BALA’0’IN DA ’YA’YAN FATIMA (AS) SUKA SHIGA
A cikin jawabinsa da ya gabatar a taron makon zahra (As) a shekara ta 1417 (1996) a dakin taro na Otal din kongo dake zariya.
In nata ya 6uya maka, akalla na Hasan da Husain bai 6uya maka ba. Ina lya karanto maka wasu daga ciki. Imam Hasan kashe shi aka yi da guba wadda matarsa ta sa masa. Kuma bayan da ya ci, ta tabbata lallai ya ci guba ne sai ya tsine mata albarka. An shirya da ita ta sa masa guba din a kan za a ba ta kudi kaza kuma za ta auri dan Sarki.To da ya tabbata cewa yasan yanxu ya kama ciwo, kuma ya san ya kusa mutuwa saboda ya san guba aka sa masa, ita kuma suka rabu da matar, musamman ya aika yana neman. To yanxu in ya mutu a binne shi kusa da Kakansu. wasu suka ce atafau ba za a binne shi kusa da Annabi ba. Har suka hawo dawakai suku ce basu yarda ba. Sai ka ce bashi da dangantaka da annabi, Wai ba za a binne hassan kusa da Annabi ba. Sai imam Hassan ya ce in haka ta faru a binne ni a Baki‘a. Har suka zaro takubba a kan cewa ba za a binne shi kusa da Kakansa ba. Basu kuma shakkar matsayinsa.
Ya ishe ku misalin wacce aka kira sayyidatu Nisa‘il Alamina. aka kira ‘ya’yanta Sayyidah Shabbabu Ahlul janna. Amma da ake lissafin goman da aka yi masu albishir da Aljanna an manta da su. Ba su a ciki. Ko su an yi masu albishir da wuta ne ban sani ba. Wadanda aka ce Sayyidah Shababu Ahlul janna. wane albishir kuma kake jira? An ce sune su biyu Shugabanni ’yan Aljanna samari. ke kuwa ba ma ’yar Aljanna kike ba. duk wanda yake qaunarki ma za shi Aljanna. Ke ce Sayyidatu Nisa‘il alamin. amma B sunansu a cikin wadanda aka yi masu albishir da shiga Aljanna. Kuma kun san cewa tabbatacce ne Mahaifiyar Fatima (AS) an yi mata albishir. wanda Annabi ke cewa. Allah na yi miki albishir da gida a Aljanna wanda aka gina shi da Yakutu da Zabarjad. Kun ga sunanta a cikin Ashratul mubashshara? Ita ba a yi mata albishir din ba kenan. An manta da hadisin.
Kuma kun san Bilal, Annabi ya ce Bilal me kake yi nake jkn motsin kafarka a cikin Aljanna kana zuwa wajena? Kun ga sunansa a cikin Ashratu mubasshara? An manta da shi. A ce shi ma ba shi a ciki. Ina ba ku dan misali ne don ku fahimci akwai wasu mutane da ba a so nasu addinin ba saboda haka sai aka manta sai aka kawar. Ambaton sunansu ma hadari ne.
To amma yanzu Allah ya ga daman al’amarinsa ya bayyana. tunda yake in ka ce da can wasu wadanda ba su so addinin bane. suka fake da rigarsa suka yi danniya, to yanzu ba su. Ba ma ma’abota addinin ke riqe da duniyar ba. In aka tambaye ka wa ke riqe da duniyar? Za ka ce musulmi? Ba musulmi ke rike da duniya ba. Yanzu Yahudu da Nasara ne, su suke riqe da duniya, su suke mallakarta. Saboda haka ran da Allah (T) ya dago addini fima labudda zai dago shi ne a hannun Ahlul baiti. Kuma dama wannan rubutacce ne, da su ya fara da su zai qare. Kuma yanzu alhamdulillahi muna ganin alamomi da daman gaske. Isharorin da daman gaske wadanda suke nuna mana wala'alla a lokacin ya kusa. kila ma in muna da rabo mu kasance tare da ma'abota su.
Ba zan tsawaita muku magana ba. Kamar yadda nake cewa, ban san menene aka fada,menene ba a fada ba, amma wannan magana da na yi ina fada, ina nanatawa, akwai buqatar kar ka tsaya kawai sai an zo an yi lacca a ‘hall' kamar wannan. sai kaji an fadi wata magana sa ka je ka ce kai ba ka san wannan magana ba. ba haka bane. Domin nan ba ajin karatu bane. ba zauren karatu ne ba,nan bayan an ta6a karatu ne aka zo ana tunatar da juna. Saboda haka in ma kaji wani abu kai ba ka san shi ba, to kamata ya yi ka je ka bincika har ka san shi daga tushen inda aka samo. ln ma abin ya yi maka bambarakwai, ka ce ina aka samo wannan magana? Kana iya tambayar wanda ya gaya maka. A ba ka ka bincika kai ma. Sannan sai ka gano da naka ilimin ccwa ba gaskiya bane. sannan sai ka zo ka ce ba gaskiya bace wannan magana. Amma kar kawai don ba ka ta6a jin magana ba ka ce wai ba haka bane saboda kai ba ka ta6a ji ba, akwai shi haka nan, kai ba ka ta6a sani ba, kuma rashin saninka ba yana nufin ba haka bane.
Ko wadannan 'yan misalan da na ba ku ya ishe ku ishara kan cewa lalle an 6oye wani abu. Kamar misali hadisi nawa ka ji an ce an wane, an wane, an Fatimatuz Zahra, an Rasulullahi Kala kaza, guda nawa ka ji? Babu! Illa nadiran. Haka kuma guda nawa ka ji an ce an wane, an wane, an wane, an Hasan dan Ali ya ce ya ji Kakansa ya ce? Hadisi nawa ka sani? Shi bai ji hadisin bane? Ko kuma hadisi nawa ka ji an ce an wane, an wane, an Husaini bin Ali (R) qala, kala Rasulullahi (S)?
Akwai wani da aka ce yana makewaya ya haddace hadisin qunuti da kuma“da’a ma yaribuka ila ma la yaribuka. ”Su hadisan da suka sani kenan. Wannan ya haddace hadisin kunuti, wancan ya haddace hadisi guda. Kila ka samu wasu ruwayoyi jefi-jefi, amma ba a wani babi muhimmi ba..Banda a wata matsala muhimmiya wacce ta shafi kamar zakka, humusi, yaki, wilaya ko fassatar Alkur’ani, duk ba za ka gani ba. Ka dinga ganin Hasan, Hasan a fassarar Alkur’ani, amma Hasan din ba wannan bane, Hasanul Basriy ne, amma babu na Hasan . Dan Ali, shi bai san Alkur’anin ba. Wannan ya ishe ka ishara cewa anya zai kasance haka nan kuwa? In ko wadannan mutane suka wanzu da darajojin da Allah ya yi musu, wanda yake kuma ba a musanta darajar ba, ba a musanta ita ce Sayyidatu Nisa’il Alamina ba, ba musanta cewa a gidan wahayi aka haife ta ba, ba a musanta cewa a gidan wahayi ta girma ba, ba a musanta cewa tare da Manzon Allah ta kasance ba, ba a musanta cewa Manzon ya fi son ta ba.
Rubutawa:haruna shuaibu.