KIRA GA ITTIHADU:- kar mu bari ya zama waqoqinmu in munyisu saimu yan Harka ne kadai zamuji su.




Inji Adamu ittihadu jalingo (dan Fulani)

Ma'asumiyya Nigerian News Update 🌎
Filin mawaqan mu
Tare da dan wakilinmu Salisu Umar Mazaje
.
A yau muna tafe muku da hira da Shaharerren mawaqin fulatancin nan  wato,
Malam Adamu Ittihadu Jalingo (Adamu dan fulani)
.
MA'ASUMIYYA: Masu sauraronmu zasu so suji dawa muke tare a wannan lokaci tare da dan takaitaccen tarihin ka??
.
ADAMU ITTIHADU: "Sunana Adamu Muhammad bello, amma dai Jama'a sun sanni ne da Adamu Ittihadu Jalingo, ko Adamu Dan Fulani.

Nidai An Haifeni ne a wani Gari da ake Kira Tau  cikin Jihar Taraba Nigeria, Mahafina shine Muhammad bello, Mahaifiyata Hauwa Adamu.

Mahaifina Shine  limamin masallacin Tau, sana'anmu noma

Dana Fara girma ne Kakana ta daukeni zuwa wurin Yayana a Jalingo inda na Fara karatun boko dana Addini, karatun ne dai cikin Ikon Allah da Ni'imarsa har nasamu daman Zuwa nan Iraq inda nake karatun yanzu.

A wurin Yayana Muhammad ne na Fahimci Harka Islamiyya muna fatan Allah ya tabbatar damu."
.
MA'ASUMIYYA: Ajib ya Ilahee
Allah shi gafarta kun zamo wani jigo a cikin wannan harka ta Ittihadu Musamman kasan cewarka mawaqi na fulatanci sabanin sauran mawaqan da muke dasu, shin minene ya ja hankalinku ga haka, kuma yaushe abun ya fara gudana??
.
ADAMU ITTIHADU: "Alhamdulillah dayake ni tun ina karami inajin mahaifiyata tana karanta irin waqoqin Ishiriniya, Wafatin Annabi, haka mahaifina, a duk lokacin dayake aiki zakaji yana iri wadan nan waken, da wasu kirari dai wa Annabi (saaw), irin dai waqen maluma haka.

Toni tun lokaci intanayi yana min dadi musanman na Wafatin Annabi, har zaunawa nakeyi nace tayimin naji , kafin Allah yayi mata Rasuwa.

Toni gaskiya tun lokacin sai yazama ina sha'awan waqen nima, to bayan zuwana Jalingo nedai ina saurarin waqoqin mawaqan Harka, sai ya qara min karfin gwiwa nan ne dai na fara kamar wasa, bazan mantaba farkon waqana wani malamina ne a Primary school nasamu ya Rubutamin Mal Ibrahim mai Qafiya, na zuwan Sayyed Zakzaky Jalingo da Hausa .

To daganan dai Nafara Rubutawa da kaina , lokacin na Hausa nake Rubutawa ba Fulatanci ba.

To sai daga baya naga tundani Asalina Bafulatani ne, mezai hana narinkayin waqen da Hausa da Fulatanci , don yan uwanmu Fulani su amfana, su San irin zaluncin da akayiwa Ahlulbaity (a.s) musanman wadanda basajin Hausa.

Hakane dai na Fara wakan Fulatanci kamar wasa sai yazama yafi na Hausa danakeyi karbuwa a ko ina, nanda nan Jama'a sai Neman  sabbi sukeyi na waqoqin Fulatanci, Gidajen Redio duka dai sawa akeyi Neman sabin waqoqi kullum sukeyi, Fulani kuma daga Kasashe daban Daban kirana sukeyi suna turomin saqonni, har Fulani yan Africa dake Irin Saudiya suna kirana, wasu har gobe ma muna mutunci dasu sosai.

To wannan yana cikin abinda yasa naga ya dace nayi amfani da wannan dama ta waqe wurin isarda sakon Ahlulbaity (a.s)."
.
MA'ASUMIYYA: farkon farawa zuwa yanzu ko akwai wani kalubale da aka fiskanta?
.

ADAMU ITTIHADU: "Alhamdulillah ba wani kalubale, Illa dai irin abubuwan da baza'a rasaba Wanda su kuma ko meye dama in mutum zaiyi sai ya jure yayi haquri kafin ya kaiga gaci."
.
MA'ASUMIYYA: Nasan zuwa yanzu kusan ko ina a fadin kasar nan dama wasu kasashen sunan Adamu Ittuhadu ya ratsa musamman a rewacin kasar nan shin ya kaji kasantuwar haku kuma wanne tanadi kakewa masu sauraro?
.
ADAMU ITTIHADU: "To Alhamdulillah shi sanuwa ba don mutum yafi kowa bane yake samu ba, kuma ba don yafi sauran mawaqa Hikima bane, shi sanuwa ni'imane na Allah inyaga dama asan mutum sanadin waqa daya sai duk kowa yasanshi, misali kafin insoma waqama ai akwai mawaqa a Jalingo kuma ni sanuwata tazone bangare biyu gefen yan Harka da gefen Sauran Jama'a musanman Fulani domin mu Fulani muna da kishin Yarenmu! Sosai indai Abu da yarenmu akayi to kawai ji muke namu ne kaitsaye.

