KADA KUYI BACCI...!!


Akwai wani Hadisi da aka samo daga Sayyada Zahrah (AS) tace: Manzon Allah (S) ya shiga gare ni sai na
shinfidamasa shinfida ta domin yin barci, sai
yace ya Fatima kada ki yi barci face kin aikata abubuwa hudu,
1-Kin sauke Alk ur’ani.
2- Kin sa Annabawa su zama masu cetonki.
3- Kin yardar da
mu'uminai.
4-Kin yi hajji da umra,
https://maasumiya.blogspot.com
sai tace ya Manzon Allah kayi umarni da
abu 4 wanda ba zan iya yin su duka ba a
yanzu! sai Manzon Allah yayi murmushi,
sai ya ce mata idan kika karanta kulhuwallahu sau ukku kamar kin sauke Alkur’ani, idan kin yi man salati da kuma Annabawan da suka gabace ni zamu kasance masu cetonki ranar kiyama.

Idan kika yi istigfaru ga mu'uminai duka zasu yarda dake. Idan kika ce subhanallahi,walhamdu lillahi,wala ilaha-illah,wallahu Akbar to kamar kin yi hajji da umra ne.”


Mas'udu Dan Masani Shinkafi 08149993999

2 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post