Abunda Yaja Hankali Na Nazama 'Dan Shi'a !!!

-inji Abdurazak Sani

Daga safin [M.N.N.U MA'ASUMIYA] a filinmu na Yadda na fahimci harkar slamiyya..

*Tare da wakilin mu Habib Rabiu Nasrallah.*


Da wayewar gari na duba agogo naga karfe 7:06Am na safe na tashi na nufi bandaki don nayi wanka daga bisani na yi sallar asuba, kasantuwar ya na yin gidan mu, mahaifin mu mutum ne wanda ya ke da wadata domin duk layin mu zan iya cewa babu me Rufin Assirin (kudi)  sa, wanda sam-sam abin da ake cewa kulawa da tarbiya musamman ta fuskacin addini musulunci gami da karatun addini sam sam a yanayin gidan mu basu dauke shi da wani muhimmanci ba, sabo da haka duk wani abu da ya shafi addinin musulinci ba mu dauke shi da muhimmanci.


Hakan ya sa lokuta da dama hatta sallar asubahi mahaifin mu baruwan sa ko mu tashi ko kar mutashi shi sam bai da muba.

Duk da irin wannan rashin kulawa na abin da ya shafi  addini musulumci.
An zuba mana kiyayyar shi'a a zukatan mu, muna kallan cewar gwara yahudawa da su, wanda ko a hanya idan mun fita yawo musaman hanya tabiyomu da mu a lokacin da suke gudanar da taro ba mu da wata maganar kir ki sai tsinuwa da zagi aibatawa ko kadan a rayiwata bana kaunar dan shi'a ko kadan hakama me gidan mu mutum ne me tsananin gaba shi'a wanda sanadiyar haka yawan sauraran lakcar wata kungiya wanda ako da yaushe basu da wani aiki sai zagin musulmai musamman wanda ba fahimatar su daya ba,

duk da cewa ni ne babba a gidan mu.
A wasu lokutan bamu da wani abu da zarar gari yawaye hatta makarantar bokon da maifinmu ke mutukar san yaga mun yi tazamo mana tamkar kai ka ce wanda ake Azabtawa a ko yaushe a duk lokacin da naga ranar akwai makaranta. Tare da cewar duk ranar da akwai makaranta da wuri ake tashin driven gidan mu shi ke daukar mu dan ya kai mu makaranta, lokuta masu yawan gaske da zarar an kai mu makaranta To bamu da wani abu face mugudu daga makaranta muje muyi shaye shaye dani da sauran abokan mu, tun ba'a fara ganewa a gidan mu ba har takai a gidan mu an fara fahimtar irin abubuwan da na ke aikatawa, kusan duk gidan mu zan iya cewa me dama-dama a gidan mu ita ce kan war mu, wanda ita kanta ta na abin da taga da sakamakon yadda aka shagwabamu ni kuwa da sauran kanne na maza ba'acewa komai akan mu,  domin duk inda ka kai da rashin kunya dadai sauransu ba'acewa komai,  mahaifin mu ya yi duk abin da zaiyi don ganin mu kintsu muzamo nagari amma da ya ke shirya ta allah ce,  duk da cewa ni kai na ba na san irin abin da nake aikatawa.

Akwana a tashi har lokacin da zamu zana jarrabawar karshe ta fita daga secondry sch, wanda mahaifin mu ya yi iyakar ko karin sa dan yaga mun sami nasarar cin jarrabawa domin a rayuwar sa bashi da wani buri face muga mun tsaya mun yi karatun boko.

Ba zan taba mantawa ba akwai a wani ajin mu shima dan gidan attajirine sosan gaske amman duk inda ake neman kamilin mutum, me kwarjini da mayar da hankali akan karatu zan iya cewa babu kamar sa duk ajin mu, wanda kusan duk term shi ke daukar na daya tun daga sss 1 A gaskiyar magana dan nan ya na birgeni Ana kiran sa da suna jawad amman duk tsawan lokacin da muka dauka da shi a aji ban taba sanin da cewar shi shi'a ba ne,  duk da yake idan kaga muna zuwa wajan sa to jarrabawa ta matso,  a wasu lokutan nakan ce ya tani da addua wlh abin da na ke ba'asan rai na ba, ya yi murmushi ya ce dani abdul inshaAllah wata rana zakazamo abin alfahari a gidan ku. Akwana a tashi a mafi yawan lokuta idan aka zauna hira shi da yake mutum ne wanda magana bata da meshi ba, duk da ya ke mu addini bai damebu ba ko kadan dazarar an fara musun qungiyoyin addini a ajin mu ko idan mun fito break zaka sha mamaki muamman yadda mu ke tsanan tawa da zagi da cin mutumci akan shi'a abin zai baka mamaki,  amman duk da haka shi jawad ko daya bazakata ba ji yasa baki ba, wanda ace shi dan shia ne tsawan lokaci ba mu saniva.

Sai lokacin da mu ke zana jarrabawar karshe, a lokacin nakan same shi nace a ya ta yani da addua ya ce ina yi maka abokina, a daidai wannan lokacin na ce da shi dan Allah ko kana da wani wa'azi ka turamin? Ya yi shiru na wasu dakika sannan ya ce da ni itom da yake yawan ci duk wa'azizzikan da suke wayata na kwashe su na xuba a computer kasan da ya ke ban cika zuwa da waya makaranta ba,  a ce amman na tuna ina da wani wa'azi kwaya daya da yarage ga wayar ka tura in yaso ka bani,  a lokacin wannan wazin a ashe karatun sayyid zakzaky ne wanda ya ke karanta hadith na salmanil farisi (R) wanda bayan na tura ban saurari karatun ba sai bayan na koma gida na fara saurara,  wanda wannan hadith yasa naji gabadaya shaawaice sha'waice duniya ga badaya ya fitar min daga rai,  wanda a ranar bacci ban yi shi cikin dadin raiba sabo da yadda na tsorata musamman naji yadda ake bayani akan Lahira wanda bayan kammalawata sai da na yi sallolin da ake bina harda nafilla domin yadda na firgita amman a lokacin na kasa gane wanne malami ne.
   _______________
Zan cigaba inshaAllah.
_____________

Shin wannan yaron tayaya zai gane wane malamine Wannan ya Saurara??


Idan yagano ya zata kasance dashi tunda ga Yadda Akidar gidansu take??

Muhadu a Inda Al'amarin ya Girmama a Fitowa ta biyu


Kamar zai koma Shi'a, idan yagano ya zata kasance tsakanin su da babanshi??

Kubiyomu cikin na biyu (!!) Domin jin amsoshinku

Daga shafin Ma'asumiya Nigeria news Updates

By Habib Rabiu Nasrallah.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post