Facebook dai sanin kowa ne kafa ce babba ta sada zumunta tsakanin mutanen duniya baki daya wacce tafi da ko wace irin kafa.
Facebook kuma itace kafa ta sadarwa da tafi ko wace kafa karbuwa a duniya baki daya, ba don komai ba sai don yadda a koda yaushe facebook din ke samar da wasu tsare-tsare da ke saukaka yanda mutane zasu iya saduwa tsakaninsu tare da isar da sako cikin hanyar mai sauki.
Sanin kowa ne akwai hanyoyi da dama na kafar facebook da mutane ke amfani da su wajen isar da wani sako. Wadannan hanyoyi sun hada da chattinh, message, status, foto, video, note, audio, da dai sauransu, a inda zaka ga mutum daya na iya uploading daruruwan fotuna, videos, da dai sauransu. Wani kuma chatting ne abin da yafi yi a saman facebook, a yayin da wani kuma karanta update da kuma comment shine abin da yafi aiwatarwa a facebook.
Ko ma dai minene kafi yi a dandalin facebook, a cikin wannan kasida mun kawo muku bayani akan yadda zaku iya duba duk wani abu da kayi a dandalin facebook tun daga ranar da ka bude facebook ya zuwa yanzu.
Ma'asumiya Nigeria news update
Idan kana bukatar duba tarihin abubuwan da ka aikata a saman dandalin facebook, sai ka bi wadannan matakan kamar haka:
1. Ka shiga kayi login da account dinka na facebook 2. Bayan ka yi login sai ka shiga wajen profile naka 3. Sai ka duba daga bangaren dama, akwai inda za ka an sanya “Activity Logs”, sai ka shiga nan
Da ka shiga cikin wannan “Activity Logs” za ka ga list na duk abubuwan da kayi a wannan sati.
Idan ka matsa a kasa za ka ga inda aka sanya “This month” , idan ka shiga nan, to zaka ga duk wani abin da ka aikata a wannan watan. A kasan “This month” za ka ga iya jerin shekarun da kayi a facebook. Sai ka shiga ko wace shekara kake bukata.
Mas'udu Dan Masani Shinkafi 08149993999
Idan ka bukata kuma zaka iya zabar abubuwan da kake bukatar gani (misali fotuna kadai, videos, ko comments) ta hanyar shiga inda aka sanya “filter” daga saman page. Daga nan zaka iya zabar abin da kake bukatar ganin tarihinsa.
Tags:
Yanar gizo
Maasumiya news update Allah Yakara maku Fasaha da basira alfarman Nana Fatima,free azzazzaki
ReplyDelete