JIYA BA YAU BA.

Sheik Nasiru Kabara Rahimuhulla

Takaitaccen Tarihin Sheik Nasiru Kabara
An haifi Sheikh Muhammad Nasiru Kabara a shekarar 1912, a wani kauye da ake kira Guringuwa. Ya girma a tsakanin unguwannin Kabara da Alfindiki.
Ya fara neman ilimi tun yana da kananan shekaru. Daga cikin malamnsa akwai, Alkali Ibrahim na Yakasai, Na'ibin Kano a unguwar Daneji, Alkalin Bichi, Mallam Mustapha dake unguwar Kurawa. Sai wani malami dake zaune a Chiromawa.
Ya taba zama shugaban Makarantar Judicial ta Shahuchi. Daga baya ya kafa tasa makarantar a unguwar Gwale.
Ya rayu rayuwa mai dadi. Kullum cikin bada ilimi da karba gyyara.
Bincike ya nuna cewa wasu daga cikin manyan Malaman da marigayi Sheik Nasiru Kabara ya karantar sun hada da Sheik Abubakar Gumi, Sheik Dahiru Usman Bauchi, Sheik Mudi Salga da sauransu da dama.
Shine kuma mahaifin manyan Malamai irin su Sheik Karibullahi (Jagoran Darikar Kadiriyya na Aftika), Sheik Abduljabbar da sauransu.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post