GAGARUMAR MUZAHARAR MAULUDIN SAYYIDA ZAHARA (s.a) ARANA TA UKU DAGA GARIN ABUJA







Ⓜ__Ayau Talata  5/3/2019 yan uwa Musulmi Almajiran Sayyid zakzaky (h) Sunyi tururuwa a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja Domin gabatar da Mauludin Sayyida Zahara (a.s),
Mauludin dai Anfara shine tun Ranar Lahadin da tagabata,

Aranar Lahadin Angabatar da wasannin Yara da Rana A wurin wasan  yara na [Wonderland dake Abuja],
Sannan Akayi Majalisin mawaka da daddare a marabar Gurku dake Abuja,
Aranar Litinin kuma anyi taro  A Wuse Zone 5 inda aka gabatar da Jawabai da tamsiliyya Sannan aka dauko muzahara daga [Sky memorial] Sannan aka rufeta a gadar bega [berger bridge],

Ayau Talata Kuma aka Gabatar da Gagarumar  Muzaharar mauludin,
Anfaro Muzaharar ne daga Titin Human right Akabiyo ta filin yanci [Unity Fountain ] Sannan aka iso Federal Secteriat inda aka rufeta anan,

__Muzaharar  tayau tana daga cikin Muzaharorin da suka fi sauran Muzaharorin da aka saba Gabatarwa agarin na Abuja ta fuskacin yawan Mahalarta,

Anyi Muzaharar Lafiya Antashi Lafiya,

______________________
Ma"asuma Nigerian News Updates
Wakilinmu;
    👇🏼
Mahadi Tukur Almizan

















Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post