..KANA ZAGIN SHUGABAN MUMINAI KANA YABON AZZALUMI..!!!

Daga Ma'asumah Nigeria news update


Tare da M.s.n.006

Hujur bn adi al-kindi wanda akewa lakabi da Abu abdurrahman, Yana daya daga cikin sahabban manzon Allah (s.a.w.w) Ya kasance sahabine Mai tsananin ibada da son iyalan gidan manzo hakan yasa sahabbai da dama suke girmamashi musamman wadanda suka yi zamani dashi bayan wafatin manzon Allah (s.w.w).

           Malamai da dama sunyi rubutu akan darajojinsa, kamar babban malamin nan da ake kira allama ibn abdulbarr, acikin littafinsa al-isti'ab juzi'i na 1shafi na 97 inda yake cewa: " hujur na daya daga cikin sahabbai masu daraja" sannan ibn asir shima da yake magana akan hujur bn adi acikin littafinsa *asadul ghaba fi ma'arifatussahaba* cewa yayi hujur Ya kasance daga cikin sahabbai masu daraja. Hakama Ya ware babi guda a cikin littafinsa mustadrak, Akan darajojin hujur bn adi Ya kira babin da "darajojin hujur bn adi daya daga cikin sahabban manzon Allah (s.w.w).


          Bayan wafatin manzon Allah (s.w.w) Hujur Ya kasance tare da imam Ali (a.s) Yana daga cikin Manyan mabiya imam Ali (a.s) Ya halarci yakin siffin da Jamal tare da imam Ali, bayan wafatin imam Ali (a.s) hujur bn adi Ya ci gaba da zama a kufa tare da imam Hassan (a.s).


        Lokacin da khalifanci Ya dawo hannun mu'awiya(L) sai yasa zagin imam Ali akan mumbari Ya dawo al'ada,ya zamana duk wanda zai hau kan mumbari yayi jawabi to dolene kafin Ya sauka sai ya tsinewa imam Ali (a.s) saboda yasa mutane su tsani imam Ali (a.s) wannan a sauran garuruwa kenan, amma a sham inda yake Ya dade da sunnanta zagin imam Ali (a.s)tun imam Ali Yana raye, wanda har ta kaima da dama daga cikin mutanen sham basusan wanene imam Ali ba face kafiri saboda yadda a kullum ake aibatashi a idanunsu.

        Bama haka ba, lokacin da Abdurrahman bn muljam (L) ya sari imam Ali a masallaci sai da yawa daga mutane suka cika da mamaki, taya za'a sari imam Ali a masallaci? Me Ya hada Ali da masallaci? Dama Ali Yana sallane?  Saboda jita -jitar da mu'awiya yasa akayi ta yadawa na batanci ga imam Ali (a.s),Don Ya kasance Yana kiran mutane suna zagin imam Ali(a.s) misali : muslum Ya ruwaito a sahihh dinsa kar kashin babu fada'ilu Ali bn Abu dhalib " hadisi na 4428 daga sa'ad bn abi wakkas yace : mu'awiya ya umarceni da in zagi imam Ali sai nace masa abubuwa uku manzo Allah Ya fada game da Ali wanda har abada bazan zageshi ba..... "

        Bayan wannan an ruwaito atarikh ibn khaldum juzi'i na 3,shafi na13, karkashin dhikir hijra na 51cewa: wata rana sasa'a  bn sauham ya tuhumi gwamnan mu'awiya na kufa, mughira bn shu'uba akan cewa meyasa idan ya hau kan mumbari yake zagin imam Ali bayan kuma yasan matsayinsa? Sai mughira yace masa "kafa maida hankalinka! Don na samu labarin kana yawaita ambaton Ali da darajojinsa a bayyane, ni nasan darajojin Ali fiye da yadda kai ka sani, Amman wannan shugaban (Yana nufin mu'awiya) shi Ya tilasta musa mutane su kyamaci Ali, mukan bar abubuwa da yawa bama fada Na muzanta Ali daya umarcemu mu fada, mukan fadi abubuwan da suke da sauki ne saboda mu tseratar da ranmu daga wadannan mutane(banu umayya).

        Duk lokacin da wani ko gwamna ya hau kan mumbari, Yana zagin imam Ali (a.s) hujur bn adi baya iya hakuri, Ya kan tashi ya karyata ya kuma kawo darajojin imam Ali.

KU KARANTA WASU RUBUCE RUBUCEN MU:Idan aka tambaye ku waye farkon Musulunta? Kuce Imam Aliy ne.

   Gwamnan mu'awiya na kufa mughira bn shu'uba kamar sauran yan uwansa gwamnoni ya kasance Yana hawa mumbari Yana zagin imam Ali (a.s) Yana kuma yabawa mu'awiya.

       Mabiya imam Ali suna ji Amman kuma suna tsoron suyi magana don kar a kashe su,  Amman hujur bn adi yakan tashi ya karyata, yadda mutane suke goyon bayan hujur suce gaskiyane yasa yaki daujar wani mataki akan hujur, Amman ya kirashi yake ce masa: "ka Kama kanka daga irin wadannan maganganun na yabon Ali kada Amirulmuminin (mu'awiya L) yaji Don zai kashe ka ne.

