BAYANI KAN RAMAKON SALLOLI WAJIBAI


-Muhammad Jiddah Nguru 08120204209.


Da sunan Allah mai Murkushe azzalumi Buhari, tsira da aminci su tabbata ga shugaban halittun Allah Annabi Muhammad (S) da iyalan gidansa tsarkaka.

Wajibine ramakon salloli wajibai na yini wadanda suka Kubuce a cikin lokutan su, amma ban da sallar Jumma’a, wato ita in ta kubuce ma mutum sai dai yayi ramakon sallar Azahar, wannan kubucewar da gangan ne ko rafkannuwa ko jahilci ko kuma barci wanda ya game lokaci, wato yayi barci har lokacin sallah ya shiga ya fita.
lhttps://maasumiya.blogspot.com
Haka nan wajibine ramakon sallar da mutum yayi ta ba dai-dai ba, amma ba wajibi bane ramakon sallar yaro da bai yi ba a zamanin yarintar sa, wato lokacin da bai kai shekarun Taklif ba.

Haka nan mahaukaci a lokacin haukar sa, wato duk zamanin da yayi na hauka din ba zai ramka sallolin da bai yi ba.

Haka nan wanda ya suma shima ba zai ramka sallolin da suka kubuce masa ba a lokacin sumar, amma fa nan da sharadin idan bashi ya haifar da suman ba, domin idan shi ya sumar da kansa to zai rama sallolin da bai yi ba.

Haka nan kafirin da ya musulunta shima ba zai rama sallolin da suka kubuce masa ba wato lokacin da yake cikin kafirci, amma ban da wanda yayi Ridda, wato wanda yake musulmi ne sai ya bar musulunci, misali sai kuma daga baya ya dawo musuluncin, to a nan duk tsawon zamanin da ya kasance cikin riddar sai ya rama sallolin da bai yi ba ko da ko na shekaru ne.

Haka nan babu ramakon sallah ga mai jinin haila ko nifasi wato ga sallolin da suka kubuce masu a zamanin hailar ko nifasi,wato akasin Azumi shi zasu rama wadanda suka sha. Idan sabubba da suke wajabtar da rashin ramuwa suka gushe al-hali lokacin sallah bai fita ba, to wajibine ya tashi yayi sallar ko da ko raka’a daya kawai zai samu cikin lokacin, misali wanda ya suma ko mai ciwon hauka hankali ya dawo masu gashi kuma lokacin sallah yayi amma bai fita ba,

