SAHABIYA UMMU AIMANA (RA)


   IS'HAQ MOHD KIBIYA



Ummu Aiman (RA) Sahabiya Ce, Kuma Dattijuwa Ce, A Shekaru Ma Har Ta Girmin Manzon Allah (S).

Ita Baiwa Ce Ga Baffan Manzon Allah (S) Sayyadina Abudalib (AS), Ta Kasance Ita Take Lura Da Annabi (S) A Lokacin Da Yake Karami, A Yayin Tana Budurwa Ita Kuma.

Ta Kasance Daga Cikin Wadanda Suka Yi Imani A Farkon Wannan Addinin. Kuma Da Ita Aka Yi Hijiran Farko Zuwa Habasha.

Ta Kasance Tare Da Annabi (S) Tun Yarintarsa Har Ya Girma, Har Akai Masa Wahayi, Har Aka Kore Shi Zuwa Madinatul Munawwara,
Ta Na Daya Daga Cikin Rundunar Fadimomin Da AmirulMuminin Ali (AS) Ya Yo Hijira Da Su Zuwa Madina Da Tsakar Rana!

Ta Zama Amintacciyar Manzon Allah (S), Kuma Babba Daga Cikin Masu Yi Masa Hidima

Ta Samu Shaida Daban-Daban Daga Annabi (S) Da Ahlul-Bait (AS) Na Alkairi.
https://maasumiya.blogspot.com/2018

Kuma Har Bayan Wafatin Annabi (S) Ta Kasance Mai Hidimawa Fatima (SA) Duk Da Kasancewar A Haife Ta Yi Jika Da Fatima (SA) Din.
*** Amma Abin Takaici:

Yayin Da Sayyida Fatima (SA) Ta Nemi Sarkin.... Ya Bata Gonarta Da Ya Kwace: Sai Yace Ba Nata Bane.
In Gado Ne, Ba'a Gadon Annabi (S) Inji Sarkin.

Tace Masa Ai Nata Ne, Annabi (S) Ya Bata Tun Yana Raye. Sai Yace Ta Kawo Shaidu Akan Hakan.
Sai Ta Kawo Hasan Da Husaini (AS). Shugabannin Samarin Gidan Aljanna Inji Annabi Muhammad (S).

Sai Halifa Yace Ba Za'a Karbi Shaidar 'Ya'ya Akan Uwarsu Ba!
Sai Ta Kawo Mijinta Ali Bin Abidalib (AS), Shugaban Muminai, Kuma Mai Raba Aljanna, Wanda Yake Tare Da Gaskiya, Kuma Gaskiya Take Tare Da Shi.

Al-Qur'ani Mai Furuci. Siddiq Mafi Girma Wanda Ba Wani Siddiq Baya Ga Shi A Wannan Al'ummar In Ba Makaryaci Ba! Inji Shi (AS).

Sai Halifa Yace; Ai Ba Zai Yiwu Miji Ya Yi Ma Matarsa Shaida Ba! Ba Za'a Karbi Shaidar Ali (AS) Akan 'Yar Annabi (S) Ba!

Sai Akace Fatima (SA) Ta Kawo Wani Shaidar Dai.....

Nan Ta Kira UMMU AIMAN (RA) A Kan Ta Mata Shaidar Cewa GONAR FADAK Ta Ta Ce, Annabi (S) Ya Mallaka Mata.

Da Ummu Aiman (RA) Ta Zo Fadan Mai Martaba, Sai Tace Musu Kafin Na Bada Shaida Akan 'Yar Manzon Allah (S), Ina Son Ku Fara Bada Shaida Akaina, Ko Kun Taba Jin Annabi (S) Yace Wani Abu Dangane Da Ni?

Sai Wani A Cikin Fadawa Yace: "Eh Wallahi! Naji Da Kunnina Manzon Allah (S) Ya Ce Ke (Ummu Aiman) 'Yar Aljanna Ce..."

Sai Tace: Allah Ka Shaida. Sannan Tace Musu: "Wallahi Summa Tallahi, Billahillazi La'ilaha Illa Huwa... Annabi Muhammad (S) Ya Mallakawa 'YarSa Fatima AzZahara (SA) Wannan Gonar Ta Fadak A Lokacin Da Jibrilu Ya Saukar Masa Da Ayar Da Ke Cewa; 'Kuma Ku Ba Makusanta Hakkinsu'......."

Kun San Me Fada Suka Ce Mata?
Ba Za'a Karbi Shaidar Ta Ba, Saboda Ita Ba'Kar Fata Ce. Ita Ba Balarabiya Bace. Wai Bata Iya Larabci Ba.

Ta Fa Girme Su Duk Cikansu! Kuma Ta Riga Duk Cikansu Musulunta! Kai Bata Ma Taba Bautama Gunki Ba Ita, Balle Ta Bizne 'Yarta Da Ranta A Jahiliyya.

Kuma Duk Sunyi Wayau Sun Santa A Babbanta Ne A Kasar Larabawa.
Amma Saboda Tsabaragen Raini, Suka Ce Ita Bata Iya Larabci Ba, Ita Bakar Fata Ce. Suka Ki Karbar Shaidarta Bisa Wannan Dalilin.

Sai Wani A Cikin Fadawan Yace: "To Ma Ai Ita 'Yar Gidansu Ne. Ya Za'ai A Karbi Shaidar Hadima Ga Uwargijiyarta?" Nace Kaico!
'Yar Gidansu Wa? Gidan Fatima (SA)? Gidan Annabi (S)? Kai Kuma Dan Gidan Babanka Ne Ko?

Da Gidan Babanka Da Gidan Baban Su Fatima (SA) Wanne Ya Fi?

ALLAH KA KARA YARDA GA SAYYADA UMMU AIMAN (RA).
KA KARA NARKON AZABA GA DUK WANDA YA ZALUNCI ' YAR ANNABINKA (S).
.

Sa Hannu:Mas'udu Dan Masani Shinkafi 08149993999

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post