ME YA SA KHALIFA USMAN IBN AFFAN ZAI SOKE WAJABCIN SALLAR JUMU'A A RANAR IDI (SALLAH); ALHALI HAR ANNABI MUHAMMAD(SAW) YAYI WAFATI YANA YIN SALLAR JUMU'A DA IDI KODA SUN HADU A RANA DAYA???
DAGA IS'HAQ MOHD KIBIYA
SALLAR JUMU'A WAJIBI CE; MATUKAR TA CIKA SHARUDDAN WAJABCINTA. DUKKAN MALAMAN MUSULUNCI SUN YARDA DA CEWA; AKWAI SHARUDAN DA SAI SUN CIKA SANNAN SALLAR JUMU'A TAKE WAJABA, KUMA WADANNAN SHARUDAN SUN DANGANTA DA MAZHABA, YANAYI DA KUMA MUTUM. MISALI, DUKKAN MAZHABOBIN MUSULUNCI SUN HADU AKAN CEWA; SALLAR JUMU'A BATA WAJABA GA; MACE, MARAR LAFIYA, YARO, MATAFIYI... A WASU MAZHABOBIN KUMA SALLAR JUMU'A WAJIBI CE 'YAR ZABI (TSAKANIN YINTA DA YIN AZAHAR) A LOKACIN DA AKA RASA IMAM. IDAN HAR SHARUDDAN WAJABCIN SALLAR JUMU'A BASU CIKA BA; TO DOLE NE MUTUM YAYI SALLAR AZAHAR A MADADINTA.
Allah(swt) yana cewa;
"يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا نُودِيَ لِلصَّلَاةِ مِن يَوْمِ الْجُمُعَةِ فَاسْعَوْا إِلَىٰ ذِكْرِ اللَّهِ وَذَرُوا الْبَيْعَ ۚ...".
(Q : 62 : 9).
"Ya ku masu imani, idan an kira sallah a ranar Jumu'a; to kuyi hanzarin zuwaga ambaton Allah (Sallar Jumu'a)...".
Sai dai ba kowa ne umarni ne a Qur'an yake mudulaki (sakiwawai) ba. Akwai ayoyin Qur'ani masu zuwa da umarni, amma sai a samu wasu ayoyin Qur'ani, ingantattun hadisai ko fahimtar malaman Musulunci su kayyade umarnin da wasu sharudu, misali, fadin Allah cewa:
"وَأَقِيمُوا الصَّلَاةَ وَآتُوا الزَّكَاةَ وَارْكَعُوا مَعَ الرَّاكِعِينَ".
[Q : 2. Al-Baqara : 43].
"Ku ke yin Sallah, ku bada Zakkah, kuyi Ruku'u tare da masu Ruku'u".
Idan muka ce umarnin Allah a wannan ayar mudulaki ne; ba tare da wani sharadi ko kaidi ba, kenan dole ne kowa yayi Sallah? Kenan ba'a daukewa mai Haila da Nifasi, Mahaukaci... sallah ba? Doriya akan cewa ayar kawai cewa tayi mu yi Sallah; amma bata fada mana wace sallah ba, ta farilla ko nafila, ta Idi ko ta Jumu'a?... Kenan dole ne kowa sai ya bada Zakka? Kenan kowace Sallah har Nafila wajibice a jam'i?...
Amma idan muka koma zuwaga wasu ayoyin Qur'ani, ingantattun hadisai da fahimtar malaman Fiqhu; sai mu fahimci sharadai da kaidin da ke cikin umarnin Allah da ya zo a wannan ayar. Irin wannan misalin akwai shi da yawa a Qur'ani da ma wasu hadisai ingantattu.
Ibn Kasir (babban malamin Ahlus-sunnah) a karkashin tafsirin ayar da ta wajabta sallar Jumu'a yana cewa:
"ﻭﺇﻧﻤﺎ ﻳﺆﻣﺮ ﺑﺤﻀﻮﺭ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﺍﻟﺮﺟﺎﻝ ﺍﻷﺣﺮﺍﺭ ﺩﻭﻥ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ، ﻭﺍﻟﻌﺒﻴﺪ، ﻭﺍﻟﺼﺒﻴﺎﻥ ﻭﻳﻌﺬﺭ ﺍﻟﻤﺴﺎﻓﺮ، ﻭﺍﻟﻤﺮﻳﺾ، ﻭﻗﻴﻢ ﺍﻟﻤﺮﻳﺾ، ﻭﻣﺎ ﺃﺷﺒﻪ ﺫﻟﻚ ﻣﻦ ﺍﻷﻋﺬﺍﺭ، ﻛﻤﺎ ﻫﻮ ﻣﻘﺮﺭ ﻓﻲ ﻛﺘﺐ ﺍﻟﻔﺮﻭﻉ...".
