TAFSEERIN ALKUR'ANI MAI GIRMA A HALKAN RIKKOS DAKE DA'IRAR JOS.
```_Tare da Idishia Jos```
A kowanne lokaci ana samun wakikin Manzon Allah (S), a wannan lokaci ma akwai wakilin Manzon Allah shine wanda Buhari ya zalunta kuma duk abinda mutum yaga dama yayi lokacin shine. Kamar yanda aka ga mun fito dukkan mu domin nuna rashin amincewan mu da abinda akewa Palastinawa haka zamuga karshen wannan zalunci da ake mana a Nigeriya.
Malam Abubakar ya kawo misali da Muzaharar kano inda aka jibge jami'an tsaro sosai akan dole kar ayi Muzahara amma haka 'yan uwa suka kutsa suka fasa jami'an tsaro suka sadaukar da ransu da komai nasu domin nuna goyon bayansu akan Palasatinawa.
Aci gaba da Tafseerin Alkur'ani Mai Girma wanda ake gudanarwa a Halkan Rikkos na Da'irar Jos. Wanda Malam Abubakar Ilyas (Dattijo) yake gabatarwa tare da mai jamasa baki Alaramma Abubakar Maisalati. Ana gudanar da karatun Tafseer din ne a Masallacin Zakiru dake Rikkos 'yan siminti Jos.
***
#FreeZakzaky
#Freedom4Zakzaky
Tags:
Muhimman zantuka