Daga shafin Ma'asumiya Nigeria news update
# Bashir_AdamWallahi mu muna bin Sayyed Zakzaky bisa ikilasi da yaqinin cewa shi mujaddadi ne kuma wakilin Imam Mahdy (AF) a doron qasa, domin shehu Usman dan fodio yayi bayaninsa da garin da za a haife sa da sunan sa da sunan garinsa.
Shehu dan fodio yace , " Akwai wani mujaddadi da zai zo Sunan sa Ibrahim sharfudeeni kuma da'awar tayi daban da sauran malaman zamaninsa to lallai ku bishi ."
Dan haka muna da hujjojin da yasa muke binsa domin malamai da daman gaske sunyi busharar zuwansa.
Bari na wuce domin fadin abinda nake so na fada, ni dai a bakin tasowana ban taba jin Sayyed Zakzaky (H) ya fada mana qarya ba, kuma wallahi duk abinda yace mana zai faru to nidai wallahi naga sun faru da idanuwana, dan haka ni dai ina bin Sayyed ne da yaqinin cewa shi mujaddadi ne kuma mai ceton al'umma daga hannun Azzalumai irin su Buhari mai qashin tsiya.
Dan haka duk wani abinda Buhari yayi mana na ta'addanci to Sayyed Zakzaky (H) ya sanar damu cewa lallai wadannan waqi'o'in zasu faru damu, dan hakama yace, " Duk wanda bai shirya bayar da ransa ba a cikin mu to yaja baya ."
Wallahi koda zaku bindigemu sau 1000 ku qara tayar mana da rai sau 1000 sannan ku qara bindigemu sau 1000 ba za mu bar Sayyed Zakzaky ba, balle ma ba ku da ikon yi mana hakan.
Allah qara sanya mana qaunar Sayyed Zakzaky (H) a zukatan mu, dana 'ya'yanmu.
Allah kuma ka gaggauta kwato mana jagoranmu a hannun wadannan baqaqen azzaluman su Buhari mai Qashin tsiya.
# free_Zakzaky !!!