Na Rubuta tambayoyi guda Ashirin (25) da Zan yiwa Sheikh Zakzaky!!

 -alhaji magaji


Ma'asumiya Nigeria news updates

 Daga:-Haruna shuaibu

Masu wannan shine Hirar da wakilinmu haruna shuaibu yayi da alhaji nuhu ahmad suleja.

A cikin wannan filin namu na yadda na fahimci harkar gwagwarmaya wacce sheikh Ibrahim al'zakzaky yake jagoranta.

Asha karatu lafiya


_Wakilinmu:_-assalamu alaikum

*Alhaji magaji:-*
Wa'alaikas salam

_Wakilinmu:-_ Masu karatun mu zasu so ka gabatar da kanka a garesu.

*Alhaji magaji:-*
 Sunana alhaji magaji suleja,
kuma ta wani fannin ana kirana da nuhu ahmad suleja ko ta 6angaren mu'assasatush shuhada'u ma suna kirana da Nuhu ahmad suleja,

Kuma an haifeni ne acikin garin kahutu dake karamar hukumar danja dake nan a katsina a yanxu
A shekara ta 1370BH --1949M.

_Wakilinmu:-_ Masu karatun mu zasu so ka fadi masu yadda rayuwarku take a baya kafin ku fahimci wannan harkar wacce sheikh Ibrahim Al-zakzaky yake jagoranta?

*Alhaji magaji:-*
 Kafin na fahimci harka, rayuwa ta yadda take a Gaskiya,
Muna rayuwa na Alkhairi bakin gwargwado, domin mun tashi a gaban malaman mu na tijjaniya, kuma alhamdulillahi na ta6a yin kwamandancin agaji karkashin tijjaniyya  kuma na dade gaskiya a ciki anan garin na kahutu

_Wakilinmu:-_ Akaramakallahu zamu so ka fadi mana sanadin (sila) fahimtarka wannan harkar?

*Alhaji magaji:-*  to,,  Alhmdulillah muna godiya ga allah da yasa muka fahimci wannan harkar muna tijjaniyya, kuma akan mana bayanai akan iyalan gidan manzon allah (saww), to sai dai ba buda mana abubuwan da muka fahimta a ita wannan gwagwarmayar  qarqashin jagorancin Mallam zakzaky H,
Kuma muna-nan-muna-nan dai ina port-harcourt  a taqaice dai.

Wata al'adace ta mutan arewa idan akace anyi azumi idan sallah ta zo, yakan yo gida, domin yayi sallah sannan ya gaida iyayensa da sauran yan uwa da abokan arxiki.
      Da yake mu muna kusa da zariya ne, mukan shigo zariya irin yawon sallah din nan,kuma a dai-dai wannan lokacin abinda na fahimta ga harka shine muzaharar qudus da akan yi ta duk juma'ar qarshen ramadan,
Mu mukan bi ne kawai ba mun san haqiqanin abinda ke tafiya bane.

Amma dai mukan bi aje ayi damu mu dawo, ana nan ana nan dai muka fahimci abinda ake nufi da ita harka din..

_Wakilinmu:-_ Wato dai idan na fahimta, muzahar qudus itace silar fahimtarka  wannan gwagwarmayar?

*Alhaji magaji:-* yauwa, ehh.

    Amma dai qarfin sanin harkar shine ina da wani malami a tijjaniya mai tsantseni, ba malamina bane amma dai gidan da nayi karatun allo a gidan yake, to mukan zauna dashi mu fahimci juna , har dai ta kawo wata rana muna magana akan  ita wannan harkar, har yake kawo mana maganar shehun kaulaha(sheikh ibrahim inyass).

   Nace dama muna da masaniya game dashi,
Duk da wannan lokacin ba ana kiran dariqar tijjaniyya da FAIRA ba, ana kiranta ne da dariqar TIJJANIYYA.


_Wakilinmu:-_ Yaya sunan malamin naku?

*Alhaji magaji*:-sunansa mallam sani kahutu shima a kahutu yake.

