Mu yan northwest mune muka baiwa buhari kuri,a mafi rinjaye kimanin million bakwai da dubu Dari biyu
Ragowar jahohi goma sha bakyai kur,u million uku da dubu Dari biyu suka baiwa buhari
Buhari yayiwa kasar kudu aiki yaki yayiwa kasar Hausa aiki dalili
Fashola yafadawa mutanensa cewa kuzabi jam,iyyar APC ta dawo mulki sabida munyi maku aiki munyi maku manyan tituna a southwest guda 68
(1) Jihar Lagos tasamu manyan tituna guda goma sha Tara
(2) jihar Oyo tasamu guda goma sha udu
(3) jihar Ogun tasamu guda Tara
(4) jihar osun tasami guda goma sha biyu
(5) jihar ondo tasami guda Tara
(6) jahar ekiti tasamu guda Biyar 5
Duk irin kuri,un da muka bashi aduk fadin northwest guda biyu Buhari yayimana kamar haka na farko titin daya tashi daga tambuwal zuwa sokoto
Na biyu shine kano kaduna zuwa abuja
Munbashi kuri,a tafi tasu kuma shugaban kasa Muhammad Buhari yayi alkawari cewa zai baiwa wadanda suka bashi kuri,a fiyeda wadanda basu bashi ba
Duk ba wannan ne abin mamaki abin takaici ba
Fashola yasake fadawa mutanen yankinsu cewa kuzabemu domin munyi maku gidajen wutar lantarki guda 36 akasar yarabawa
Gasu zan lissafosu kamar haka
(1) shagamu surf station
(2) akwai Ibadan surf station
(3) akwai Oshogbo ebe
(4) akwai owere Oshogbo rony road
(5) akwai nuhu akure surf station
(6) akwai ijebo surf station ondo
(7) akwai oyobo ejida surf station
(8) kere eborene surf station
Wannan kadan ne daga ciki
Zan dawo northeast mu guda nawa akayi mana kucemin guda daya takkk shine Wanda akeyi a Kaduna state mai kilowatt 215
Karmu manta fashola yace anyi guda 36 a kasar kudu su masu kuri,a Million uku da wani Abu
Amma mu da muka bada kuri,a million bakwai da dubu Dari da hudu
Sai harkar sifri wato transportation rotumi amechi yamike yace kuzabi APC badan komai ba sabida munayi maku titin dogo daga Lagos zuwa kano awatan nan na December za,a gama acewarsa akan kudi dollar billion daya da million Dari shida
Idan ka change wannan kudin zuwa naira anayin titin jirgin kasan akan naira billion Dari bakwai da saba,in da shida acewar rotumi amechi
Osinbajo shine ya kaddamar da aikin ranar 7 /5/2017 sannan yakara dacewa idan akayi wannan aikin zai baiwa matasansu na tsakanin Ibadan zuwa Lagos mutum dubu Dari Biyar aikinyi
Mu a Arewa anbaiwa mutum dubu goma aiki shine kuke cewa wai ansallamemu
Idan kanaso ka tabbatar da gaskiyar magana ta kaje kaduba jaridar tribun ta yankin yarabawace sun bugata ranar 26/10/2018
Kokuma kaduba jaridar the nation gidan jaridar APC ne ta bola duba ranar 26/10/2018
Zakaga irin wannan aika aikar da akeyiwa yan arewacin Nigeria
Babu shakka wannan Abu yayi matukar batamin rai tuna
A watan April 2015 gwamnatin Good luck Jonathan akarkashin jagorancin minister education malam Ibrahim shekarau an tabbatar da jami,o,i guda biyu FCE kano dakuma FCT Zaria tsakanin katsina da kano da Kaduna sai ansami dalibai sama da mutane dubu goma sun shiga wannan makarantun amma Buhari yana zuwa akazugashi ya soke su duk da yasan cewa mune zamu Mora
Wani babban abin mamaki abin takaici mu wadanda yasokewa wadanda universities mune mukabashi kuri,a million bakwai da dubu Dari biyu
Ranar 16/10/2016 Buhari yasa bill na kafa sabuwar university na man fetur a irong delta state jahar da subashi kuri,a dubu Dari shida da sitti da biyu anyi masu sabuwar university awatan dayagabata aka basu naira billion Biyar na grand
Ranar 14/1/2016 uwar gidan shugaban kasa Aisha Buhari uwar yayansa tayi shira a gidan radio BBC tafadi wannan batutuwan tace akwai matsala domin gwamnatin tasu bata tafiya daidai tace akwai wasu mutane da suka hana mai gidanta aiki
Malam basiru el,rufai gwamnan Kaduna shine gwamnan dayafi kowanne gwamna kusanci da shugaban kasa Muhammad Buhari
El,rufai ya rubutawa Buhari memo akalla page talatin a watanni September 2016
Ga abinda yace our APC administration has fail
Ma,ana shugabancin da APC takeyi takasa aje aduba jaridar vungard ta ranar 17/3/2017 za,aga wannan abinda el,rufai yace
Sai kuma Hamid Ali shugaban custom yayi bayani kamar haka mun sauka daga kan abinda mukace zamuyi bamayin abinda mukace zamuyiwa yan Nigeria aduba jaridar the nation ta ranar 27/10/2017 kokuma premium time ta ranar 28/10/2017 zakuga wannan abin
Kunsan dai duk isarka a Nigeria bakakai first lady Aisha Buhari ba domin matarsa ce shekararsu 29 tare tace akwai kuskure
Hamid Ali shine chief of staff na Buhari yace akwai kuskure
Nasiru el,rufai aduk gwamnonin Nigeria babu kamarsa shine babban na hannun daman Buhari yace akwai kuskure
Sabida haka idan nace akwai kuskure kokuma wani yazo yace akwai kuskure yakamata ayimana adalci domin muma duk dalibaine karantawa mukayi
Amakonnin da suka gabata mai dakin shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari tafito tace mutum biyu ne suka hana mai gidanta yiwa jama,a aikin alkhairi
Adan haka inason mutane su fahimta duk Wanda kukaga na matsa akansa to yasauka daga layin gaskiya da amana
Ni babban burina agyara bazamuyiwa kowa sharri ba abinda kayi shi zamu fada bisa adalci
Idan kuma zakuyimin adalci in mun fito da kura kurai kudauka Ku gyara domin ba kirkira mukayi muka fada ba ba sharri mukayi ba domin mun ajiye hujja acikin bayanin
Matar shugaban kasa tace a taimaki mai gidanta agayamasa gaskiya ko Allah zaisa yagane
Allah yasa kuna sane da martanin da Buhari ya mayar akan matarsa akan irin wannan batun na fadar gaskiya to kunga kenan Ashe gaskiyar ce baya bukata
Da wannan dalilin nake cewa yan,uwana yan Nigeria su tabbatar sun zabi mutum Wanda suka tabbatar zaiyi masu adalci a tsarin gudanar da gwabnatinsa.
Tags:
Muhimman zantuka