Takaitaccen Tarihin Gwagwarmayar; ‘Malama Majiddah Abubakar’.
Kashi na Farko [ l ]
Sunana; H. Mai jeedda, sunan Mahaifina; Malam Abubakar, sunan Mahaifiyata; Amina Malam Abubakar. An haifeni a cikin garin Suleja, saidai Mahaifiyata ba haifaffiyar garin Suleja bace, hakama Mahaifina shima ba haifaffen garin Sujeja bane, yanayin tafiyar rayuwace Allah Ya nufi kasancewar Mahaifana a garin Suleja, har Allah Ya azurtasu da Iyali.
_______________________
Daga Shafin [M.N.N.U=MA'ASUMIYA]
_______________________
Nayi karatun primary da secondary a garin Suleja, hadi da karatun Addini a wata makarantar Islamiyya a kusa da unguwarmu(kamar yadda aka saba bisa al'ada). Na taso tare da Iyayena da sauran ‘yan uwana cikin rayuwa mai cike da farin ciki, sannan na sami kulawar rayuwa dai-dai gwargwado daga wajan Iyayena.
Na taso da shaukin karatun boko, kuma Alhamdulillah Allah Yayi min baiwar fahimtar karatu, da sanya min hannu a dukkanin al'amurana. Ta bangaren karatuna kuwa, Iyayena sun bani gudummawar su a bisa hakan, har lokacin dana kammala karatuna na gaba da firamare (secondary school).
Na fara fuskantar gwagwarmaya a cikin rayuwata ce, tun daga lokacin dana kammala karatuna na secondary. Dake Allah Ya nufi kasancewar Makarantar Fudiyya ta kasancene a kusa da gidan mu, hakan ya sanya nake samun daman ganin wasu daga cikin tarurrukan da ‘Yan Shi'a suke gabatarwa, tare da ganin hotunan Malamin su (Sayyid Zakzaky h.) da kuma samun daman sauraren wasu daga cikin jawabansa a lokacin da suke gabatar da tarurrukansu.
Bansan lokacin da zuciyata ta fara kamuwa da kaunar wannan Allah ba (Malam Zakzaky) a sanadiyyar makwaftaka da muyi da makarantar Almajiransa. Hakan ya sanya nake da kyakykyawar alaqa a tsakani na da Malamai da Daliban Makarantar. Hakan ya sanya har na fara sha'awar kasancewa Daliba a cikin makarantar.
Saidai kuma inada yakinin cewa kasancewata Daliba a wannan makaranta ba zai taba yiwuwa ba, sabida ba zan taba samun goyon baya wajan Iayayena ba, don kuwa basu da ra'ayin kiran Malam Zakzaky ko kadan a wannan lokaci. Amma dukda haka sai nayi karfin hali na fara zuwa makarantar a boye ina kai musu ziyara lokaci bayan lokaci, tare da tambaya akan dukkanin abinda ya shige min duhu dangane da abinda ya Shafi Malam Zakzaky da abinda yake kira a kai. Kuma cikin ikon Allah Malamin makarantar yana wayar min da kai ta hanyar bani amsoshin tambayoyina.
Ta haka na fara fahimtar Harka, a hankali kuma nayi zurfi a cikin kaunar Malam Zakzaky da goyawa Da'awar sa baya. Daga bisani sai ya zamana sun bukaci dana ke bada tawa gudummawar wajan koyar da Daliban makarantar da abinda Allah ya sanar da ni ta bangaren karatun boko. Dake lokacin ina matakin 'yar sakandire ce.
Haka ko akayi ina zuwa makarantar ina bada tawa gudummawar a sirrince duk ba tare da Iyayena sun san halin da ake ciki ba. A hankali bayan wani dan lokaci sai Soyayyah ta shiga tsakanina da Shugaban Makarantar ta Fudiyyah (Malam Adam) ba tare da masaniyar Iyayena ba don gudun abinda zai biyo baya idan suka san halin da ake ciki.
Kwatam! A kwana a tsahi sai al’amari ya bayyana ga Iyayena suka san halin dana fada na kasancewata ‘Yar Shi'a da kuma fadawa Soyayyah da Shugaban Makarantar ‘Yan Shi'a (Fudiyyar Unguwar mu).
Mai zai faru ?
Mu hadu a Kashi na biyu, don jin yadda al’amarin ya kasance tsakanin Hauwa'u da Iyayenta....
® Rubutawa: Abbakar Ibraheem Kudan.
Kukasance a shafin mu Na MA'ASUMIYA NIGERIA NEWS domin samun sahihan ilimumuka mabanbanta.
Tags:
Labari Na