•Part 2, ABUN DA YAJA HANKALI NA ZAMA DAN SHI'A!!


Inji Abdulrazak sani. 

                  Ci gaban Labari na a inda muka tsaya......
Daga Shafin [M.N.N.U-MA'ASUMIYA]

            Tare da wakilin mu Habib Rabiu Nasralla


Jim kadan bayan na kammala sauraran hadithn salmanil farisi, shakka babu zuciyata ta girgiza, yanayina ya sauya, dukkan sassan jikina sun yi rauni fiye da yadda mutum ya ke zato, wanda a dai-dai wannan lokacin bayan na kammala salloli wanda na dauki tsawon lokaci bana yin su,  abin da zan iya ki yayewa shi ne ina sallar asubahi shima ba kullum ba, ina cikin wannan yanayi bansan lokacin da na fashe dakuka ba,  sakamakon yadda naji yadda ake bayanin lahira kai ka ce a gabana ake yi ta yadda na ji bayanin mutuwa da kuma bayan mutuwa, ina cikin wannan hali tun ina kukan zuci ban san lokacin da kukana ya fito filiba, can zuwa wani lokaci ban ankaraba sai naji mahaifina da maman mu sun shigo daki na suna cewa dani lafiya abdul?  Amman ina alokacin kai na yana kasa na yi sujjada ina kuka ban ankara ba sai naji murya na cewa KAI ABDUL....ABDUL.. ABDUL...  LAFIYA?  Da ya ke hankali na ga badaya ya tafi,  sai jina yi mahaifina ya sa hannuwan sa ya dogoni, nan take ban san lokacin da na rungume abban mu ba ina cewa abba ka ya femin abba na tuba, abba dan Allah ka yafemin ita ko mahaifiyata nan take batasan lokacin da hawaye ke gangarawo daga idanun ta aba,  abun da zan iya tunawa shi ne naga mahaifiyata ta sa hannun ta tana goge fuskarta, a dai dai wannan lokaci ban san lokacin da na nufi wajan maman mu na fadi kasa tare da rike kafafunta ina cewa mama ki yimin aikin gafara na tuba mama.

Ya na yin da ake ciki yasa sauran yan uwana suka nufo dakina sakamakon sunji sautin kuka shugowar su ke da wuya sakamakon halin da sukaga ina ciki suma gaba daya tausayina ya kamasu, mahaifiyata tasa hannun ta ta dagoni ta ce abdul na yafema ka duniya da lahira tasa hannuna ta ta na gogemin hawaye, mahaifina kuwa ya tsaya ya yi shiru cike da mamaki domin Tabbas kamar yadda mutane ke fada shakka babu shiriya ta Allah ce,  duk kan matakin da mutum yasani ya dauka dan yaro ya shiryu zan iya bugar kirji nace babu wanda mahaifina bai yiba, yar takai ya zubamin ido mahaifiyata kam babu abin da batai ba iya ka iyawar don ganin na shiryu amma ina ko kusa, ko Ala'ama, wanda a wannan satin na daukewa maman mu sarkar ta da a war waran ta set guda na gold na je nasiyar da ni da abokaina wanda hasalima abisa haka sai da ta fadi sabo da tsananin bacin rai na, shiko mahaifina nasha dauke masa kudade wanda ban san adadiba, wanda akwai wani abu kwaya daya tak da nakewa Allah godiya duk irin munanan aiyukan da muke zuwa muke aikatawa ba mu taba sha'awar daukar kayan wani ba, ko muyiwa wasu kwace mu dai bar mu da munan aiyukan mu.

Hakika iyayena na sasu kuka wanda ni kaina bansan adadiba, bacin raina kuwa yasha sa iyayayena faduwa, wanda kuma ko ajikina ban damuba.

Bayan mahaifina ya yi shiru ya cika da mamaki wai yau ni ne abdul na ke kuka agaban sa abu kamar wasa, ya dubeni ya ce cikin murya me ban tausayi sauran yan uwana duk suna kallan mu, cikin murya me dauke da sautin kuka ya ce abdul na yafemaka, ina fatan yasa shiryuwar ka shi ne silar shiryuwar kannan ka baki daya. Jin haka ke dawuya mai bina Abubakar ya ce abba wlh mukan mu ba'a san ran mu muke aikatawa ba Amman abba insha Allah mun yimaka alkawari bazamu sake bata maba, abban mu ya fashe da kuka ya ce babu wani abu na yafemuku duniya da lahira, Allah ya yi muku albarka, ita ko mahaifiyar mu kukan dadi ya lullubeta, kan war mu ta nufi wajan maman mu tace mama insha Allah daga yau duk abin da kuka umarce ni zan yi, ni dai duk da irin maganganu da mahaifana suke da sauran yan uwana hankalina ba ya tare da su gaba daya kuka kurum na ke maman mu tasa hannuta ta dago ni ta ce ya isa abdul tashi kaje ka wanke fuskar ka, ya isa haka.