to idan har zai tashi yayi alwala ko taimama ya tada sallah ya iya samun ko da raka’a daya ne kafin lokacin ya fita to dole ne gareshi ya tashi yayi, in ko bai yi ba to ramuwar sallar ta wajaba gareshi, Haka hukuncin yake gamai jinin haila ko nifasi da ya dauke, Haka nan kuma da yaron da ya balaga lokacin sallah bai fita ba duka shima shigen wancan hukuncin ne.
Wani tambihi anan shine shekarun balaga wato na taklif
a mazhaba ta Ja’afariyya ga namiji shekaru 15 ne, ga mace kuma shekaru 9 ne, wani abin lura anan wannan lissafi ana nufin a kidaya ta kamariyya wato watannin musulunci.amma idan a kidayar miladiyyane wato na boko,ga namiji shekara 14 da wata 7 ne, ga mace kuma shekara 8 da wata 9 ne.
Haka nan wajibi ne ga Mukalif bayan istib-sarinsa, misali da yana Mazhabar Malikiyya sai ya dawo Mazhabar Ja’afariyya ramka sallolin da suka kubuce masa, ko wadanda yazo dasu sabanin malikiyyar, sai dai a lura nan ban da sallolin da yayi wadanda suka yi muwafaka da koyarwar malikiyya, wato ko da sun saba ma koyarwar Ja’afariyya, to a nan ba zai rama su ba.
Sai dai wani abin lura muhimmi kamar yadda Imam
Khumaini yayi bayani a nan shine, da mutum zai yi istibsari misali daga malikiyya ya koma ja’afariyya to wajibi ne akansa sallolinsa da dai sauran ibadodinsa su yi muwafaka da koyarwar Ja’afariyya, da zai yi su sabanin haka sai daga baya ta bayyana masa cewa ba haka yake a ja’afariyya ba to dole sai ya ramka su.
Saboda haka yana da gayar muhimmanci ire-iren mu da muka girma a cikin sunna daga baya Allah madaukaki yayi mana baiwa da riko da Ahlul Bayt da kuma ‘ya’yan mu da aka Haifa a ciki, ya kasance dukkan Ibadodin mu da kuma Mu’amalolinmu su dace da fatawowin mujtahidin da mutum yake Taklidi dashi, domin in bahaka ba daga baya idan ta bayyana ma mutum cewa ayyukan ibadodinsa akasin fatawowin mujtahidin da yake taklid da shine ta sai fa ya maimaita ayyukan komi yawan su.
Haka nan kuma ya halatta yin ramakon salloli ko da wane lokaci da daddarene ko da rana a tafiyane ko a zaman gida, misali idan a tafiyane zai iya rama sallolin da suka kubuce masa na zaman gida kuma zai rama sune a cike ba kasaru ba, in kuma a zaman gida yake zai iya rama sallar kasaru da ta kubuce masa amma a kasaru zai rama ta, wato dai abinda ake nufi a nan shine idan sallah ta kubuce ma mutum a zaman gida ba tafiya ba, to wajibine ya ramata cikakkiya, ko da ko a lokacin ramakon yana halin tafiyane,haka ma in a tafiya ne ta kubuce masa to zai rama ta a kasaru ko da yana zaune gidane.
Haka kuma idan sallah ta kubuce ma mutum amma farkon lokacin sallar yana mazunin gida, amma a karshen
lokacinta yana matafiyi ko kuma akasin haka wato farkon
lokacin sallar mutum yana matafiyi amma karshen lokaci
yana zaune gida, to fatawar Imam Khumaini a nan itace in da mutum yake a karshen lokacin sallar, saboda haka a wannan misali da aka bayar tun da a karshen lokacin yana matafiyi ne, to a kasaru zai rama sallar wato ko a gida yake ko a tafiyar,
a misali na biyu ko zai rama sallar cikakkiyane tun da a karshen lokacin yana zaune gida ne, sai dai wani tambihi
anan shine Imam Khumaini yace Ihtiyadi istihibabi mutum ya hada tsakanin yin ta kasaru da cikawa. Kuma wata mas’ala makamanciyar wannan itace, mutum ne lokacin salla ya shiga yana mazunin gida, kuma zai iya yin salla sai bai yi ba,sai yai tafiya gabanin yayi salla,
to a nan idan in da ya tafi ya kai haddin a yi mashi sallar kasaru to abinda ya hau kansa shine sallar kasaru, amma shima ihtiyadi istihibabi wato taka tsan- ltsan da aka fi so shine mutum ya hada, wato bayan yayi sallar kasarun sai kuma ya cika sallar amma fa yin haka ba wajibi bane.
Haka nan kuma da lokacin salla zai shiga mutum yana matafyi bai yi sallar ba har ya dawo gida, kuma da
sauran lokacin sallar to abin da ya hau kansa shine zai cikabsallar sane,amma idan ya hada wato bayan haka ya tashi yayi sallar kasaru, to haka aka fi so, wato ba wajibi bane yin haka.

BAYANI KAN RAMANKON SALLLOLIN NAFIL-FILI


Bayani kan Ramakon sallolin nafil-fili: Mustahabbi ne ramakon salloli nafil-fili na Rawatib wato nafilolin salloli wajibai wadanda sune, raka'a 2 gabanin sallar Asuba. Raka’a 8 gabanin sallar Zuhur. Raka’a 8 gabanin sallar Asar. Raka’a 4 bayan sallar Magrib. Raka’a 2 a zaune bayan sallar Isha’i.

To wadannan nafilolin ana son idan mutum bai samu yi ba ya rama daga baya, misali bai samu yin nafilolin zuhur da asar ba, to zai iya rama su cikin yinin ko kuma da daddare,ko kuma misali bai samu yin nafilolin magariba da isha’i ba to zai iya rama su cikin daren ko kuma washe gari. Wani tambihi anan shine nafilolin sallar zuhur da asar sun fadi ga matafiyi wato ba zai yi su ba,
wadanda zai yi sune nafilolin sallolin magariba da isha’i da kuma asuba.Haka nan yazo akan cewa kamar yadda Imam khumaini yayi bayani idan mutum bai samu yin wadannan salloli na nafiloli ba, kuma bai samu rama su ba, to mustahabbi ne ya yi sadaka,mafi karanci shine ko wace raka’a biyu yayi sadakar mudi-nabiyy,
in kuma bai da ikon haka to ko wace raka’a hudu mudi- nabiyy daya,in kuma bai da ikon haka to mudi-nabiyy daya ga nafilolin dare da kuma mudin nabiyy daya ga
nafilolin rana.Saddam Kamar yadda yake mustahabbi ne mutum ya rama wadannan salloli na rawatib, haka nan kuma mustahabbi ne ya rama sallar Tahajjud din sa kashe-gari tsakanin fitowar rana zuwa zawal, wato idan ta kubuce masa.
Haka nan wanda yake da ramuwar salloli wajibai zai iya yin sallolin nafiloli wato akasin Azumi shi idan ana bin
ka na wajibi to dole ne sai ka rama shi gabanin ka iya yin
azumin nafila.
Allah ta'ala ya gaggauta dawo mana da su Maulanmu Sayyid Ibrahim Zakzaky (H).

FREE SAYYID ZAKZAKY

Ma'asumiya Nigeria news update

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post