Nura Shahidi da Aword din daya samu
.Hirar da Shafin Ma'asumiyya tayi da fitaccen Mawakin nan Wato
Nura Shaheedi Wanda akafi sani da (GARKUWAN 'YAN CAJI)
.
Ma'asumiyya: Masu sauraron zasu so jin dawa muke tare a wannan lokaci tare da dan takaitaccen tarihin,vakon namu?
.
Nura Shaheedi: "Bismillahi rahmani raheem wasallahu ala nabiyinal kareem wa alihi addaiyibina dahireen a takaice suna na Nuruddeen Faruk amma suna da ake mini lakabina shine nura Shahidi ni an haifeni a cikin garin Kano a Kofar Nasarawa, Kuma na fara karatun Islamiyya a makarantar babballe ila dake unguwar gyadi gyadi dake tarauni L. G. A na kuma yi karatun allo a unguwar gwange da bulum kuttu a birnin maiduguri ta jihar Borno naci gaba da abin da ya sawwaka bayan na dawo da nayi diploma sai naci gaba da neman na kaura."
.
Ma'asumiyya: Nura Shaheedi ko nace Garkuwan 'yan caji yana daga cikin manya daga cikin mawaqn wannan harka shin yaushene ka fara waqa kuma da wacce ka fara?
.
Nura Shaheedi: "To na fara waka kusan shekara kamar ashirin da biyar tun bayan waki'ar katsina ta biyu lokakacin gwamnatin baban gida na Fara ne da wakar salamu Alaika rasulullah amma a wancan lokacin cewa nake kayarda na ganka rasulullah sai kuma wata waka da nake cewa zakzaky yace mui himma mu Kare martabar manzon Allah."
.
Ma'asumiyya: Ko wanne mawaqi yana da nasa salon, sai gashi naka kusan salone na caza zukatan masu sauraro, ko me yaje hankalinka ga wannan salo?
.
Nura Shaheedi: "To da yake ni dama ni na fahimci harka ne sanadiyyar waki'a kuma ban jima da fahimtar harka ba na fara waka kuma kusan mafi yawan lokaci nafi iya slogan Wanda shi dama a kwalta ake yi Ko fagen kwami sai daga baya ne nake hawa minbari to ina tsammani shi yasa kake jin wakokina a haka kusan kaga har yanzu ban iya wakar marsiyya ba( juyayi)"
.
Ma'asumiyya: Kusan ko wanne mawaqi da irin kalubalen da yake fiskanta na rayuwa akan harkar waqa ko tanaka bangaren an fiskanci wannan kalubalen?
.
Nura Shaheedi: "Kwarai da gaske ana ma fuskanta ne ba an fuskanta bane, na farko dai Koba komai mutum a kashin kansa yana da kule na rayuwa da iyałi, to kuma gana gwagwarmaya, ga na alumar da muke rayuwa a ciki ga kuma musamman fagen da ake kallonmu a ciki wato harkar wake kuma anyi mana nisa sosai to a gaskiya saidai mutum yayi iya abinda zai iya ya barwa Allah sauran amma kulen dake gabanmu ba zai kirgu ba."
.
.
Nura Shaheedi: "Suna da yawa shukuran la fakharan daga cikin abin farin ciki da bazan manta ba shine sunbantar( kissing) hannun Allama jikan Ma'aiki sayyiid Ibrahim zakzaky (H) a yayin da nake karbar kyautar award na shuhada da kuma kasancewa nine na fara Karbar irinsa Alhamdlillah, sai kuma shafa goshina da Sayyid (H) Yayi lokacin da nake wakar barawon akuya."
.
Ma'asumiyya: A shekarun baya zamu iya cewa mawaqan harka basu da yawa amma saqonsu yana isa fiye da tunani, kusanma al'umma da dama sun fahimci harkarnan ta waqa ne, To sai gashi yanzu adadin mawaqanmu bazai kirguba idan za a kwatanta dana baya shin ya kake ganin yanayin, kuma me ya kamata ace mawaqanmu na yanzu sun doru akai don isar da saqon kamar yanda yake a baya?
.
Nura Shaheedi: "To shi zamani baya jira binsa ake a shekarun baya hanyoyin isar da salon mawaka sune Kaset na tape aka zo CD. Plate kusan kowa yana dogara Da wadancan hanyoyi ne don jin wakokin kuma mawakan sun fahimce su da kyau amma hanyoyin da sako ke isa ga Al umma na yanzu ba kowa ya lakancesu ya kuma gane yadda zasu rike shi akan aikin nasa da kyau ba shi yasa a baya nace anyi mana nisa sai munyi da gaske.
