MIYAGUN MALAMAI SUNE MUSABBABIN JEFA QASA CIKIN BALA'I !!!

Daga Shafin MA'ASUMIYA NIGERIAN NEWS UPDATES
______________________________
Komai na da sanadi, idan kaga mutum ya fada cikin mummunan yanayi wanda ba jarrabawa ce daga Allah ba, to shi ya janyowa kansa.
Jarrabawa daga Allah ita ce wacce mumanan ayyukan wani ko wasu ke janyo ta. To, mu a halin da muke ciki na qunci sakamakon miyagun malaman da muke da su ne.

Allah (T) ya zargi Banu Isra'ila inda yake cewa,
" ALLAH YA LA'ANCI WADANDA SUKA KAFIRTA DAGA BANU ISRA'ILA BISA HARSHEN DAWUDA DA ISAH 'DAN MARYAMA. HAKAN KUMA SABODA SABAWAR DA SUKE YI NE, KUMA SUN KASANCE SUNA QETARE IYAKA ".
" SUN KASANCE BA SA YIN HANI DAGA ABIN QI DA SUKE AIKATAWA. TIR DA ABINDA SUKA KASANCE SUNA AIKATAWA ".

" ZA KAGA DA YAWA DAGA CIKINSU SUNA JIBINTAR WADANDA SUKA KAFIRTA. TIR DA ABINDA RAYUKANSU YA GABATAR SABODA SU, ALLAH YAYI FUSHI DA SU, KUMA A CIKIN AZABA ZA SU DAWWAMA ".
(Ma'ida, aya ta 78-80).
Yadda Banu Isra'ila suke yi shine, mutum zai hadu da dan'uwansa yace masa kaji tsoron Allah kabar abinda kake yi, amma washe gari in ya ganshi yana aikata irin wannan aiki ba zai sake ce masa komai ba.
Malamanmu na wannan zamani kuwa sunfi na Banu Isra'ila muni, domin ga shi ana fasàdi cikin qasa ba sa iya cewa komai a kai, sai dai ma su goyi bayan masu wannan aiki don neman duniya, kuma su riqa kasancewa a gindinsu suna neman gurin zama.

Manzon Allah (S.A.W.W) na cewa,
" LALLE ALLAH BA YA AZABTAR DA AL'UMMA GABA 'DAYANTA SABODA AYYUKAN WASU, HAR SAI SUN KASANCE SUNA GANIN ANA AIKATA MUMMUNA A TSAKANINSU KUMA SUNA DA IKON SU NUNA RASHIN AMINCEWARSU AMMA BA ZA SU NUNA BA. TO, IDAN SUN AIKATA HAKA SAI ALLAH YA AZABTAR DA KEBABTATTUN (masu laifin) DA SAURAN AL'UMMA ".
(Musnad Ahmad, J:4,Sh:192)
ALLAH KA RABA MU DAGA WANNAN BALA'IN.

Daga wakilanmu na Zone din Bauchi.
Tare da (Ado Isah Guda).
08137925034

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post