        Hujur bai saurareshi ba yaci gaba da tunasar da mutane matsayin imam Ali saboda kar a sasu su zageshi.

        Kamar kullum wata rana mughira bn shu'uba ya hau kan mumbari Ya fara huduba sai Ya fara fadar munanan kalamai ga imam Ali Yana kuma yabawa mu'awiya, dama hujur Yana cikin masallacin, sai Ya Mike Ya fada da karfi ta yadda kowa zai iya jinsa yace: "kai wannan mutum!  yanzu bakasan wanda kake zagi ba? Kana zagin shugaban muminai kana yabon azzalumi?. Haka hujur yaci gaba da rayuwarsa har lokacin da mughira ya mutu. Bayan mtuwar mughira shekaru 50bayan hijira, sai mu'awiya ya dauki garin kufa ya hadawa gwamnan sa Na Basra ziyad bn abih, sai Ya zamana kufa da Basra duk suna karkashin sane.

        Ibn kasir ya ruwaito a bidaya wanni haya juzi'i na8 shafi na 50-55 karkashin dikhir na shekara ta 51 bayan hijira, ibn asakir ya ruwaito a tarik dinsa juzi'ina 12 shafi na 227 karkashin dhikir hujur bn adi, dabarani ma Ya ruwaito a tarik dinsa juzi'i na 4 shafi na 190,200 ibn asir ya ruwaito a tarik dinsa juzi'i na 35 shafi na 234-242 cewa: " alokacin khalifan cin mu'awiya an maida tsinuwa da zagin imam Ali ya dawo al'ada a kan mumbari a masallatai, hakan bayayin dadi a zukatan muminai, Amman mutane sukan kasa magana saboda tsoron kar a kashe su. Akufa hujur bn adi baya iya yin shiru yakan tashi ya karyata Mai zagin kuma Ya kawo darajojin imam Ali (a.s).

        A lokacin da mughira yake gwamna yayi shiru akan abinda hujur yake yi, Amman alokacin da aka bawa ziyad gwamnan kufa sai Ya tsanantawa hujur, saboda shima hujur baya barinsa duk lokacin da ya zagi imam Ali.

        " ziyad yasa aka Kama hujur da mutanensa, guda 6 da laifin suna yabon imam Ali sannan Ya nemi shaidu dasu shaida cewa "wadannan mutane (su hujur) sun hada kungiya suna fadin munanan kalamai ga Khalifa mu'awiya (L) suna umartar mutane dasu yake shi(mu'awiya ) suna cewa ba wanda zaiyi khalifan ci sai yayan Abu turabb, suna nuna goyon baya ga Abu turabb, suna nuna tausayi gareshi, kuma suna nisanta kansu da makiyanshi.

    Daga cikin shaidu Akwai kadi shudri, Wanda daga baya ya rubutawa mu'awiya wasika Yana cewa: Na samu labarin cewa daga cikin shaidun da aka tura maka kan hujur harda shaida ta to asalin shaidata kan hujur itace : Yana daga cikin mutanen da suke sallah, suke bada zakka, suke hajji da ummara saboda haka jininsa da dukiyar sa haramunne,amman in kanason kashe shine, to kana iya kashe shi, Amman in ba hakaba kana iya barinsa.

        Sai aka tura hujur bn adi da sahabbabsa wurin mu'awiya, shi kuma sai Ya yanke musu hukuncin kisa, sai aka daukesu aka kai su wani kauye mil 12daga dimaskus, Mai suna adhra bayan sojojin mu'awiya sun kawo su kauyen  sai suka ce musu : lallai shugaba mu'awiya ya umarcemu damu kashe ku saboda kune shuwagabannin fitina masu taurin  kai, Marassa imani, kuma masu nuna goyon baya ga Abu turabb, amma da sharadin in zaku bar imani da abinda kukayi imani dashi Na shi'ar Ali ku kasance masu tsinewa shugabanku,  (imam Ali ) ku daina ambaton darajojin sa to zamu kyaleku.

        Sai hujur da sahabbansa suka ce musu lallai hakuri da kisan da zakuyi mana yafi sauki a garemu, da muyi abinda kuke umartar mu dashi, kuma haduwa da Allah da manzon sa, da wasiyyin manzon sa yafi soyuwa garemu damu shiga wuta.

        Akarshe dai an kashe hujur da sahabbansa guda 6 a wannan kauyen. Daga cikinsu mu'awiya ya ware Abdurrahman bn hasan ya aika dashi gun ziyad da wasika cewa a kashe shi ta mummunan yanayi sai ziyad yasa aka bizne shi da ransa.

