Jama’a barkanku da wannan lokaci, barkanku da Bukukuwan Sallah da saduwa da mu a cikin wannan Rubutu namu, a inda zamu yi muku bayani akan hanyoyin da zaku bi domin gano inda wayarku take a lokacin da ta bace ko a aka sace ko kuma ka manta inda ka ajiye ta. A wannan Rubutu, za mu yi Magana ne akan wayar Android.
Sanin kowa dai ne sau da yawa mutum yakan rasa wayarsa ta hanyar sacewa, yadawa ko kuma manta inda aka ajiye wayar. Sai ka ga yana ta faman nema, idan ma sace wayar aka yi ko kuma ya yada to a mafi yawancin lokaci shi da ganin wannan wayar har abada. Wasu lokutan kuma mutum zaya iya sanya wayarsa a silent kuma ya manta inda ya ajiye ta ka ga kenan ko da an kirawo wayar ba zaka ji tayi kara ba.
Domin war-ware muku da wannan matsalar, mun kawo wasu hanyoyi ko kuma matakai saukaka da zaku dauka domin lalubo inda wayarku take, ko da kuwa saceta aka yi.
Kafin ka iya gano inda waya take, a dole ne kafin wayar ta bace ko kuma a lokacin da ke a wajen ya zamto ko dai ace kayi amfani da wani application wanda ke ajiye wasu bayanai da za’a iya amfani da su domin gano inda wayar take, ko kuma kayi amfani da wani tsari da ake cema “Device Manager” wanda Google yake samarwa.
Su dai wadannan application zaka iya saminsu a Google Play store, kuma suna da matukar saukin amfani. Misalan wadannan application din sun hada da Family Locator, Cerberus, Prey Anti-theft, Where’s My Droid da dai sauransu.
https://maasumiya.blogspot.com
Shi kuma wanda Google suke samarwa wato “Device Manager”, yana da matukar saukin amfani. Domin yin amfani da wannan tsari sai ka ziyarci website dinsu a
www.google.com/android/devicemanager. Abinda kawai kake bukatar yi anan shine kawai kayi amfani da account dinka na google wato Gmail domin yin login. Da zaran kayi login shi ke nan, google din zayayi searching din bayanan wayarka sai ya ajiye su. A duk lokacin da ka bukaci wayarka to sai ka shiga wannna website din, zaka ga sunan wayar da kuma Map din inda wayar take. Akwai wasu zabuka da za’a baka. Na farko shine “ring”. Idan ka danna wannan malatsin wayarka zata kama yin ringin ya na tsawon minti biyar ba tare da ta tsaya ba. Zabi na gaba ku a zaya baka dama kodai ka kasha wayar ko kuma ka goge abin da ke cikinta gaba daya.
Wadannan sune hanyoyi da zaku iya bi domin yin tracking din wayarku a lokacin da kuma yadda ta, ko aka sace ko kuma kuka manta da inda kuka ajiye ta.
Idan kana bukatar tofa albarkacin bakinka game da wannan kasidar, ko kuma kana da wata tambaya to karka yi wata-wata kayi comment a nan kasa. Ga duk mai bukatar samun kasidunmu ta hanyar Whatsapp shima ya iya yin comment da lambarshi.
Mas'udu Dan Masani Shinkafi 08149993999
Tags:
Yanar gizo