SUNAN DA IMAM ALI YAFI SO AKIRASHI DASHI (ABU TURAB)



*MA'ASUMIYA NIGERIA NEWS UPDATES*

Daga cikin sunayen da ake kiran Imam Ali (A.S) da su akwai wannan suna ABU TURAB. Da yawa daga mabiyansa na wannan zamani sun san shi da wannan suna, sai dai da za ka tambaye su ta ina ya sami wannan suna, kuma menene dalili? Tabbas, ba za ka sami amsa daga mafi yawansu ba.
SANIN DALILIN NA DA MUHIMMANCI GARE KA
Bukhari ya ce, Abdullahi Bn Maslamata ya bamu labari, Abdul-Azeez Bn Abiy Hazeem ya bamu labari, daga babansa cewa, wani mutum ya zo wajen Sahal Bn Sa'ad sai yace;
" Wannan wani mutum ne daga shugabannin Madinah, yana kiran Aliyu (da wani irin suna) akan Mimbari ."
(Sahal) yace, " Me ya ke fada ?"
Yace, " Ai yana cewa ne ABU TURAB ." Sai (Sahal) yayi dariya sannan yace;
" Wallahi ba wani ne ya sanya masa wannan suna ba face Manzon Allah (S.A.W.W), kuma babu wani suna da ya fi soyuwa gare shi daga wannan ."
Sai hankalinsa ya kada zuwa ga wannan zance na Sahal, sai yace, " Yaa baban Abbas, to, ya hakan ta kasance ?"
Sai yace, " Aliyu ya shiga wajen Fatima, sai ya fito ya kishingida a masallaci (har bacci ya kama shi). Sai Annabi (S.A.W.W) ya cewa Fatima (S.A), " INA 'DAN BAFFAN KI ?"
Sai tace, " YANA MASALLACI ."
Sai ya fita zuwa gare shi ya tarar (da shi) mayafinsa ya fadi daga bayansa, qasa ta zuba a gadon bayansa. Sai ya riqa share wannan qasa da ke jikinsa (da hannayensa masu albarka) yana cewa,
" ZAUNA YAA ABU TURAB !" Sau biyu.
(Bukhari, Kitabul-Fadha'ilul As'habun-Nabiyyi (S.A.W.W), babin falalar Ali Bn Abiy 'Dalib, hadisi me lamba 3703).
Daga wakikanmu na Zone din Bauchi, Gombe da Adamawa.
Tare da (Ado Isah Guda).
08137925034/08126385470
👇👇👇
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=195938557806038&id=16080874

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post