.
Ma'asumiyya: To yanzu a naka tunanin wanne salo ya kamata ace mawaqanmu sunyi amfani da shi don ganin saqon ya isa kamar yanda ya kamata?
.
Nura Shaheedi: "Subi salo irin na zamani shine mafita."
.
Ma'asumiyya: An shiga wani yanayi sakamakon wannan waqi'a da muka tsinci kanmu a ciki minene shawararka ga 'yan uwa a wannan,lokacin?
.
Nura Shaheedi: "To dama sunan abinda muke shine gwagwarmaya saboda haka jagora (H) ya gama sanar damu cewa akwai jarabawoyi iri-iri a tafiyar, shawara ta itace mubi umarnin jagora a duk yanayi domin shi bai barmu a duhu ba duk yanayi ya gaya mana irin matakin da ake daukar masa.
.
Ma'asumiyya: A kalla yanzu waqoqinka sunkai nawa kuma a ciki waccece Bakandamiyarka?
.
Nura Shaheedi: "To shekara uku da suka wuce nayi bikin cikar wakokin na dari biyu da yan kai (200+) amma yanayi bai bari nayi bahasin na bana da na bara ba kuma, bakandamiyar ba boyayya bace itace garkuwa wato (mai maganin dawagitai Al zakzaky waliyullah)
DANNA BOTTOM DINNAN DOMIN KAYI DERLODING DINTADINTA
makandamiyar nura shahidi |
Ma'asumiyya: Akwai matasan nawaqa masu ta sowa a cikin harkar nan, wanda kusan babu kalar da babu minene shawararka a garesu a matsayinka na tshohon mawaqi?
.
Nura Shaheedi: (Dariya) idan kace tsohon mawaki wanda yayi ritaya kenan saidai dadadden mawaki to shawara ta ga matasan mawaka shine su kiyaye da kurakuran da magabata suka yi su dauki izina sannan suyi nazarin nasarorin magabatan ya zama musu darasi, kuma su fahimci zamanin su kuma suyi dan Allah ba riya ba hassada to Insha Allahu In suka yi haka to ina musu albishir da nasarori."
.
Ma'asumiyya: (murmushi)
Me Zakace game da wannan Shafin na Ma'asumiyya, shawara ko makamantan su?
.
Nura Shaheedi: "Abinda zan ce ga wannan shafi na Ma'asumiyya shine ku sani shafin ba na mutum bane na A'imma ne (a.s) Sabo da haka duk wanda ya tsinci kansa cikin masu yiwa shafin hidima ya gane cewa Allah ne ya azurta shi da yiwa addini aiki kuma amanar Sahibuzzaman (Ajf) ya dauka sai ya godewa Allah ya kuma nemi taimakonsa da sabati."
.
Ma'asumiyya: A karshe ko akwai wani abu da kake son furtawa ko wane saqo da kake son isarwa wanda a cikin tambayoyinmu bamuyi shiba?
.
Nura Shaheedi: "Sakona ga masu sauraron wakoki na harka musamman masu hannu da Shuni su fahimci cewa hidimar waka ba sassaukan aiki bane dan haka suma akwai nauyi da ya kamata su sauke wajen isar da sakon harka ga alumma ta hanyar wake suyi musharaka a cikin ladan aikin kamar mawaka."
.
Ma'asumiya: Kamar Yadda kace Masu Hannu da Shuni kana nufin (Ahlul Dusur Kenan) ? Kuma Kamar wane irin taimako kukeson subaiwa mawaka??
.
To muna iya cewa ahlul dusur tunda dasu muke tare, suna iya taimakawa harkar wale ta sigar da allama ya taba bada misali a loncin din Ittihadu da ya gudana a kano misali wani na iya daukar nauyin buga waka da yada ta (producing and distribution )dan shima yayi musharaka da wanda ke da baiwar Waka a lada wajen isar da sakon harka.
.
Ma'asumiyya: Mun gode garkuwan 'yan caji do lokacinka daka bamu.
.
Nura Shaheedi: "Nima na gode Malam Salisu Mazaje."
.
Daga
Ma'sumiyya Nigerian News Update
Tare da Wakilinmu
Salisu Umar Mazaje
09021381323
Tacewa Mas'udu dan masani shinkafi 08149993999
Tags:
Filin Mawaka