HALIN DA QASATA TAKE CIKI!!!


Daga Shafin [M.N.N.U MA'ASUMIYA..]

Tare da Abdullahi M Ali Alpostaskumy✍🏻

Abinda yafaru a Jahar borno yabaiyana abubuwa da dama dangane da Lamarin tsaro aqasarmu Nigeria amma game Hankali da tunani.

Game da Zanga-zangar da mabpol (mobile police) sukayi a Jahar borno sun Gudanar da Zanga-zangar ne  maitake sai anbamu haqqinmu saboda Wasu dalilansu masu qarfi wadda kukaji kuma kuga ni.

Sun baiyana hakan Tareda nuna fushinsu game da lamarin dake faruwa akansu wadda gwamnatin take halin ko Inkula dashi suna qira ga gwamnatin Nigeria da ta gaggauta biyasu kudadensu da tariqe.

Bugu daqari sun baiyana cawa Yazama wajibi abiyamu haqqinmu domin musamu qarfin guiwa awajen tabbatar da tsaro a qasarmu Nigeria ba'a iyananbama hardama sauran Sassan qasarmu baki daya.

Sun Bayyana wannan qarara Ayadda suke cewa Lallai Sune Jami'an tsaro da suke rayuwa ajahah mafi Tsada ma'ana mafi hatsari daga cikin guraren da akafi yawaita tsaro aqasar sannan kuma suke aiki tuquru badare barana amman gwamnatin bata duba wannanba kudin da ake bamu mugudanar darayuwar tamuma wadda zaina debe mana kewa shima anhana anbarmu cikin qonci to baza mu yadda da wannan lamariba.
Wannan Shine koken Jami'an tsoron Jahar borno ga gwamnatin Nigeria.

Waishin kataba tambayar kanka game da lamarin tsaro a Nigeria maiyake haifar da matsalar? Ko kataba tambayar kanka meyake hana Jami'an tsaron Nijeriya zuwa wajen da ake buqatar su yayinda wani Abu yake faruwa nadaga fashi ko ta'addanci ko rikicin qabilanci?

Ya Dan Nigeria kataba tambayar kanka meyasa Jami'an tsoron Nigeria suke qin isa gurinda ake yin wani rikici? yayinda suka tabbata mutanen suna dauke da makamai sai an gama maharan har sungudu sannan kaga Sunzo dasaurinsu suna muku muzurai inkukai wasama sufuce akanku sudurar muku da wata suffa zasu rufe ido suyi wannan barnar ne ga raunana wadda baruwansu domin ace sunyi aiki dasunan dauki suka kawo wajen.

Yi tunani da tunaninka bada tunanin waninkaba duk irin wannan matsalar da muka kawo Abaya susuke haifarda duk wannan matsalar nan tarashin tsaro aqasar tamu.
ba'ana maganar Addini bane ko aqida a'a walau kai Dan shi'ane, izalah, ko dariqa, da salafiyya a'a muna maganar 'yancine ga 'yan qasa masu yanci game da haqqinsu awajen Mahukunta.

Munyi fira dawani Jami'in tsaro Alhalin baisanni Dan shi'a bane lokacin ina Nigeria yayinda yake baiyana takaicinsa ga yadda ake Musu halin ko inkula babban dalilin da yabayar shine yabaiyana abin dayasa Jami'an tsoron suke shakka Tareda fargaba ayayinda Aka Sanar dasu ana buqatar su awani wajen domin kwantar da tarzoma Dan kawo zaman lafiya awajen yayinda wani Abu yake faruwa musamman ma masu makamine awajen.

Dalilinsa da yabayar  saida yasa ni tausayinsa cikin Qanqanin lokaci
Dalilin nasa shine kamar haka dazar katafi Ankashe ka a wannan wajen to kaifa taka taqare shikenan iyalinka sunshiga wani hali damuwa musan manma irinmu wadda bamu kai wani mataki a aikinba in a bariki kake kaida iyalanka to za'a sallame Sune batareda wata kyakkyawar kulawaba harma a basu lokaci da rana sukwashe kayansu sufita daga barikin cikin Qanqanin lokacin. Wannan bawai a iya gwamnatin nan yake faruwa har gwamnatin baya da ta wuce.

Shikenan kaikagama Musu aiki maimakon gwamnatin tadau wani mataki maiqarfi akan hakan domin kaifa sadaukar da ranka kayi ga qasarka kabar iyalanka dakomai naka domin qasarka amman ranka sai yatafi abanza Lallai hakan bayyiba.

Duk wadda yake yankin borno, Yobe, Adamawa, Zamfara, Kaduna, da plateau wato yanki da ake rekice na babu gaira babu dalili yasan wannan batun Damuka kawo na rashin zuwan Jami'an tsoro gurin kwantar da tarzoma dawuri sai bayan komai yalafa.

Abdullahi M Ali Alpotaskumy

#FREEZAKZAKY
May Allah protect zakzaky

alpotaskumeey@gmail.com
Wed, 4 July 2018

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post