"Sallar Jumu'a bata wajaba ga mata, bayi, yara, matafiyi, marar lafiya, da mai kula da marar lafiya... mai bukatar cikakken bayani zai iya komawa littafan Fiqhu".
- ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺍﺑﻦ ﻛﺜﻴﺮ : ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ : آية 9 : ﺩﺍﺭ ﻃﻴﺒﺔ : ﺳﻨﺔ ﺍﻟﻨﺸﺮ 1422 : ﻫـ / 2002 ﻡ : ﻋﺪﺩ ﺍﻷﺟﺰﺍﺀ : ﺛﻤﺎﻧﻴﺔ ﺃﺟﺰﺍﺀ.
Kenan Ibn Kasir ya nuna karara cewa; lallai don bukatar samun cikakken bayani akan sharadan wajabcin sallar Jumu'a, to muna da bukatar malaman Fiqhu.
Qurdabi (fitaccen malamin Ahlus-sunnah) yana cewa:
"ﻗﻮﻟﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ: 'ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺁﻣﻨﻮﺍ' ﺧﻄﺎﺏ ﻟﻠﻤﻜﻠﻔﻴﻦ ﺑﺈﺟﻤﺎﻉ. ﻭﻳﺨﺮﺝ ﻣﻨﻪ ﺍﻟﻤﺮﺿﻰ... ﻭﺍﻟﻤﺴﺎﻓﺮﻭﻥ ﻭﺍﻟﻌﺒﻴﺪ ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﺑﺎﻟﺪﻟﻴﻞ، ﻭﺍﻟﻌﻤﻴﺎﻥ ﻭﺍﻟﺸﻴﺦ ﺍﻟﺬﻱ ﻻ ﻳﻤﺸﻲ ﺇﻻ ﺑﻘﺎﺋﺪ ﻋﻨﺪ ﺃﺑﻲ ﺣﻨﻴﻔﺔ. ﺭﻭﻯ ﺃﺑﻮ ﺍﻟﺰﺑﻴﺮ ﻋﻦ ﺟﺎﺑﺮ ﺃﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ(ص) ﻗﺎﻝ: "ﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﻳﺆﻣﻦ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﻭﺍﻟﻴﻮﻡ ﺍﻵﺧﺮ ﻓﻌﻠﻴﻪ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﺇﻻ ﻣﺮﻳﺾ ﺃﻭ ﻣﺴﺎﻓﺮ ﺃﻭ ﺍﻣﺮﺃﺓ ﺃﻭ ﺻﺒﻲ ﺃﻭ ﻣﻤﻠﻮﻙ..." ﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺪﺍﺭﻗﻄﻨﻲ. ﻭﻗﺎﻝ ﻋﻠﻤﺎﺅنا(ر) ﻭﻻ ﻳﺘﺨﻠﻒ ﺃﺣﺪ ﻋﻦ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﻣﻤﻦ ﻋﻠﻴﻪ ﺇﺗﻴﺎﻧﻬﺎ ﺇﻻ ﺑﻌﺬﺭ ﻻ ﻳﻤﻜﻨﻪ ﻣﻨﻪ ﺍﻹﺗﻴﺎﻥ ﺇﻟﻴﻬﺎ؛ ﻣﺜﻞ ﺍﻟﻤﺮﺽ ﺍﻟﺤﺎﺑﺲ، ﺃﻭ ﺧﻮﻑ ﺍﻟﺰﻳﺎﺩﺓ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺮﺽ، ﺃﻭ ﺧﻮﻑ ﺟﻮﺭ ﺍﻟﺴﻠﻄﺎﻥ ﻋﻠﻴﻪ ﻓﻲ ﻣﺎﻝ ﺃﻭ ﺑﺪﻥ... ﻭﺍﻟﻤﻄﺮ ﺍﻟﻮﺍﺑﻞ ﻣﻊ ﺍﻟﻮﺣﻞ ﻋﺬﺭ ﺇﻥ ﻟﻢ ﻳﻨﻘﻄﻊ. ﻭﻟﻢ ﻳﺮﻩ ﻣﺎﻟﻚ ﻋﺬﺭﺍ ﻟﻪ...".
