Sheikh Sani Rijiyar Lemo yace bai kamata malamai su shiga siyasa ba





Daya daga cikin malaman Ahalussuna a Najeriya Sheikh Sani Rijiyar Lemo ya yi tsokaci game da shigar malaman addini cikin siyasa tsundum inda yace sam hakan bai dace ba a nashi ra'ayin da kuma fahimtar sa a addinance.
Shehin malamin ya bayar da wannan fatawar a lokacin da yake gudanar da karatu ga dumbin mabiyan sa a masallacin sa dake jihar Kano.

malamin yace bai kamata ace malamai sun shiga harkokin siyasa ba har ta kai ga suna kama suna wajen fadawa mabiyan su wanda ya kamata su zaba a ranar zabe.
Sheikh Rijiyar Lemo ya kara da cewa siyasar nan duka domin neman duniya ake yin ta domin kuwa babu wanda zaka zaba don ya jagorance ka a addinance sai don samun maslahar harkokin duniya kamar tsaro, abinci da kuma ingantattar rayuwa.

Ya cigaba da cewa shi malamin addini kamata yayi kawai ya fadakar da mutane akan siffofin wanda ya kamata su zaba sai ya kyale su suje su zabi wanda ya kwanta masu a rai.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post