Bayan abubuwan da suka faru sun faru, a wannan daran baci sai dai na ce barawo, a wannan dare sai zuciyata ta fara sauwalamin shin wannan wanne malami ne, domin hatta ya na yi maganar sa ta fita daban,  baya ga haka ko da lokacin ramadan mukan dan shiga taitayin mu, ni da abokaina mukan dan ji wa'azizzika na malamai musamman tafsir amman ni ko a redio ban taba jin muryar wannan malami ba, hakan yasa na fara tunanin yakamata na tanbayi jawad wannan wanne malamine,  cikin hanzari na dakko wayata wadda take cike da kayan masha'a kala-kala da zumar na kira jawad domin nakosa na tambaye shi wanne malami ne wannan?
Domin ina ganin gobe kamar sam sam bata yiba,  a daidai wannan lokacin ina kira sai na ji wayar sa akashe.

Hakan yasa dole na hakura  a wannan lokaci, batare da bata lokaciba duk wani abu da nasani wanda yasa bawa sharia na take na yi deleted nasu.

Washe gari kuwa da wuri na farka tun misalin karfe 4:02 na dare, wanda da yake ranar zamu zana jarrabawar karshe ta fita daga matakin secondary bazan taba mantawa ba biology muke da ita.
A wannan rana ni naje na tashi abban mu daga bacci wanda a ranar bacci ya yimasa nauyi, da a sauran yan uwana.

Bayan da lokaci ya yi driver yazo ya dauke mu, wanda na takaita muku zance ban shiga makaranta ba sai da carbina a hannu wanda hatta shi kansa driver gidan mu yasha mamaki da yake baba muke cewa da shi, ya dubeni ya ce malam abdul yau kai ne da carbi?  Na dan yi murmushi domin taciki na ciki ta baka na abaka.

Haka na shiga makaranta tun daga malaman makarantar mu zuwa dalibai kowa mamaki ya ke, abokaina kuwa wanda muke aikata masha'a har wasun su na yimin isgili to ustaz ka ce jiya ka zama ustaz suka fashe da dariya ni kam sam-sam ban ma bi takan su ba,  na nifi hole ganin yadda sukaga ban yi dariya ba kuma tabbas ina cikin damuwa sai suka rabi da ni.

Da shiga ta hole na fara dubawa ko zan ga jawad  amman ban gan shiba can zuwa jimawa sai na ga an kawoshi a motar gidan su. Allah-Allah nake ya shigo batare da 6ata lokaci ba, ya shigo muka gaisa ya dubeni ya ce Abdul to adai samu a addua domin shima yaga carbi a hannuna na yi murmushi na ce wai kuwa daman inason in tambaye ka jawad jiya na saurari karatunan wai shin dan Allah wanne malami ne haka? Jawad ya dubeni ya yi shiru na wasu dakika ya ce ko kasan SHEIK IBRAHIM AL ZAKZAKY?  A'A NA DUBESHI NACE DA SHI WAKACE ZAKZAKY WANDA NASANI?

NAN DANAN SAI KAINA YA FARA SARAWA DOMIN KO DAWASA BANTABA ZATAN JAWAD ZAI FADAMIN HAKA BA,  NA SAKE DUBAN SA ZAKZAKY NA ZARIA DAI?  YA CE EMANA. NAN TAKE BIRON DA KE HANNUNA YAFADI A NA HAKA SAI MALAMAN MU SUKA SHIGO DON SURABA MANA JARRABA SU DA SUPER VAIZAS ...
______________
Karshen tika tiki tak inji Dan Hausa... Yanzu dai Abdul yasan ko tafsirin wa ya saurara a Daren jiya ko ya zata kaya  bayan can baya makiyinsa ne haka ma mahaifansa sunkoya masu tsanar malamin??

Kuci gaba da kasancewa da shafin MA'ASUMIYA NIGERIA NEWS UPDATES domin cigaban wannan labarin.
__________________
zan cigaba inshaallah.
__________
Daga dan uwanku har kullum Habib Rabiu Nasrallah

Email:habibrabiu81@gmail.com
Editing; Mas'udu Dan Masani Shinkafi

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post