ZUWA GA HARISAWAN HARKA.!!


Sadar Yusuf Kano.


Bayan gaisuwar ban girma da jinjinawa tare da neman iso gami da lale marhaban daga gareku yaku manyan bayin Allah, Ina neman alfarmar ku bani aron 'yan mintoci daga cikin lokacin ku na wannan rana domin ku saurara me wannan karamin kane naku ke shirin hakaitar muku.

Na taba fira da wani haris, a cikin firar nake masa tambaya nace yanzu misali ace ana muzahara sai ka hango wani ko wata kuma baka yadda dashi ba ma'ana kana tsammanin ko yazo da kayan fashewa ne kuma ya tunkaro muzaharar kai tsaye a matsayin ka na haris da kake duty a gurin me zakayi? Haris din yayi murmushi yace min mal sadar ai a yadda aka koya mana shine kurum zan tunkari wannan bako ne da niyyar koma menene a tare dashi ya karata iya ni dashi kada dai in bari ya karaso cikin 'yan uwa, ma'ana idan ma abin fashewa ne ya karata iya ni na cika aikina kenan.

Allah sarki kunji irin sadaukarwar da ake koya ma harisawa kuma a kan haka suke ayyukansu.
https://maasumiya.blogspot.coml
Magana ta biyu ni shaida ne na shaidi harisawa da tsananin ibada kama daga raya darare da sauran su domin nasan mafi yawancin program mai zafi wanda ake tsammanin waqi'a zaka taras harisawa wadanda zasu duty suna shiga halwar kwanaki ne daga fitowar su su wuce program kaga a kwai tsarkin ruhi a lokacin saboda haka komi yazo za'a rungume ko da shahada ce kuwa, wannan kenan.

Ka ture ta janibin riyadha wannan shiru ake domin nasan harisawan da sukayi gudu a kafa na fiye da kilomitoci barkatai har wasu ma na faduwa a hanya amma basu sare ba, jarumta da rashin tsoro ba za'a gaya ma harisawan mu ba, wannan ina fada kuma ba don ganin ido ba kowa ya sani haka ne, Ta janibin sallamawa harka rayuwa dungurum ko nasan har wata sara aka shigo da ita cikin sistoci wai su basu son haris saboda kullum yana wajen duty shi zasu aura ko duty? ko ba haka kuka ta fadi ba sistoci?, haka kuka dinga cewa, amma hakan bai sare gwuiwar harisawan mu ba, A kwai ranar da naje markaz kofar waika nayi dare kusan karfe daya na dare sannan na kama hanyar gida gashi ana wani mugun sanyi dai dai kwana na taras da harisawa sun kunna wuta rakabe jikin katanga wallahi kwallah ta kusan kufce min saboda lokacin sanyin da akeyi in dai ba cikin wutar za'a cilla ka ba to wallahi zaka dandana kaji, gashi ni zan koma gida in shiga bargo suko gasu a nan zasu kwana bayin Allah kenan.

Hmm idan abin in ta bayani ne misalan baza su kare ba....... Daaa kenan, amma yanzu abinda na kasa ganewa, a yanzu  kullum nake nazari kaina ke daukar chaji shine yanzu me ya kawo naji har ana gwaba ma harisawa magana wai suna dan nokewa shiga abuja struggles?

Ayi hakuri amma wajen aka zo kuma idan aka lura da kyau za'a gane hakan ba mu ce harisawa basa zuwa abuja struggle ba, a'a lallai suna zuwa amma in aka kwatanta da yawansu da kuma tasiri gami da tsarin su a harka islamiyya gaskiya ya kamata ace sun dauki wani kaso mai gwabi a cikin lamarin nan, idan basu ja gaban abuja struggle ba ya kamata ace dasu ake jan ragamar al'amarin.

Kodashike nasan kuna da tsare tsaren ku kuma haka ake so amma tsarin ya kamata yayi amfani ne wajen ci gaban abuja struggle, idan zamuyi kira tom zamuyi kira da salimar zuciya ga kwamandojin harisawa cewa abuja fah na fama da kishirwar harisawa, a kwai bukatar azo a mana irin rawar 'yan mazan nan da akeyi a nisfu, a kwai bukatar abuja ta girgiza tunda a kwai 'ya 'yan malam zakzaky H watau harisawa kuma nasan shirye suke su yi duk mai yiwuwa wajen ganin 'yancin jagora ya samu koda hakan na nufin zubar jinainan su a falalin kwaltar garin abuja ne.

Tunda aka kama jagora ake ta fafutuka, jagora fa ba wadatacciyar lafiya ta ke tare dasu ba, ga ciwuka da dama da radadi zogi na addabar jagora don rashin tausayi har matsa ma jagora kafar sa mai masa ciwo suke, ga ciwon hakori ga bullet jikinsa shida umma zeenat, gashi dungurum burinsu su raba mu dashi.
Ma'asumiya Nigeria news updatel
Yanzu zamani ya shuda azzalumai sun toge wasu 'yan uwan sun noke wasu 'yan uwan kuma sun dage ku kuwa harisawa ya kamata a zage, ku bama azzalumai citta ne ku fito ku nuna 'ya'yan malam zakzaky H kuke, ace a kwai wani tsari na duty duty da zai bada dama.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post