"Wajabcin sallar Jumu'a ya kan mukallafi ne banda karamin yaro, marar lafiya, matafiyi, bayi, mata, makaho da tsohon da baya iya tafiya sai da jagoran (a mazhabar hanafiyya). Abu Al-zubair ya ruwaito daga Jabir, Annabi(saw) yana ce; sallar Jumu'a wajibici ga duk wanda yayi imani, amma banda marar lafiya, matafiyi, mace, yaro, bawa... Darul-Qutni ne ya ruwaito wannan hadisin. Sannan wasu malanmu sun kara da ce; halartar sallar Jumu'a wajibi ne ga wanda bai da wani uzuri; kamar rashin lafiya, tsoron karuwar rashin lafiya, jin tsoron wani azzalumin sarki da zai iya cutar dashi ko dukiyarsa, mamakon ruwan saman (amma a Malikiyya ba uzuri ba ne)..."
- ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺍﻟﻘﺮﻃﺒﻲ (ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﻷﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ) : ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ : آية 9 : ﺩﺍﺭ ﺍﻟﻔﻜﺮ : ﻋﺪﺩ ﺍﻷﺟﺰﺍﺀ : ﻋﺸﺮﻭﻥ ﺟﺰﺀﺍ.
Jarullah Zamkhashari (sanannen malamin Ahlus-sunnah a fagen Tafsiri) yana cewa:
"ﻭﻻ ﺗﻘﺎﻡ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﻋﻨﺪ ﺃﺑﻲ ﺣﻨﻴﻔﺔ(ر) ﺇﻻ ﻓﻲ ﻣﺼﺮ ﺟﺎﻣﻊ، ...ﺍﻟﻤﺼﺮ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ : ﻣﺎ ﺃﻗﻴﻤﺖ ﻓﻴﻪ ﺍﻟﺤﺪﻭﺩ ﻭﻧﻔﺬﺕ ﻓﻴﻪ ﺍﻷﺣﻜﺎﻡ، ﻭﻣﻦ ﺷﺮﻭﻃﻬﺎ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺃﻭ ﻣﻦ ﻳﻘﻮﻡ ﻣﻘﺎﻣﻪ، ...ﻭﻗﻮﻟﻪ(ص): "ﺃﺭﺑﻊ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻮﻻﺓ : ﺍﻟﻔﻲﺀ، ﻭﺍﻟﺼﺪﻗﺎﺕ، ﻭﺍﻟﺤﺪﻭﺩ، ﻭﺍﻟﺠﻤﻌﺎﺕ" ﻓﺈﻥ ﺃﻡ ﺭﺟﻞ ﺑﻐﻴﺮ ﺇﺫﻥ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺃﻭ ﻣﻦ ﻭﻻﻩ ﻣﻦ ﻗﺎﺽ ﺃﻭ ﺻﺎﺣﺐ ﺷﺮﻃﺔ : ﻟﻢ ﻳﺠﺰ، ...ﻭﻋﻨﺪ ﺍﻟﺸﺎﻓﻌﻲ ﺑﺄﺭﺑﻌﻴﻦ. ﻭﻻ ﺟﻤﻌﺔ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﺴﺎﻓﺮﻳﻦ ﻭﺍﻟﻌﺒﻴﺪ ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﻭﺍﻟﻤﺮﺿﻰ ﻭﺍﻟﺰﻣﻨﻰ، ﻭﻻ ﻋﻠﻰ ﺍﻷﻋﻤﻰ ﻋﻨﺪ ﺃﺑﻲ ﺣﻨﻴﻔﺔ، ﻭﻻ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺸﻴﺦ ﺍﻟﺬﻱ ﻻ ﻳﻤﺸﻲ ﺇﻻ ﺑﻘﺎﺋﺪ..."
