'Dan Shi'a kar ka yaudari kanka!!

Ya kai 'Dan uwa
'Dan Shi'ar
gidan Annabi {s}
kar ka
yaudari kanka,
wallahi babu
Alheri ga Mutumin
da ya ke
ikirarin shi
Musulmi kuma
mabiyin
A'imma {as},
amma kuma
ba ya yin
Tahajjud
komai
karancinta.
Abin da ake
nufi da
Tahujjud: shi ne
sallar dare.
Imam Sadik {as}
ya ce,
duk wanda
baya Sallar dare
hakika ba ya
tare da mu.
kuma ya ce,
"Halittar da
Allah ya fi Ki
shi ne
Mushen dare
ma'ana
mai shararar
barci har gari
ya waye.
Danna domin karanta Wasiyyar Usman Dan fodiyyo Akan Shek Zakzaky.
Manzon Allah {s}
ya ce,
"Mahaifiyar
Annabi Dawud {as}
ta ce
ya 'Dana!
Na hane ka ga
yawaita barci
a cikin dare,
domin yana
sa mutum
ya tashi
a matsiyaci
ranar
alkiyama.
Wani Mutum
ya zo
wajen
Imam Ali {as}
ya ce masa
"Ni fa ba na
iya yin sallar dare
sai Imam
ya ce, masa
babu shakka
kai mutum ne
da zunubai
suka
dabaibaye ka.
==>>
Kuma Allah
yana suffanta
munafukai
da cewa
"sune masu
kin tashi da dare,
masu gantali
da rana."
'Yan uwa
sai dage saboda
tahajjud
tafarki ne
na Annabawa
da A'imma {as}.
Allah yasa
mu dace
Bihaqqi Imam

Hussai {as}.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post