Karkumanta kuna tare da Ma'asumiya Nigeria News Updates
Tabbas, idan ka fassara munafukan wannan zamani da sunan kafirai ba kayi laifi wajen Allah ba, domin sun fi kusantaka da kafiran.
Kalli halayya da kuma ayyukan Wahabiyawan Saudiyyah, a suna sukan amsa sunan muslimci, amma a ayyuka irin aikin kafiran Yahudawa suke yi.
Ba za ka fahinci hakan ba sai ka nazarci soyayyarsu gare su, da kuma qiyayyarsu ga musulmi.
Su irin wadannan mutane da muke magana a Kansu, sun watsu ko ina har cikin wannan qasa tamu Nigeria. Suna rayuwa da aiki a madadin kafircin duniya.
Huzaifatul Yamani (SAHIBUL SIRRIN-NABIY ) yana cewa;
" ABIN SANI MUNAFURCI YA KASANCE A ZAMANIN MANZON ALLAH (S.A.W.W) NE, AMMA A YANZU KAFIRCI NE BAYAN IMANI ."
(Bukhari, hadisi na 7114).
Ba Wahabiyawa kadai bane, cikin kowacce da'awa suna nan birjik, kuma kafirai suke yiwa aiki. Wadannan sharrinsu ya fi na munafukan zamanin Manzo (S.A.W W). Kamar yadda Huzaifatul-Yama
ni ya sake fada.
" LALLE MUNAFUKAN WANNAN ZAMANI, SHARRINSU YA FI NA ZAMANIN MANZON ALLAH (S.A.W.W), DOMIN A WANCAN LOKACI SUNA BOYE MUNAFURCINSU, AMMA A YANZU BAYYANAWA SU KE YI ."
(Bukhari, hadisi me lamba 7113).
Za mu qarqare wannan magana da fadin Allah (T) cewa;
" LALLE ALLAH ME TARA KAFIRAI DA MUNAFUKAI NE CIKIN JAHANNAMA GABA 'DAYA !"
Allah ka raba mu da kafirci bayan imani.
Daga wakilanmu na Zone din Bauchi, Gombe da Adamawa.
Tare da (Ado Isah Guda).
08137925034/08126385470
Tags:
Tunatarwa