"Abu Hanifa (shugaban mazhabar Hanafiyya, ya ce); Sallar Jumu'a bata zama wajibi sai a babban gari, kuma babban gari yana nufin; garin da ake gudanar da shari'ar Musulunci, kuma sallar Jumu'a bata zama wajibi har sai akwai Imam (Shugaba)... Saboda hadisin da aka ruwaito Annabi(saw) yana cewa; abubuwa 4 hakkin Imam (Shugaba) ne: zartar da haddi, raba Zakka, raba Ganima, da wajabta sallar Jumu'a (kenan idan ba Imam sallah Jumu'a bata wajaba ba), idan ma aka yi sallar Jumu'a ba tare da izinin imam ba... to bata wadatar ba (har sai mutum ya hada da sallar Azahar)...".
- ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺍﻟﻜﺸﺎﻑ ﻋﻦ ﺣﻘﺎﺋﻖ ﻏﻮﺍﻣﺾ ﺍﻟﺘﻨﺰﻳﻞ : ﺍﻟﺰﻣﺨﺸﺮﻱ : ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ : آية 9 : ﻣﻜﺘﺒﺔ ﺍﻟﻌﺒﻴﻜﺎﻥ : ﺳﻨﺔ ﺍﻟﻨﺸﺮ 1418 : ﻫـ - 1998 ﻡ : ﺭﻗﻢ ﺍﻟﻄﺒﻌﺔ : ﺍﻟﻄﺒﻌﺔ ﺍﻷﻭﻟﻰ : ﻋﺪﺩ ﺍﻷﺟﺰﺍﺀ : ﺳﺘﺔ ﺃﺟﺰﺍﺀ.
Wannan hadisin da ya ke nuna Jumu'a bata wajaba sai da Imam (Shugaba) ya zo a littafan Ahlus-sunnah masu yawan gaske, daga Sahabbai masu yawan gaske:
ﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﻣﺴﻌﻮﺩ ﻭﺍﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ
ﻭﺍﺑﻦ ﺍﻟﺰﺑﻴﺮ ﻣﻮﻗﻮﻓﺎ ﻭﻣﺮﻓﻮﻋﺎ ...ﺃﺭﺑﻊ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻮﻻﺓ : ﺍﻟﺤﺪﻭﺩ، ﻭﺍﻟﺼﺪﻗﺎﺕ. ﻭﺍﻟﺠﻤﻌﺎﺕ، ﻭﺍﻟﻔﻲﺀ.
- ﻓﺘﺢ ﺍﻟﻘﺪﻳﺮ : ﻛﻤﺎﻝ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﺑﻦ ﻋﺒﺪﺍﻟﻮﺍﺣﺪ (ﺍﺑﻦ ﺍﻟﻬﻤﺎﻡ) : ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﺤﺪﻭﺩ : ﺍﻟﺠﺰﺀ ﺍﻟﺨﺎﻣﺲ : ﺹ : 235 : ﺩﺍﺭ ﺍﻟﻔﻜﺮ : ﻋﺪﺩ ﺍﻷﺟﺰﺍﺀ : ﻋﺸﺮﺓ ﺃﺟﺰﺍﺀ...
Hakama zantukan wasu daga cikin Tabi'ai ya nuna lallai sai da Jagoran Musulmi sannan sallar Jumu'a take wajaba:
ﻭﻋﻦ ﻋﻄﺎﺀ ﺍﻟﺨﺮﺍﺳﺎﻧﻲ ﻗﺎﻝ : ﺇﻟﻰ ﺍﻟﺴﻠﻄﺎﻥ ﺍﻟﺰﻛﺎﺓ ﻭﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﻭﺍﻟﺤﺪﻭﺩ .
- ﻣﺼﻨﻒ ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺷﻴﺒﺔ (5 / 506). ﺍﺑﻦ ﺣﺰﻡ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺤﻠﻰ ﺑﺴﻨﺪﻩ (12 / 73). ﻣﻤﻦ ﺫﻛﺮﻩ ﺍﻟﺴﺮﺧﺴﻲ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺒﺴﻮﻁ (9 / 80)....
Malaman mazhabar Hafiyya suna cewa;
"ﺍﺷﺘﺮﻁ ﺍﻟﺤﻨﻔﻴﺔ، ﺇﺫﻥ ﺍﻟﺴﻠﻄﺎﻥ ﺑﺬﻟﻚ، ﺃﻭ ﺣﻀﻮﺭﻩ، ﺃﻭ ﺣﻀﻮﺭ ﻧﺎﺋﺐ ﺭﺳﻤﻲ ﻋﻨﻪ، ﺇﺫ ﻫﻜﺬﺍ ﻛﺎﻥ ﺷﺄﻧﻬﺎ ﻓﻲ ﻋﻬﺪ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ(ص) ﻭﻓﻲ ﻋﻬﻮﺩ ﺍﻟﺨﻠﻔﺎﺀ ﺍﻟﺮﺍﺷﺪﻳﻦ"
"Sharadi ne kafin Jumu'a ta zama wajibi a samu iznin shugaban Musulmai, ko halartasa a gurin (yin Sallar) ko ya turo da wakili, haka ake yi a lokacin Annabi(saw) da lokacin khulafa'ur-Rashidin".
- ﺍﻟﻤﻮﺳﻮﻋﺔ ﺍﻟﻔﻘﻬﻴﺔ: ﺝ 27 ﺹ 196. وﺯﺍﺭﺓ ﺍﻷﻭﻗﺎﻑ ﻭﺍﻟﺸﺆﻭﻥ ﺍﻹﺳﻼﻣﻴﺔ – ﺍﻟﻜﻮﻳﺖ . ﺍﻟﻄﺒﻌﺔ ﺍﻷﻭﻟﻰ 1992 ﻡ.
- ﺍﻟﻌﻨﺴﻲ ﺍﻟﺼﻨﻌﺎﺋﻲ: ﺍﺣﻤﺪ ﺑﻦ ﻗﺎﺳﻢ : ﺍﻟﺘﺎﺝ ﺍﻟﻤﺬﻫﺐ ﻷﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﻤﺬﻫﺐ ﺝ 1 ﺹ 136. ﻣﻜﺘﺒﺔ ﺍﻟﻴﻤﻦ ﺍﻟﻜﺒﺮﻯ / ﺻﻨﻌﺎﺀ.
- ﺍﻃﻔﻴﺶ : ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ ﻳﻮﺳﻒ : ﺷﺮﺡ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻨﻴﻞ ﺝ 2 ﺹ 324. ﺍﻟﻄﺒﻌﺔ ﺍﻟﺜﺎﻟﺜﺔ 1985 ﻡ – ﻣﻜﺘﺒﺔ ﺍﻹﺭﺷﺎﺩ، ﺟﺪﺓ.
A Fiqhun Shia, jagoran musulmi, shugaba ko Imam ya nufin Annabi Muhammad(saw) ko daya daga cikin Imamai Ma'asumai(as) 12, wannan ne yasa; Sallar Jumu'a a wannan zamani namu (lokacin gaibar Imam Al-Mahdi(as) wajibace 'yar zabi (tsakanin mutum yayi sallar Jumu'a ko kuma yayi Azahar).
Ayatullah Khomeini(qs) yana cewa:
"ﺗﺠﺐ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﻓﻲ ﻫﺬﻩ ﺍﻷﻋﺼﺎﺭ ﻣﺨﻴﺮﺍ ﺑﻴﻨﻬﺎ ﻭﺑﻴﻦ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻈﻬﺮ، ﻭﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﺃﻓﻀﻞ ﻭﺍﻟﻈﻬﺮ ﺃﺣﻮﻁ، ﻭﺃﺣﻮﻁ ﻣﻦ ﺫﻟﻚ ﺍﻟﺠﻤﻊ ﺑﻴﻨﻬﻤﺎ، ﻓﻤﻦ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﺳﻘﻄﺖ ﻋﻨﻪ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻈﻬﺮ ﻋﻠﻰ ﺍﻷﻗﻮﻯ، ﻟﻜﻦ ﺍﻷﺣﻮﻁ ﺍﻹﺗﻴﺎﻥ ﺑﺎﻟﻈﻬﺮ ﺑﻌﺪﻫﺎ"
"Sallar Jumu'a a wannan zamani namu wajaba ce 'yar zabi; tsakanin yinta da kuma yin sallar Azahar (saboda gaibar Imam Al-Mahdi(afs), amma yin sallar Jumu'ar ya fi, sai dai kuma yin Azahar shine ya fi zama ihtiyadi, yin duka 2 (Jumu'a da ya Azahar) ya fi zama (babban) ihtiyati, don haka wanda yayi Jumu'a ta dauke masa Azahar, amma a bisa ihtiyati yin Azahar bayan sallar Jumu'a ya fi".