        Abdurrahman bn hasan Yana daga cikin wadanda ziyad ya aika dasu wurin mu'awiya da nufin wai su tuba, lokacin da yaje gun mu'awiya sai mu'awiya yace masa " dan uwan Rabi'a me zakace dangane da Ali? sai abdurrahman yace masa :" Na shaida cewa shi Yana daga cikin masu tsoron Allah sosai, Yana umartar mutane da bin gaskiya, yanayin adalci, kuma Yana yafewa mutanen da suka zalunceshi, sai mu'awiya yace to kuwa ka kashe kanka tunda ka yabi Ali a gabana, sai abdurrahman yace masa ko kuma Na kashe ka ba. Sai mu'awiya ya aika dashi gun ziyad da sakon  cewa yayi masa mummunan kisa, da ziyad ya karbi sakon mu'awiya sai yasa aka haka rami Mai zurfi sannan yasa aka dauki abdurrahman aka daddaureshi aka jefashi cikin ramin  aka maida kasa aka bizne (wa'iyazubillah) kuma wai musulmaine suke haka masu tambarin (R.A).

          Daga cikin sahabban hujur bn adi da mu'awiya yasa aka kashe, saboda soyayyar su ga imam Ali sun hada da:shuraikh bn shaddad, saif fasi al-shaibaniyy, abdurrahman bn hasan al-anzi, kubaisa bn Rabi'a al-abasi, kaddum bn hayyan al-anzi, da muhriz bn shabab al-tamimi.

        An ruwaito a al-isab juzi'i na 1 shafi na 313 kar kashin dhikir hujur bn adi cewa: bayan yakin kudsiya hujur bn adi Ya halarci yakin Jamal da siffin tare da imam Ali kuma Yana daga cikin mabiyansa, an kashe shine bisa umarnin mu'awiya a wani kauye da ake cema  adhra kusa da dimaskus.

        Alokacin da za'a kashe shi Ya roki masu kisan cewa : bayan kun kashe ni, kada ku ciremin sarkar da kuka daureni da ita,kada ku wanke min jinin da zai zuba ajikina ina son in hadu da mu'awiya ranar lahira Allah yayi mana Shari'a dashi. Kashe hujur da sahabbansa da mu'awiya yasa aka, yasa mutane dana kusa dashi sun rabu dashi sun kumayi Allah wadai da abinda ya aikata.

Ni sakina Ahmad daga hannun hagu sai khadijat da Asiya da bakaken hijab a wajen Taron karawa juna sani da wakilan Ma'asuma sukayi a garin katsina 

        Dabarani ya ruwaito a tarik dinsa juzi'i na 4 shafi na 190-207, ibn asir ya ruwaito juzi'i na 3 shafi na 234 cewa kashe hujur da mu'awiya yasa aka yi ya girgiza zukatan al'umma abdulahi bn umar da ummulmuminini Aisha (ra)sunyi bakin ciki sosai lokacin da sukaji labarin.Aisha ta rubuta wasika tana sukan mu'awiya akan kashe hujur,  bayan ta hadu da shi kuma sai tace masa : mu'awiya baka tsoron Allah ko kadan da zaka kashe hujur?

     Lokacin da gwamnan mu'awiya a kurasan, Rabi'a bn ziyad yaji labarin an kashe hujur, sai yayi ku ruruwa da karfi yace: ya Allah indai har akwai wani alheri daka tanadarmin to ka dauki rayuwata, baibar gun ba face Allah Ya dauki ransa.


        An ruwaito a kanzul Umma juzi'i na135,556, hadisi na 37511 ibn asakir juzi'i na 12shafi 227 karkashin dhikir bn adi al'aswad da sa'id bn hilal cewa :mu'awiya yaje hajji sai yaje wurin uwar muminai Aisha (R) sai tace masa me yasa ka kashe mutanen adhra hujur da sahabbansa sai mu'awiya yace mata :Ya uwar muminai gani nayi mutuwarsu shi yafi amfani ga al'umma, rayuwarsu kuma cutarwa ce ga al'umma sai tace masa : na rantse da girman Allah naji manzon Allah Yana cewa: za'a kashe wasu mutane a adhra, Kuma Allah da mala'iku da suke sama zasuyi fishi da hakan.

        Ibn kasir ya ruwaito a bidaya wannihaya juzi'i na 8 shafi na 55kar kashin dhikir na shekarata 51 bayan hijira daga marwan yace: Ya mu'awiya ka kashe hujur da sahabbansa kayi abinda kaga dama, yanzu baka tsoron shigowar da kayi wurina zan iya boye wani kana zuwa Ya kashe ka?


        Hujur bn adi dai an kashe shine bissa zalunci, saboda soyayyarsa ga imam Ali yanzu haka kabarinsa Ya Na siriya kuma al'umma Na ziyartar sa,  ajikin kabarin an rubuta *HAZA  KABARU  SAYYADUNA HUJUR BN ADI (RA) ,KATALU SAYYIDINA MU'AWIYA (RA) LI ANNAHU YU HIBBU  SAYYIDINA ALI (RA)* wato wannan kabarin hujur bn adi ne (ra) wanda shuganmu mu'awiya ya kashe (ra)saboda yanason shugabanmu Ali (as).


Dawanda Ya kashe, da wanda aka kashe, da wanda aka kashe dominsa duk suna amsa  (R.A) ne *ANYA KU TAYANI GANI*


 *Tare da  Sakina Ahmad Kazaure
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post