     Kuma allah da ikon sa sai ya karanta mana kitabul bushra,

Da ya karanta mana wannan littafin tabbas ina da shi littafin na kitabul bushra.

Sai nake cewa allah shi gafatta mallam ai wannan ibrahim din a  gaskiya ya bambanta da na kaulaha,
Domin ita kitabul bushra kace min tace za a haifi shi wannan mallamin a cikin garin zariya ba qauye ba, a cikin gari mai yawan rimaye.

To kaga ya sa6a da wancan ibrahim din da yake kaulaha.
Kuma mun san adatan zariya tana da yawan rimaye,
To anan dai yake cemin a yanxu dai a Africa ba wani ibrahim din sai ibrahim na kaulaha,
Sai nace to shima wannan ibrahim din ba mamaki zai fito, amma dai gaskiya akoi sa6ani.

          To, ana-nan-ana-nan sai na fahimci to ai sunan mai jagorantar wannan al'amari sunansa Ibrahim ,
To daga nan dai muka dan tattauna dashi har yake cemin ni gani na tashi a dariqar tijjaniyya kuma ina neman na koma wani guri,
Sai nake ce masa a'a ba ina neman na koma wani guri bane,ina son na fahimci gaskiya ne, in koma inda take.


   To Alhmdulillah dai bayan munyi wannan sai na qara fahimtar harkan da kuma shi jagoran da sunansa da ake fadi. Da kuma wancan abinda mallaman mu na tijjaniyya sukan dan bamu haske akan iyalan gidan manzon allah(saww), to sai na qara qarfafa dashi wananan jagora din.

  To Alhmdulillahi, ita kanta harka din anayi mata taqiyya sosai, don na dade a cikin garin mu (tunda ba zaune nake a cikin garin ba)ina harkar ba wanda ya sani.

To bayan na fahimci harkar sosai,

Ana nan wata rana sai da nayi qoqarin ganin cewa yan uwanmu(burazun garinmu) zasu zo ziyara wajen malam (zakzaky), sai na roqi qanina mai suna mansir (uwa daya uba daya) da yake kuma duk harka din ce muke ,

Sai nake ce masa yasan yadda yayi yazo da wannan malamin namu na tijjaniyya da ya nuna min kitabul bushra, domin yazo yasan mallam kuma ya fahimce shi.
  To alhamdulillahi mun sami nasara,
Qanina din sai ya dauki nauyin kudin motar sa da sauransu har zuwa zariya domin yazo yaga malam.

     Sai yake cemin shi ya rubuta tambayoyi guda ashirin da biyar da zai yi

Da muka shigo wajen ganawa da mallam, sai malam ya fara yi mana jawabi a taqaice,


Sai shi wannan malamin namu na tijjaniyya yaji ai mallam zakzaky ya bashi amsar duk abinda ya rubutu a takardar sa,har da wasu doriya akai,

Sai malamin namu na tijjaniyya sai ya fito waje ya tsaya yayi-zikiri-yayi-zikiri-yayi-zikiri sai da ya gaji.

Shi kuma malam zakzaky yana can ya gama jawabinsa har ma ya fara hira da mutane,

Sai ya shigo ya zauna sai yake cewa su mallam alhamdulillahi,
 Wato tambayoyi na rubuto har guda ashirin da biyar domin in yi maka, sai kuma allah yasa ban tambaya ba sai ka bani amsa har da qari.
Sakamakon wannan yasa na fita waje nayi zikiri domin nuna godiya ga Allah, sabida ban tambaya ba sai naji ka bani amsar abinda rubuto.

To, sai naji dadi sosai da wannan malamin namu har ziyarci kuma ya fahimci mallam din.

 Allah cikin ikon sa kuma bayan mun koma gida ba dauki dogon lokaci ba sai allah yayi masa rasuwa...

*_Mu hadu fitowa ta biyu_*

Daga Shafin nan Mai Farin jini ma'asumiya Nigeria news Updates

Haruna Shu'aibu Suleja

2 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post