- ﺗﺤﺮﻳﺮ ﺍﻟﻮﺳﻴﻠﺔ – ﺍﻟﺴﻴﺪ ﺍﻟﺨﻤﻴﻨﻲ ﺝ ۱ ﺹ ۲۳۱.
Ayatullah Khamnein(dz) yana cewa;
"ﺻﻼﺓ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻧﺖ ﻓﻲ ﺍﻟﻮﻗﺖ ﺍﻟﺤﺎﺿﺮ ﻭﺍﺟﺒﺎ ﺗﺨﻴﻴﺮﻳﺎ، ﻭﻻ ﻳﺠﺐ ﺍﻟﺤﻀﻮﺭ ﻓﻴﻬﺎ، ﻟﻜﻦ ﺑﺎﻟﻨﻈﺮ ﺇﻟﻰ ﻓﻮﺍﺋﺪ ﻭﺃﻫﻤﻴﺔ ﺍﻟﺤﻀﻮﺭ ﻓﻲ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ، ﻓﻼ ﻳﻨﺒﻐﻲ ﻟﻠﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﺣﺮﻣﺎﻥ ﺃﻧﻔﺴﻬﻢ ﻣﻦ ﺑﺮﻛﺎﺕ ﺍﻟﺤﻀﻮﺭ ﻓﻲ ﻣﺜﻞ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻟﻤﺠﺮﺩ ﺍﻟﺘﺸﻜﻴﻚ ﻓﻲ ﻋﺪﺍﻟﺔ ﺇﻣﺎﻡ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ، ﺃﻭ ﻷﻋﺬﺍﺭ ﻭﺍﻫﻴﺔ ﺃﺧﺮ"
"Ko da yake sallar Jumu'a a wannan zamani namu wajiba ce 'yar zabi (tsakanin yinta da sallar Azahar), halartarta ba wajibi ba ne, to amma soboda la'akari da falalolin da ke cikinta; bai kamata ga muminai su haramtawa kansu albarkar da ke cikinta ba; don kawai shakkar adalcin Liman, ko saboda saboda wasu dalilai da ba su da wani muhimmanci".
- ﺃﺟﻮﺑﺔ ﺍﻻﺳﺘﻔﺘﺎﺀﺍﺕ – ﺍﻟﺴﻴﺪ ﻋﻠﻲ ﺍﻟﺨﺎﻣﻨﺌﻲ ﺝ ۱ ﺹ ۱۸۰.
Sannan Ayatullah Khamnein(dz) ya kara da cewa:
"ﺗﺮﻙ ﺍﻟﺤﻀﻮﺭ ﻭﺍﻟﻤﺸﺎﺭﻛﺔ ﻓﻲ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﺍﻟﻌﺒﺎﺩﻳﺔ ﺍﻟﺴﻴﺎﺳﻴﺔ ﻣﻦ ﺃﺟﻞ ﻋﺪﻡ ﺍﻟﻤﺒﺎﻻﺓ ﺑﻬﺎ ﻣﺬﻣﻮﻡ ﺷﺮﻋﺎ، ﻭﺍﻹﺑﺎﺀ ﻋﻦ ﺍﻟﻤﺸﺎﺭﻛﺔ ﻓﻴﻬﺎ ﺑﺼﻮﺭﺓ ﺩﺍﺋﻤﺔ ﻟﻴﺲ ﻟﻪ ﻭﺟﻪ ﺷﺮﻋﻲ".
"Barin Sallar Jumu'a saboda rashin daukarta da muhimmanci abin zargi ne a shari'a".
Sannan kuma (dz) ya ce:
"صلاة الجمعة مجزية عن صلاة الظهر، ولكن لا اشكال في الإيتان بصلاة الظهر احتياطا بعد صلاة الجمعة..."
