— GWAMNATIN KASAR NAN KAMAR GININ TOKA NE!
"Wasu mutane sun dauka hankoronmu Hukuma ne, sai nace Sam mu Hukuma bata dame mu ba. Ita Gwamnatin Nigeria kamar yadda nake fadi, kamar ka kwaba toka ne ka yi gini da shi. In Ana so a rusa ginin, yaya? Ana tabansa zai murmushe. To Gwamnatin Nigeria kamar ginin toka ne, bar ganinta hawa - hawa, kafar hagu za Ka saka, ba wani karfi ka Dan tunkuda kawai gidi-gidi-gidi (za ta ruguje).
"To Amma mutane ne basu shirya ba. Saboda haka mu mutane ne suka dame mu ba Hukuma ba. Hukuma fankar fayau ce. Amma su mutane ne zukatansu bai shiryu ba. Saboda haka 'target' dinmu mutane ne ba Hukuma ba. Idan al'umma suka shiryu to komai ya yi daidai."
— Sheikh Ibraheem #Zakzaky a jawabin Tunawa da ranar Wafatin Imam Khumaini (QS) da ya gudana a Husainiyyah Bakiyatullah a shekarar 2011.
Tags:
Jawaban Shek Zakzaky