FIFIKON NANA FATIMA (AS) A KAN SAURAN MATA
Ya ishe ka misali wata ruwaya da aka ce Manzon Allah ya yi mata magana a kunne, sai aka ga ta yi kuka, wannan ruwayar A’isha ce. Suna zaune tare da matansa, sai ya ce marhaban da ’yata, ya buda mata wuri ta zauna kusa da shi, sauran matan na gani. Sai ya yi mata magana a kunne, sai aka ga ta yi kuka, sai ya yi mata magana a kunne sai aka ga ta shiga dariya. Sai daga baya A’isha ta tambayi Fatima, “Menene ya gaya miki na ga kin yi kuka? Menene ya gaya miki na ga kin yi dariya?” Sai ta ce, “ba zan gaya miki ba saboda asirinsa ne.” Sai bayan da ya rasu, sai ta ce, “amma yanzu ina iya gaya miki. Lokacin da ya gaya min magana na yi kukan nan, ya ce min ya kusa rasuwa ne, domin Mala’ika Jibril yakan bijiro masa da Alkur’ani a kowane Ramadan sau daya, amma wannan shekara sai ya bijiro masa sau biyu, saboda haka yana jin wannan na karshe ne ba zai kai badi ba,” saboda haka sai ta yi kuka. “Amma kuma sai ya sake yi min magana a kunne, sai ya ce min ke za ki fara cimmani a Aljanna cikin iyalan gidana,” sai ta yi murmushi. Ba tana murmushin za ta mutu bane ba fa, za ta je wajen wa? Za ta wajen Manzo. Ko wannan ma yana iya nuna maka fifikonta a kan A’isha. Tunda da ba ta fi ta ba, da ba ta kasance ita za a ke6e da wani abin da ba a gaya mata ba, har ma ya zama ita kawai ta sani, sai ma daga baya ne take gaya mata. Amma muna da hadisai birjik daga A’isha, har ma an ce rabin addini, amma ba mu da ko kashi daya na addininmu daga Fatima. Duk da kuma A’isha an daura aurenta ne gab da hijira, kuma ta tare ne bayan hijira. Ita kuwa Fatima an haife ta a gidan wahayi ne ta girma.
Ina fadin wannan, amma ba ina nufin wasu mutane ba su hadisi bane. ba mu ce haka ba. Abin da muke cewa shi ne in mutane na hadisi me ya sa mutanen gidan Annabi ba za su yi ba? In matar Annabi za ta ba da hadisi, me ya sa 'yar Annabi ba ta da hadisi? Ban ce muku matar Annabi ba ta hadisi ba. Ba haka na ce ba. Abin da nake cewa shi ne me zai sa a sami hadisi daga matar Annabi ba a samu daga ’yarsa ba? In an samu daga matarsa kila ma a fi samu daga wajen ’ya, musamman ma ita da aka haife ta, ta girma a gidan.
Wadannan isharori ne da suke nuna mana cewa lallai akwai wadansu abubuwa da dama da aka 6oye, wadanda alhamdulillahi da yardar Allah, da ganin damansa 6oyewa aka yi. Masu 6oyewa sun yi iya Kokarinsu su ga cewa sun kawar ne, amma Allah bai ga daman ya kawu ba, saboda haka yana nan. Ka san in aka 6oye abu wata ran ana iya gani ko? Su sun hana mu ji ne, sun sa shamaki ne, amma yana nan a inda yake. Ka san idan aka ce maka ai ba kowa a nan ba shi kenan? Ran da mai rufewar ya tafi, al’amarin zai bayyana. To me rufewar ya tafi, saboda haka yanzu bayyanar abin yake yiwuwa, amma akwai shi dama. Da ace an debe shi an mutsuttsuke an binne shi a rami ne, ba mu iya tonowa ba, sai mu ce babu, a’a an hana mu ji ne, aka ce ga addini, wanda muka gaya muku shi ne addini, kada ku saurari wani kuma, saboda mene? Saboda in an saurari wadancan za a ji wadansu abubuwa da ba a son ji, wanda zai nuna ashe wadancan mutanen ba su cancanci su rike mukamin da suka rika ba, saboda haka kuma za a iya kawo fitina. Saboda haka maganin abin kar a ji. To amma, alhamdulillahi yanzu Allah ya ga daman a ji.
Kamin kaci gaba da Karatu KASANCE DAMU A FACEBOOK: - Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update
Kuma kamar yadda nake cewa zan sake cewa ya kamata wannan magana ta zaburantar da mu ga ainihin bincike. Kowanne ya dauka wa kansa zai bi wadannan asar din ya ji bayani, ba kawai ya dauka sai an fadi magana ba ya ce shi bai ta6a ji ba saboda haka ba haka bane. Ya bincika tukuna, alabashi in ya ce ba haka bane, ya ce ba haka bane da ilimi, ba kawai don bai ta6a ji ba. Kuma da wadannan bayanai ina so in takaita mana. Da fatan Allah ya sa wannan ya zama kamar matashiya wadda za ta zama sanadiyyar bayyanar da gaskiyar abin da su Sayyidatuna Fatima suka kasance a ciki, wanda zai zama shiriya gare mu da kuma daukacin al’umma baki daya.Kamar yadda nake cewa kafin ka so mutum dole ka san wani abu daga gare shi, ba zan iya gaya mana abin da shi ne kason Fatima ba, amma na sa a karatu akwai shi, saboda haka in mutum yana da bukata ya bincika ya ji abin da zai sa shi ya so ta, wanda zai farin ciki da abin da zai sa ya so ta, wanda zai sosa mata rai da wanda zai iya sa shi ya yi kuka, wanda yake kuka a sanadiyyar son ta da tausaya mata mumini kawai yake yi, Wanda yake har ya ga abu ya ji ya tausaya mata ya yi kuka, to albishirinsa shi mumini ne. In har kaji abin da ya same ta ka yi kuka, albishirinka, kai mumini ne, don yana daga cikin alamomin imani. Wannan kuma ba nan ne muhallinsa ba, akwai shi a muhallinsa. Fatanmu shi ne Allah ya ganar da mu gaskiya ya kuma ba mu ikon binta, ya kuma ganar damu qarya, ya bamu ikon wurgi da ita, yasa mufi qarfin zuqatanmu, yasa ya zama ba son ranmu muke bi ba, muna qoqarin mu gano saqon da Allah ya aiko manzonsa da shi tsintsa don mu bi,kuma ya bamu ikon bi din, don fakam da yawa sai mutum ya gano gaskiya din sai Allah (T) yayi masa baiwa na ya bi, don zai iya gani yace haka din ne amma kuma an qi a bi, akwai masu yin wannan. Allah ya sawwaqe.
Allah ya ganar damu gaskiya ya sa mubi, yasa mu fi qarfin son ranmu.
Assalamu alaikum Warahmatullahi ta'ala wa barakatuhu.
Wannan wani yanki ne daga cikin jawabin da Malam Ibrahim Yakub Alzakzaky ya yi a lokacin rufe Makon Zahra da ’yan uwa mata suka shirya a zauren taro na otal din kongo dake Zaria a shekara ta 1417. Shine kuma jawabinsa na karshe kan wannan Makon Zahra kafin waki’ar da ta auku janar tazarce ya tsareshi. Don haka an shekara biyu ba ayi irin wannan jawabin ba, saboda yana tsare a lokacin.
Tags:
Filin Sayyadah Ma'asumah