'ika Jibrilu (As) ya sauko yace masa mai girma da ɗaukaka yana gaisheka kuma yace ka sanyawa Jaririyar suna ZAINAB haƙiƙa Allah ya zaɓar mata wannan suna, duk da cewa ba kanta ne aka fara raɗa suna Zainab ba amma nata saukakke ne da wurin Ubangiji.
LAƘUBBAN SAYYIDA ZAINAB BINTU ALI (AS)
"
Sayyida Zainab tana da laƙabi da dama da ake kiranta dasu, masana sun jero laƙubba kusan 50 da take dasu wasu laƙubban ana kiranta dasu ne saboda girman sha'aninta da karamominta daga cikin laƙubbanta ana kiranta da:-
Aƙila, Kamila, Sabira, Badiyya, Muhaddasa, Asirah, Mazlooma, Aminatullah, Karbala, Ka'abatur Razaya, Siddiƙatus Sughra, Aƙilatu Bani Hashim, Ummul Musa'ib, Kurratu'ain, Khalisah, Mujahidah, Amilah, Faadimah, Zahidah, Abidah, Rakiyah,
Wannan ataƙaice kenan rayuwar Sayyida Zainab (sa)
Allah Ta'ala Ya haɗamu a Ceton A'Immatul Huda (As)
12-02-2019
Wa zainaba
ReplyDelete