IDAN BA KA DA GATA ZA A IYA FADAR KOMAI MA A KANKA !
MA'ASUMIYA NIGERIAN NEWS UPDATES
Abdullahi Bn Ubaiyi Bn Salul shine kadai wanda za ka iya kama sunansa kace munafuki daga Sahabban Manzon Allah (S.A.W.W), alhali ba Qur'ani ne ya ambaci sunansa ba.Allah (T) yayi magana kan munafukai a gurare da dama cikin Qur'ani, har ma Surah ce sukutum ta sauka a Kansu. Amma duk da haka sai kaji sunan mutum daya (1) rak ake ambatowa don rashin gata.
Tabbas, babu mai kokwanto cewa shi munafuki ne ciki da waje, amma duk maganganun da ake yi kan munafukai da shi kadai ake yi?
Kada na cika ku da surutu har ku soma tuhumata da cewa tunda ba shi kadai bane to na fadi sauran mana!
A'a, lalle nima karantawa nayi, ku biyoni don ganin hujjata kan wannan magata da ba ku son jinta.
Imam Ahmad yace, Waki'i ya bamu labari, Sufyanu ya bamu labari daga Salamata Bn Iyadh, daga babansa, daga baban Mas'ud Uqbatu Bn Amru yace, Manzon Allah (S.A.W.W) yayi mana Khudba, ya godewa Allah (T), yayi yabo gare shi, sannan yace,
" LALLE DAGA CIKINKU AKWAI MUNAFUKAI, DUK WANDA NA KIRA SUNANSA YA MIQE "! Sannan yace,
" YAA WANE MIQE TSAYE ! YAA WANE MIQE TSAYE !! YAA WANE MIQE TSAYE !!! Har sai da ya ambaci mutane talatin da shida (36), sannan yace,
" LALLE A CIKINKU, KO KUMA DAGA CIKINKU AKWAI MUNAFUKAI, KUJI TSORON ALLAH "!
Yace, said Umar ya hadu da wani mutum daga cikin wadanda aka ambaci sunayensu a tattakure, kuma (Umar) ya riga ya san shi. Sai yace,
" MEYE GARE KA "?
Sai ya bashi labarin abinda Manzo (S.A.W.W) ya fada. Sai yace,
" SAURAN KWANUKA (days) SUNYI NISA GARE KA "!
(Musnad Ahmad, J:5, Sh:273).
==== ABIN MAMAKI ====
______________________________
Cikin mutane 36 nan da aka ambata amma ace duk an manta sunayensu? To, idan kuwa gata ce wannan, lalle an cutar da addini. Domin ya kamata a fadi sunayensu kamar yadda aka fadi sunan dan'uwansu don a nisanci aikinsu.
Daga wakilanmu na Bauchi Zone.
Tare da (Ado Isah Guda).
08137925034/08126385470
Editing Mas'udu Dan Masai Shinkafi
Tags:
Makaranta