To, kuma suna fada damu ne ta fagage biyu. Fagen farko, kai tsaye su da kansu su kai hare-hare da hujumi daban-daban, imma dai da makamai wanda suka yi, za a ga cewa; yanzu Amerika idan aka duba inda Sojojinsu suke a fadin duniya za a ga duk tana (Sojojinta) a kasashen Musulmi ne. Ko ina a kasashen Musulmi kashe-kashe suke yi. Suna da Soja ko’ina a kasashen Musulmi. Kuma ba su da wani aiki idan ban da kisan kai. Sun rugurguza kasashe yanzu daya bayan daya guda nawa? Sun yi Biji-biji da Afghanistan, kasa ce ta Musulmi. Sun yi biji-biji da Irak. Sun yi haka nan. Yanzu kuma sun shiga Siriya suna mutsutstsukata. Haka nan kuma, haka nan kuma. Kowace kasa haka nan daban-daban, kasashen Musulmi suke ta hankoro. Ba ya ga wannan, wannan shi ne ainihin yaki da makamai karfafa.
To sai kuma yakin cusa ra’ayi, wanda akan kokarin a cusa ma samari ainihin ra’ayoyi iri daban-daban na nuna kyamar Musulunci da kuma koya musu miyagun dabi’o’in tarbiyoyi musamman ‘yan mata. Don suna cewa ainihin; idan ka bata Yarinya Budurwa, to ka bata gida ne, domin don ita Yarinya budurwa nan gaba ba da jimawa ba zata zama Uwa. Idan kuma ta zama Uwa, zata haifi ‘ya’ya ke nan, zata yi musu tarbiyyah, saboda idan ka bata tarbiyyarta, to, ka bata tarbiyyar gidan da zata kasance anan gaba bada jimawa ba. Saboda haka sukan ta hankoron bata tarbiyyah da yin Fima-fimai. Da wadansu karikitai irin wanda ake nunnuwa ta hanyar su, yanzu ga hanyar sadarwa ya yi sauki. Su irin wayan nan na aljihu yanzu ana zuba abubuwa daban-daban. Ban da su Talabishin da ‘internet’, ainihin ana ta hujumi akan kwakwalen samari. To hanyar da suka fito da shi kwanan nan shi ne su nuna cewa; shi Musuluncin nan a nuna shi a mummunan kama. A nuna shi a matsayin shi ne ta’addanci. Shi Musulunci suna nuna shi shi ne ta’addanci. Saboda haka basu da wani labari idan banda ta’adda. Idan ka bude Rediyo, kana budewa zaka ji labarin abin da ake bayarwa shi ne; a ina ne an kai hari, a ina ne an kai hari, an yanka Jarirai, an yanka Mata, wai masu kishin addini ne suke yin wannan. Harma sunayen kungiyoyin nan, harma suna da wadansu sunaye. Daga a ce; Ansaruddin, wai harda Ansarullah , Ansarullah (mataimakan Allah). Da Ansaruddeen, Ansarul Islam dko kuma ainihin Jaishu Muhammad. Ko kuma Daulatul Islamiyyah (Islamic state). Yanzu wanda suke ta cewa; suna kashe-kashe din nan a Siriya da Irak, wai sunanta Daular Musulunci. Wato ke nan, duk lokacin, abin da kokarin a nuna maka idan ka ji an ce Daular Musulunci, ko ka ji an ce Shari’a ko ka ji an ce Alkur’ani, kawai abin da ake so ka fahimta wannan yana nufin ta’addanci ne. Haka kuma idan suna labarurrukan su a Talabishin, idan kana kallon Talabishin, duk lokacin da ake bada labarin ta’adda da kai hare-hare da kashe-kashe, to, zaka ga a lokacin da suke labarin suna nuna wadansu hotuna wanda suke so su kai sako a kwakwalwarka, cewa; wadannan su ne ‘yan ta’adda. Zaka ga a daidai lokacin an nuna Musulmi na Sallah, zaka ga ana ruku’u ana Sujjada (kamar a sallar Juma’a). Kuma zaka ga an nuna ana kewaya Ka’aba ana Dawafi, amma ana labarin ta’addanci ne. Sai kuma a nuna wani mutum da rawani da Gemu. Ko kuma a nuna yana rike da Carbi, ko kuma a nuna wata ta Gilma da Hijabi. Idan ana labarin ta’addanci ka lura da Talabishin da kyau. Wato abin da ake so a kwakwalen mutane, mutum ya fahimci wadannan alamomi na addini din nan, sune alamomin musiban duniya. Yanzu ba abin da ya dami duniya (a yadda suke kokarin su nuna), illa Musulunci shi ne babban Musifar da ya fuskanci duniya ke nan.
Wani bangare na jawabin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da ya yi a Maulidin Manzon Allah na Khatama da ya gudana a wajen Masallacin Kofar Fada dake cikin garin Zariya. A ranar Asabar din 4 ga watan Rabi’us Sani, 1436. Ammar Muhammad Rajab ya rubuta muku.
Tags:
Jawaban Shek Zakzaky