GAGARIMIN MAULIDIN SAYYIDA ZAHRA(AS) NA HARISAWAN AZZAHRA(AS) A KATSINA
A rana ta biyu cikin bukukuwan Maulidin Sayyida Zahra(as) wanda gangamin Harisawan Azzahra(as) karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) suke gabatarwa a birnin Katsina, yanzu haka ana cigaba da gasar wasannin maza da mata a tsakanin Harisawan da suke amsa sunan Azzahra(as) na sashen Harisawa wanda suka hada yankunan Katsina, Daura, Malumfashi, Kankia, Maraɗi da Funtua. A jiya an fafata a bangaren gasar Kaci-kaci kan fik'hu, tarihi da duniyar musulunci a yanzu da sauran fannikan ilmi.
Wassanin yau sun haɗa da gudun kwai, gudun yada-kane wani, gudun mita ɗari, wasan dauki saka na lemu da na wasan ɗibar ruwa a kwalba da sauransu.
Yanzu haka ana tsakiyar filin wasannin birnin katsina ana baje kolin bajintar wasanni kala kala masu ban sha'awa. A gefe guda kuma ga yan uwa nan maza da mata anata kwalla kabbarori da salatin Annabi(SAWA) domin murnar wasannin dake gudana masu ɗaukar hankali da birgewa.
NAN KUMA WASU DAGA HUTUNAN GASAR KARATU NE.
@Mlmusa
16/03/2019

Wasu daga hutunan wasanin yau kenan |