"Sallar Jumu'a tana dauke sallar Azahar, sai dai ba matsala mutum ya kara da yin Azahar bayan sallar Jumu'a saboda ihtiyadi".
https://maasumiya.blogspot.com
- ﺃﺟﻮﺑﺔ ﺍﻻﺳﺘﻔﺘﺎﺀﺍﺕ – ﺍﻟﺴﻴﺪ ﻋﻠﻲ ﺍﻟﺨﺎﻣﻨﺌﻲ ﺝ ۱ ﺹ ۱۸۰.
SALLAR IDI BATA DAUKE WAJABCIN SALLAR JUMU'AH:
Al-Qurdabi (babban malamin Tafsiri) yana cewa:
"Sallar Idi bata dauke wajabcin sallar Jumu'a, sabanin abinda Ahmad bin Hambal ya tafi akai na cewa: idan sallar Idi ta fada ranar Jumu'a; to ta dauke wajabcin Jumu'a, (Ahmad bin Hambal) ya dogara ne da cewa khalifa Usman yayi izini ga ma'aikatansa da ba sai sun yi sallar Jumu'a ba idan ta fada ranar Idi, amma wannan aikin na sahabi (Usman) ba hujja ba ne tunda ba'a yi ittifaki akai ba... (sannan kuma ya saba da hadisi ingantacce) da ya zo a Sahihul Muslim daga Nu'uman bin Bashir cewa; Annabi(saw) yana karanta Suratul a'ala da Gashiya a Sallar Idi 2 (Karama da Babba) da Sallar Jumu'a, idan kuma Idi ya hadu da Jumu'a wadannan surorin 2 yake karantawa (kenan Annabi(saw) yana sallar Jumu'a ko da ta hadu da sallar Idi)....":
"ﻻ ﺗﺴﻘﻂ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﻟﻜﻮﻧﻬﺎ ﻓﻲ ﻳﻮﻡ ﻋﻴﺪ، ﺧﻼﻓﺎ ﻷﺣﻤﺪ ﺑﻦ ﺣﻨﺒﻞ ﻓﺈﻧﻪ ﻗﺎﻝ: ﺇﺫﺍ ﺍﺟﺘﻤﻊ ﻋﻴﺪ ﻭﺟﻤﻌﺔ
ﺳﻘﻂ ﻓﺮﺽ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ; ﻟﺘﻘﺪﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﻭﺍﺷﺘﻐﺎﻝ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺑﻪ ﻋﻨﻬﺎ. ﻭﺗﻌﻠﻖ ﻓﻲ ﺫﻟﻚ ﺑﻤﺎ ﺭﻭﻱ ﺃﻥ ﻋﺜﻤﺎﻥ ﺃﺫﻥ ﻓﻲ ﻳﻮﻡ ﻋﻴﺪ ﻷﻫﻞ ﺍﻟﻌﻮﺍﻟﻲ ﺃﻥ ﻳﺘﺨﻠﻔﻮﺍ ﻋﻦ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ. ﻭﻗﻮﻝ ﺍﻟﻮﺍﺣﺪ ﻣﻦ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﻟﻴﺲ ﺑﺤﺠﺔ ﺇﺫﺍ ﺧﻮﻟﻒ ﻓﻴﻪ ﻭﻟﻢ ﻳﺠﻤﻊ ﻣﻌﻪ ﻋﻠﻴﻪ. ﻭﺍﻷﻣﺮ ﺑﺎﻟﺴﻌﻲ ﻣﺘﻮﺟﻪ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪ ﻛﺘﻮﺟﻬﻪ ﻓﻲ ﺳﺎﺋﺮ ﺍﻷﻳﺎﻡ. ﻭﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ ﻋﻦ ﺍﻟﻨﻌﻤﺎﻥ ﺑﻦ ﺑﺸﻴﺮ ﻗﺎﻝ : ﻛﺎﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻘﺮﺃ ﻓﻲ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ ﻭﻓﻲ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ: ﺏ ﺳﺒﺢ ﺍﺳﻢ ﺭﺑﻚ ﺍﻷﻋﻠﻰ ﻭ ﻫﻞ ﺃﺗﺎﻙ ﺣﺪﻳﺚ ﺍﻟﻐﺎﺷﻴﺔ ﻗﺎﻝ: ﻭﺇﺫﺍ ﺍﺟﺘﻤﻊ ﺍﻟﻌﻴﺪ ﻭﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﻓﻲ ﻳﻮﻡ ﻭﺍﺣﺪ ﻳﻘﺮﺃ ﺑﻬﻤﺎ ﺃﻳﻀﺎ ﻓﻲ ﺍﻟﺼﻼﺗﻴﻦ. ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ﻭﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ ﻭﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ".
- ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺍﻟﻘﺮﻃﺒﻲ (ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﻷﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ) : ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ : آية 9 : ﺩﺍﺭ ﺍﻟﻔﻜﺮ : ﻋﺪﺩ ﺍﻷﺟﺰﺍﺀ : ﻋﺸﺮﻭﻥ ﺟﺰﺀﺍ.
Mafi yawan masu riwaito hadisai sun riwaito ce Annabi(saw) yana yin sallar Jumu'a ko da ta yi daidai da ranar Idi:
878 ( 62 ) وَحَدَّثَنَا يَحْيَى بْنُ يَحْيَى ، وَأَبُو بَكْرِ بْنُ أَبِي شَيْبَةَ ، وَإِسْحَاقُ ، جَمِيعًا عَنْ جَرِيرٍ ، قَالَ يَحْيَى : أَخْبَرَنَا جَرِيرٌ، عَنْ إِبْرَاهِيمَ بْنِ مُحَمَّدِ بْنِ الْمُنْتَشِرِ ، عَنْ أَبِيهِ ، عَنْ حَبِيبِ بْنِ سَالِمٍ مَوْلَى النُّعْمَانِ بْنِ بَشِيرٍ، عَنِ النُّعْمَانِ بْنِ بَشِيرٍ قَالَ : كَانَ رَسُولُ اللَّهِ(صَ) يَقْرَأُ فِي الْعِيدَيْنِ، وَفِي الْجُمُعَةِ بِـ { سَبِّحِ اسْمَ رَبِّكَ الْأَعْلَى }، وَ { هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ الْغَاشِيَةِ }، قَالَ : وَإِذَا اجْتَمَعَ الْعِيدُ وَالْجُمُعَةُ فِي يَوْمٍ وَاحِدٍ ؛ يَقْرَأُ بِهِمَا أَيْضًا فِي الصَّلَاتَيْنِ.
- صحيح مسلم : كتاب : الجمعة. | باب : ما يقرأ في صلاة الجمعة : 878.
- سنن أبي داود ( 1122 ).
- سنن الترمذي ( 533 ).
- سنن النسائي ( 1424, 1568, 1590 ).
- سنن ابن ماجه ( 1281 ).
- سنن الدارمي ( 1609, 1648 ).
- مسند أحمد ( 18383, 18387, 18409, 18431, 18442 ).
- ﻧﻴﻞ ﺍﻷﻭﻃﺎﺭ : ﺃﺑﻮﺍﺏ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ : ﺑﺎﺏ ﻣﺎ ﻳﻘﺮﺃ ﺑﻪ ﻓﻲ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ : 1259.
Maganar Al-Qurtabi da wadannan Ingantattun hadisan; suna tabbatar da Khalifa Usman ne ya soke wajabcin sallar Jumu'ah; idan ta fadi ranar Idi.
Kenan lokacin Khalifancin Usman an kauda wasu farilloli da canza sunnar Annabi(saw); da gangan ba tare da hujja ba?
Ta ya Sallar da take Mustahabbi zata sauke wajabcin farilla?
Kusan dukkan malaman Musulunci sun hadu akan cewa; Sallar Idi mustahabi ce (a wannan zamanin namu):
Ayatullah Khomeini(qs) yana cewa:
"صلاة العيدين واجبة مع حضور الإمام(ع)... و مستحبة في زمان الغيبة..."
"Sallar Idi wajibi ce a lokacin bayyanar Imam Al-mahdi(as), amma a yanzu mustahabbi ce"
- ذبدة الأحكام، ص ٧٥.
Ayatullah Khamnein(as) shima ya tabbatar da mustahabbancin sallar Idi a wannan zamanin namu.
- منتخب الأحكام، ص ١١٠ - ١١١.
➖➖➖
IS'HAQ MOHD KIBIYA