Insha Allah zanyi iya kokarina wurin ganin na inganta waqoqina sun ciga jerin waqoqin mawaqa na zamani don masoyana su gamsu daidai gorgodo.

Musanman waqoqina na Fulatanci zanyi kokarin ingantasu sosai daga Sauti Videos , sannan zanyi kokarin samar da hanyoyin da waqoqin zasu rinqa isa ga Al- umma da masoyana cikin Sauqi."
.
MA'ASUMIYYA: Yanzu a kalla waqoqinka zasu kai nawa?
.
ADAMU ITTIHADU: "A kalla zasu kai talatin (30)"
.
MA'ASUMIYYA: A cikin waqoqinka waccece kamar Bakandamiyarka?
.
ADAMU ITTIHADU: "Bakandamiyata itace Jabbama Rasulullah, sai wacce ta biyunta,mai taken Zakzaky Jabbama."
.
MA'ASUMIYYA: Da kuka je kasar Iraq wanne cigaba kuka samu, ko kuke samu wanda zai kara fadada ita ittuhadu a idon duniya?
.
ADAMU ITTIHADU: "Gaskiya naga abubuwa da dama musanman yadda mawaqa suke inganta harkokin waqoqi da hanyoyin Isarda waqan ga al'umma ta hanyoyin Social Media, kamar su Facebook, Twitter, Whatsapp, You tube da sauran su."
.
MA'ASUMIYYA: To kenam yanzu akwai wani tanadi da kukeyi wanda zaku dawo mana da shi dan kara fadada Ita harkar a anan gida Nigeriya?
.
ADAMU ITTIHADU: "Insha Allah akwai wasu tanadi na musanman gasu mawaqa da shawarwari."
.
MA'ASUMIYYA: Anyi gasar waqa Akan Sayyida zahra (sa) kwananki da suka gabata ya kukaji faruwar wannan babban al'amari a zukatanku a can?
.
ADAMU ITTIHADU: "Gaskiya nayi Farin ciki sosai daganin yadda Gasan ya gudana , duk da cewa bana Nigeria.

Domin hakan zai kara karfafa Mawaqa Sosai, da kuma kara zumunci da soyayya a Tsakanin Mawaqan Harka.

Allah yasakama wadanda suka shirya wannan Gasan na Mawaqan."
.
MA'ASUMIYYA: Muna da matasan mawaqa a harkar nan, kusan zance ba kalar da babu, bangaren waqoqin bege da yaruka daban-daban kamar irin hausa fulatanci dama waqoqi na turanci Rabs da sauransu, shin wanne jan hankali kake dashi a garesu kasantuwarsu matasa don inganta harkar?
.
ADAMU ITTIHADU: "Jan hankalin da zanyi ga abokaina matasan Mawaqa na harka dai bai wuce ince Mawaqi yayi kokarin inganta waqoqinsa, to tayaya zai inganta waqoqinsa? dole akwai bukatan Ilimi, Duk wani abu inkanada ilimi akai to inkazo yinsa zaka gashi daban ne.

Ta haka ne zamu samu dama Fadan abinda ya dace sosai a waqoqinmu ta yadda masu Jin wadan nan Yarurrukan zasu gamsu sosai.

Sannan muyi kokarin samar da hanyoyin da waqoqin zasu ringa shiga cikin Jama'armu musanman masu amfani da yarurrukanmu, musamu alaqa sosai  dasu ta yadda zasu rinka samun waqoqin Annbi da Iyalansa tsarkaka, kar mu bari ya zama waqoqinmu in munyisu saimu yan Harka ne kadai zamujisu.


Wannan alaqa kuma yafi sauqi ta hanyoyin Social Media.
.
MA'ASUMIYYA: A karshe ko akwai wani abu da kake son fada mai muhimmanci wanda bamu tambaya ba?
.
ADAMU ITTIHADU: A Karshe dai ina rokon masu Sauraron idan akwai abinda na fada cikin kuskure tosumin Afuwa, da sauran Mawaqa , Sanna  Inayiwa MA'ASUMIYYA MEDIA godiya da kuka bani wannan dama, ina muku Fatan Alheri Allah ya taimakeku ya kuma Tabbatar damu tare da Jagoranmu Maulana Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) Allah ya gaggauta kwato manashi daga Hannun Azzalumai.

Na Gode.
.
MA'ASUMIYYA: Mun gode Malam Adamu
.
Daga
Ma'asumiyya Nigerian News Update🌎
Tare da Wakilinmu
Salisu Umar Mazaje
09021381323

3 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post