A FARA GYARA WANNAN A NIGERIA, SAI A NEMI CANJI.

A FARA GYARA WANNAN A NIGERIA, SAI A NEMI CANJI.

✏️MSN0012


Nigeria Qasace Ta Musulmi, Kirista Da Wanda Bashida Addini Koma Beyi Imani Da Allah Ba, Qasace Da Take Tafiya Akan Tsarin Democracy Qarqashin Dokoki Da Tsari Na Constitution Ba Wai Izala, Dariqa, Kirista Ko Shi'a Ba, Yakamata 'Yan Qasa Da Gwamnatoci Su San Wannan Ba Tsarin Musulunci Ko Kiristanci Akeyiba Dukda A Haqiqa Tsarin Ya Saba Dana Musulunci A Mafi Yawanshi Koma Yaci Karo Dashi, Kuma Duk Abunda Yasaba Da Musulunci Balle Ace Yaci Karo Koda Da Hukunci Ko Doka Daya Ta Musulunci To Ya Fita Daga Musulunci In Kaso Kace Kafirceni Ko Kuma Kabashi Sunan Da Kakeso.

Idan Anaso Ayima Qasa Aiki, Kuma 'Yan Qasa Su Zama Masu Kishin Qasarsu Da Samar Da Cigaba To Matakin Farko Ya Wajaba Cewa; Duk Wanda A Lokacin Takara, Siyasa Ko Zabe Ya Nuna Aqida Ko Fahimtarshi Ko Ya Fito Da Gemu Ko Wata Alama Domin Nuna Addini Alhali Ba Addini Akeyi A Nigeria Ba To Dole A Haramtamashi Takara Balle Zama Shugaba Koda Kansila Kuwa Domin Ba Abunda Zaiyi Sai Fada Da Wani Bangare Da Danne Haqqinsu Da Sunan Addini Alhali Ba Domin Haka Aka Zabeshiba Kuma Ba A Haka Aka Kafa Nigeria Ba Kuma A Akan Wata Aqida Ko Addini Ake Tafiya Ko Hukunciba.

Dolene Dan Siyasa Ko Wanda Zaiyi Takara Ya Aje Addini, Aqida Ko Fahimta Gefe Yayi Mu'amala Da Kowa A Matsayin Dan Qasa Kawai, Kodama Menene Addini, Aqida Ko Fahimtarshi, In Zaiyi Bauta Ko Wata Alaqa Yayi Can Gefe Ba Wai A Zahiri Da Sunan Gwamnati Ba.

Idan Akayi Haka, To A Lokacin Ne Adalci Zai Tsayu, Kishin Qasa Zai Shiga Zukata Sannan A Bunqasata Da Ciyar Da Ita Gaba, Bawai A Riqa Kyawun Dan Siyasa Da Yawan Masallatai Ko Coci Ko Tallafin Limamai Da Malaman Coci Da Yake Bayarwa Ba Domin Wannan Ya Saba Da Tsarin Da Nigerian Ta Kafu, Tayi Imani Kuma Take Tafiya Akanshi, Balle Ace Sai Nagartar Dan Takara Shine Yawan Kashewa Ko Takurawarshi Da Wasu 'Yan Qasa Saboda
 Saba Dashi A Fahimta Ko Domin Biyama Wata Qasar Larabawa Ko Turawa Da 'Yan Kanzaginsu Na Nigeria Buqata.

Inba Nigeria Wai Dan Film Shima Abun Koyine Da Zaice A Zabi Wane A Zabeshi, Malamai Suma Sun Zama 'Yan Kasuwa A Basu Kudi A Kashemasu Maqiyansu, Kawai Kowane Shugaba Yayi Kanfen Da Ayyukan Da Yayima Qasa, Da Cigaban Da Yakawo Ba Wai Shirme Da Shiriritar Mawaqa, 'Yan Film Da Malamai Wadanda Basu San Komaiba Sai Ci-da-gumin-wasu Ko Ci-da-addini Ba Wai Ayyuka Ko Kishin Qasa Da 'Yan Qasa Ya Damesuba, Indai Su Butarsu Zata Biya.

A Qasashen Da Sukaci Gaba Dukda Yawan Addinai Da Qabilu Da Sukedasu, Akan Haka Suke Tafiya Hatta A Makwabciyarmu Niger.

Muhammad Maharazu.
March:05-2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post