DON EL-RUFA'I YA MAIMAITA SHEKARU HUƊU, SAI ME?
✏️
Ishaq sagir magaji
Mutane sun bi duk sun takurawa kansu akan zaɓen Gwamna na Jihar kaduna tsakananin masu son koda tsiya sai Nasiru ya zarce wato: 'Yan ƙungiyar Izala, yan Shi'ar Gwamnati, Jakadan Amurka a Najeriya da dai sauran su.
Da masu burin ganin Nasiru bai sake zama Gwamna ba, 'Yan uwa mabiya Sayyid Zakzaky da wasu 'Yan Ɗariƙun Sufaye.
Ban san meke damun ku ba har Nasiru ya zama wata tsiya da za'a damu ya dawo ko kar ya dawo.
Gareku Masu burin ya dawo yaci gaba da maganin mu kamar yadda kuke furtawa to, sai me don yazo ya ci gaba ka shemu? Kuke tsoron akasheku akan abinda kukeyi.
Nasan gaba ɗayan ku baku manta da Mu'awuya ba wanda ya shafe shekaru 23 yana kashe 'yan shi'a, harda Sahabbai bai bari ba.
Ina da yaƙinin bazaku manta da Hajjaj bin Yusuf ba wanda ya maida ran 'Yan shi'a kamar na kiyashi.
Nasan dukkan ku kunyi zamani da Saddam wanda jinin yan shi'a baida ƙima a wurin shi.
Samada shekaru kusan 20 yayi yana kisan 'Yan shi'a.
Shine wanda yasa jirgin sama yana farautar duk masu Tattakin 40 yana kashe su kamar ba gobe, amma yanzu babu mai musun Tattakin 40 na Imamu Husaini da akeyi a Iraq shine taro mafi tara mutane a duniya.
Wai don Nasiru ya zarce a mulki sai me?
Nasan dukkan ku da kuka haɗa ƙarfi da ƙarfe kuke taimaka masa ko ta halin ƙaƙa don kawai yaci gaba da zubar da jinin mu kun san cewa duk irin kisan kiyashin Nasiru ga Shi'a bazai kai Sarki Shah ba, dukkan ku kun rayu zamani ɗaya dashi kuma nasan bazaku manta waƙi'ar black Friday ba wadda ta faru 1963 ana hasashen aranar an kashe 'Yan shi'a sama da dubu hamsin yau ina Sarki Shah da sarautar sa? Babu mai musun ayanzu ƙasar sa itace Cibiyar shi'a ta duniya, jama'a ina sarki Shah?
Mu ƙaddara Nasiru ya zarce yaci gaba da kisan mu, da rusa gidajen mu da wuraren ibadan mu tare da makarantun mu, toh sai me?
Shikenan sai yakawo ƙarshen Tafarkin gidan Annabin rahma a duniya?
Wai kuna zaton bamu san da zuwan wannan ranar bane?
Kun ɗauka akwai wani mabiyin Sayyid Zakzaky da bai san akwai ranar da zaku kashe mu ku rusa gineginen mu ku hana mu aikata addini yadda muka fahimta ba?
Wai don Nasiru ya zarce sai me? Shikenan sai dukkan burace buracen ku su biya?
Da kuna da hankali da tunani yakamata kusan cewa waƙi'ar zariya fantsama lamarin Sayyid Zakzaky tayi.
Idan zamuyi babban taro wani ƙauye me Titi ɗaya muke zuwa mai cike da Kukoki da Rimaye, ga yawan 'Yan baƙin ciki
Amma yanzu fa?
Fadar Gwamnatin tarayya muke yiwa tsinke, Abuja ta zamar mana kamar gida ƙana nan yaran mu zasu iya zana maka cikin garin garin Abuja.
Inama 'Yan uwa da suka damu da fallasa makircin da Nasiru da yake ƙullawa 'Yan Ɗariƙa da rikicin addini dayakeso ya haifar zasu daina?
Su fita harkar shi ya daɗe bai zarce ba, kurabu da Malaman Fada suyi ta masa kamfen, inaso idan ya zarce ya aiwatar da duk mugun nufi da mummunan ƙullin dake zuciyar shi, karya raga mana karya tausaya mana.
Inaso kusani kuma ku shaida, in zama farkon wanda zaku bada fatawa akashe, kai kuma Nasiru idan ka fasa kashe ni ka raina Uche Udoma Kuku.
Kasani azabar ka batayi Jahannama ba, don haka mun shirya shiga, nasan dai iyakar mulkinka shekaru 8 gaba ɗaya don ka shekara 8 sai me?
#AllahaSaveZakzay
©Shehu Al-ja'afaree Kaduna
Tags:
Labaran Duniya