FATIMA CE ALKAUSAR

FATIMA CE ALKAUSAR 


Ita ce Kausar.
  Kuma ko da hankali kamar yadda nake fadi bara zai yarda da wannan. Masu tafsiri da dama sun ce kausar din nan qorama ce a Aljanna, kuma sun ce har wala yau Kausar din nan na nufin alheri mai yawa, har wala yau kuma Kausar din nan na nufin Sayyidatuna Fadima. Babu korewa ga wannan. Bai kore kasantuwar akwai qorama sunanta Kausar ba, tunda yake Kausar kalma ce da ta samo suna daga kasir, kasara, ma’ana da yawa ko ya yawaita. Kausar shi ne abu mai yawa, wanda yake kasir, saboda haka ma aka kira Kausar ‘khairun kasir’. Alheri mai yawa shi ne Kausar. In abu mai kyau ya yawaita sunansa Kausar. Tunda koramar Manzo alheri ne mai yawa, ga shi fari mai zaqi, ga shi kuma wanda ya sha shi ya tsira, a ranar alkiyama ran da ake faman shan wahala, su mabiya Manzo suna shan Alkausar. Duk ba wanda yake musun cewa Alkausar qorama  ce ta Manzo, wacce mutanen Annabi za su sha daga gare ta a yayin da wasu mutane ke shan azaba kafin a gama hisabi. Da kuma cewa qorama ce a Aljanna. Wannan bai kore kasantuwar cewa Kausar Sayyida Fatima ce ba don ayar ta yi munasaba da wannan. Wani ya yi maka gori ba ka da da. sai Allah Ta’ala ya wadace ka ya ce maka ya ba ka Kausar, wanda ke maka gori ma shi ne ba shi da, ka ga ko ba a gaya maka ba, Kausar na nufin me? Yana nufin da. Ko ba haka bane? Saboda ba zai yiwu a yi maka gorin wani abu, a lallashe ka da wani abu komabayansa ba.
     Tunda an yi wa Annabi gorin ba shi da da, in ya zamana aka ce masa ai kana da korama a Aljanna za ka je ka sha, kar ka damu, zai zama yana da wuyan gaske (ya dace). Na’am Alhamdulillah za a samu korama, amma dai ba dadi a rasa da, ko ba haka bane? Ya kamata ya zama in aka yi maka gorin da a ba ka da. Ballantana ma sai Allah Ta’ala ya ce “Makiyinka ne ma abtar.” Shi ne ma yankakke, shi ne ma bai da da. Sannan kuma a lokacin Abu'Jahl yana da da.

Kamin kaci gaba da Karatu KASANCE DAMU A FACEBOOK: - Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update

Sai ga shi daga Cikin alheri kasir din nan akwai zuriyar ita Kausar. Ayanzu zancen nan da muke yi akwai mutane da daman gaske wadanda ake ce ma Sayyid-Sayyid, Sharif-Sharif, wadanda Suke takamar su jinin Manzon Allah ne. Akwai miliyoyi.
  Amma wane mutum ne a yanzu haka yake tinkaho ga shi shi jinin Abu Lahabi ko Abu Jahl ne? In da shi ya daga hannu. Na san akwai jinainen Abu Jahl a aiki, suna nan in an ambaci sunan Annabi suna bakin ciki, a aiki sun gaje shi, wannan ko a jini ake magana. Kuma sai ya nuna mana tabbas haka nan ne, ita an samu zuriya ta hanyarta masu yawan gaske, wadda ta hanyarta aka gaji Annabi. Sai ya zama lalle kam gorin da aka yi masa-bai da da bai ce komai ba, saboda ga shi Allah ya ga dama ta hanyarta ne Manzo zai zama yana da zuriya. Kuma sai ya zamana ’ya’yanta ma halittar da aka yi masu sa6anin wadda ake wa sauran mutane ne, domin nasabar tsatson mutane yana bin ta wajen uba ne, amma banda ’ya’yan Fatima, su ’ya’yan Fatima duk tsatson Manzon Allah ne. Don haka ne ma wadanda suka shaida sun sani cewa Hasan da Husain (AS) sun yi kama da Manzon Allah'(S). Har ila yau kasantuwar ta zo bayan Isra’i ya tabbatar da wasu . labarurruka da kuma aka ruwaito cewa an nuna masa haihuwar ita Fatimatuz Zahra a yayin da ya yi Isra’i da Mi’iraji. Wata ruwayar na cewa an ba shi Tuffaha ya ci, wanda shi ne ya zama maniyyin da ya zama ita. Akwai wani lokaci da na karanta wani yake cewa wannan ba daidai bane, saboda ai haife ta ne kafin Isra’i ne, an haife ta ma kafin a aiko Manzon Allah, amma wanda ya fi qarfi an haife ta bayan ma Isra’i da shekaru uku ne, bayan aiko shi ma da shekara biyar. Wannan shi ya fi karfi. Ta shekara takwas tare da Manzo a Makka, sannan ta yi hijira ta shekara goma tare da shi a Madina, sannan ya rasu ta kwana saba’in da biyar bayan rasuwarsa. Saboda haka rayuwarta duka-duka shekara 18 ne. A cikin wannan gajeren lokaci ne Allah ya yi mata daukaka mai yawan gaske. Wannan shi ya nuna daukaka in hadisi ne daga mutum sai ka rasa yadda zaka yi ka ce yaya wannan al'amari yake? Daukaka baiwa ce daga Allah (T). ba wani abu ne da mutum ke haqarwa ta nasa Bangaren ba, shi ne kuma Allah (T) ya yi wa Sayyidatun Fatima (AS).

-sheikh Ibrahim Alzakzaky (H)  a jawabin sa da ya gabatar a lokacin rufe Makon Zahra da ’yan uwa mata suka shirya a zauren taro na otal din kongo dake Zaria a shekara ta 1417. Shine kuma jawabinsa na karshe kan wannan Makon Zahra kafin waki’ar da ta auku janar tazarce ya tsareshi. Don haka an shekara biyu ba ayi irin wannan jawabin ba, saboda yana tsare a lokacin.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post