WASU SIFFOFIN SHEIKH ZAKZAKY (H) DA DAN FODIYO (TR) YA AMBATA

Daga shafin; MA'ASUMIYYA NIGERIA NEWS UPDATES

Mujaddadi shehu usman dan fodiyo (tr) mujaddadi, wato siffofin gane kowane mujaddadi alittafinsa 'sirajul ikhwan' wadanda suke dukkansu malam (h) yariga daya misaltu dasu. Ga abinda shehu dan fodiyo yake cewa: 'ba makawa ga wannan malami na kowane karni,yanayinsa yakasance yana acikin umarni da aikin kwarai da kuma hani da mummunan aiki. Da gyaran lamuran jama'a da kuma tabbatar da adalci a tsakaninsu.

Da taimakon Gaskiya akan karya da kuma wadanda aka zalunta akan Wanda yayi zalunci. Zai sabawa yanayin malaman zamaninsa. A kan wannan zai kasance bako atsakaninsu. A saboda kadaitar yanayin siffarsa da kuma karancin misalinsa (samun irinsa).

Mun fitar da siffofinsa guda tara daga wannan zance na shehu dan fodiyo (tr) wadanda ya kawo. Ga yarda muka jero siffofin:
*.umarni da aikin qwarai da Kuma hani da mummunan aiki
*gyaran lamuran mutane
*Tabbatar da adalci a tsakanin mutane
*Taimakon gaskiya akan Karya
*Taimakon Wanda aka zalunta akan Wanda yayi zalunci*
*Sabawa yanayin malaman zamaninsa.
*Kasancewa bako atsakanin malamai.
*Kadaitar siffar yanayinsa.
*Karancin samun irinsa.
Kamar yadda muka kawo cewa malam (h) ya riga ya misaltu da siffofin nan duka.

Idan mai karatu yanada masaniya,idan kuma yana biye da kokari da malam yake yi a tafarkinsa na tajdidin musulunci a wannan kasar, to hakika zai tabbatar da cewa malam (h) ya riga ya cike dukkanin wadannan siffofin da shehu dan fodiyo (tr) ya ambata a matsayin siffofi na gane kowane mujaddadi.
Daga wakiliyarmu
*Sukhaina Ahmad Sadiq Kazaure.*

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post